Wasu mambobin ƙungiyar “Tinubu Must Go” a Jihar Kano sun zargi rundunar ƴansanda da hana su shiga wurin da suka tanada domin gudanar da taro ranar Lahadi, 11 ga Oktoba, 2026. Ƙungiyar ta bayyana matakin a matsayin tauye ’yancinsu na haɗuwa da bayyana ra’ayoyinsu kan gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Lauya Abba Hikima, ɗaya daga cikin jagororin tafiyar, ya bayyana hakan ne a wani bidiyo kai tsaye da ya wallafa a shafinsa na Facebook. Ya yi zargin cewa an girke motocin ƴansanda sama da 10 a wajen cibiyar taron, duk da cewa sun biya kuɗin amfani da wurin.
Hikima ya ce kwamishinan ƴansandan Jihar Kano, Ibrahim Bakori, ya kira shi ta waya ranar Asabar, inda ya shawarce shi da ya sanar da jami’an tsaro game da taron. Sai dai lauyan ya ce ya tabbatar wa kwamishinan cewa taron zai gudana ne a cikin wani wuri da aka killace, kuma za a gudanar da shi cikin lumana da bin doka.

Ya kuma yi bayani kan sashi na 35, 39 da 40 na Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya, waɗanda suka shafi ƴancin mutum, da bayyana ra’ayi da yin taro cikin ƴanci. Abba Hikima ya ƙara da cewa wasu jami’an sun nuna rashin amincewa da kayan da mambobin ƙungiyar ke sanyawa masu ɗauke da tambarin “Tinubu Must Go”, ko da yake ya dage cewa hakan na cikin ƴancinsu na siyasa.
Ƙungiyar ta ce manufarta ita ce wayar da kan ƴan Nijeriya da kuma ƙarfafa su su kaɗa ƙuri’a domin cire Shugaba Tinubu daga mulki a zaɓen 2027. Ta kuma yi alwashin ci gaba da shirya taruka da zanga-zanga. Sai dai kakakin rundunar ƴansandan Kano, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, bai mayar da martani ga kiran waya da saƙonnin da aka aika masa domin jin ta bakin rundunar ba har zuwa lokacin kammala rahoton.














