ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

2027: Hadakar Obi Da Kwankwaso Na Shan Suka Daga Wasu Jagororin Siyasar Kano

by Rabi'u Ali Indabawa
4 months ago
kwankwaso

Wani jigo a jam’iyyar APC ta Jihar Kano, Faizu Alfindiki, ya soki tsohon gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, kan abin da ya bayyana a matsayin kusancinsa da tafiyar siyasar tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party, Peter Obi.

Da yake magana da manema labarai a Kano jiya, Alfindiki ya nuna shakku kan alkiblar siyasar Kwankwaso, yana zarginsa da kasa bai wa hadin kan Arewa muhimmanci a lokacin da yankin ke bukatar karin hadin kai tsakanin shugabannin siyasa.

Alfindiki, wanda tsohon shugaban karamar hukumar Kano Municipal ne, ya ce ‘yan Arewa da dama sun yi mamakin yadda Kwankwaso ya fi nuna sha’awar hada kai da bangaren Obi maimakon gina fahimta tsakanin manyan ‘yan siyasar Arewa masu tasiri.

ADVERTISEMENT

A cewarsa, Arewa na bukatar karin hadin kai tsakanin fitattun ‘yan siyasar yankin domin kare muradun yankin da karfafa matsayinsa a siyasar kasa.

Ya ce: “Mutane da dama a Arewa suna kallon wannan mataki a matsayin rashin bai wa hadin kan yankin muhimmanci, musamman ganin cewa ana sa ran manyan shugabanni su fi mayar da hankali wajen hada kan Arewa da kare muradunta.”

LABARAI MASU NASABA

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

Ya kuma yi zargin cewa Obi bai nuna damuwa kan manyan matsalolin Arewa ba, ciki har da rashin tsaro, noma da bunkasa tattalin arziki.

“Ba kasafai ake jin yana magana kan manyan kalubalen Arewa yadda mutane da dama ke tsammani daga wanda ke neman cikakken goyon bayan yankin ba,” in ji shi.

Alfindiki ya kuma yi zargin cewa rashin sha’awar Kwankwaso wajen yin aiki tare da sauran manyan ‘yan siyasar Arewa ya haifar da tunanin cewa muradinsa na siyasa ya fi karkata ga anfani na kai maimakon muradin yanki baki daya.

Ya ce: “A siyasa, ana auna mutum ne da matsayinsa da kuma irin hadin kan da yake ginawa. Mutanen Arewa na bukatar shugabanni da za su hada kai domin tabbatar da ci gaban yankin da kare martabarsa a siyasa.”

Sai dai ya yaba wa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu bisa abin da ya kira ayyukan ci gaba da ake gani a fadin Arewa, musamman a fannoni kamar gine-ginen more rayuwa, tituna da noma.

Obi
Rabi'u Ali Indabawa
+ postsBio
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ƙungiya Ta Gudanar Da Zaɓen Sabbin Shugabanninta A Abuja
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Jihar Katsina Da UNICEF Sun Ceto Rayuwar Yara Ta Hanyar Samar Da Abinci Mai Gina Jiki
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Yadda Tinubu Ya Kashe Naira Biliyan 37.64 A Tafiye-tafiye
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ta’addaci: Mutum 14,500 Sun Bace A Arewa Maso Gabas

MASU ALAKA

'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare
Labarai

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Next Post
RMAFC

Rabar Da Tattalin Arzikin Kasa: Hukumar RMAFC Ta Kaddamar Da Aikin Tattara Sahihan Bayanai

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.