ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

ATBU Ta Janye Filin Ginin Masallaci Da Ta Bai wa TIMSAN, Ta Amince Kowa Ya Yi Addininsa Yadda Ya Fahimta

by Sulaiman and Khalid Idris Doya
2 months ago
ATBU

Hukumar gudanarwar Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBU) da ke Bauchi ta janye izinin bada fili wa ƙungiyar ɗalibai na ɓangaren Ɗarikar Tijjaniyya wato ‘Tijjaniyya Muslim Students Association of Nigeria’ (TIMSAN) a cikin harabar jami’ar da ke Gubi domin gina masallaci.

Jami’ar ta kuma sanar da shirinta na sake yin garambawul ga tsarin gudanar da harƙoƙin addini ta hanyar tabbatar da cewa dukkanin ɓangarorin Musulunci da ke cikin jami’ar su na da wakilci a cikin Majalisar Shura da kuma shugabancin ƙungiyar ɗalibai musulmai ‘Muslim Students’ Society of Nigeria’ (MSSN) reshen jami’ar.

Daraktan yaɗa labarai da hulɗa da Jama’a na jami’ar, Alhaji Zailani Bappa, shi ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da ya yi a sakatariyar ‘yan jarida da ke Bauchi a ranar Laraba.

ADVERTISEMENT

Ya ce taron ya mayar da hankali ne kan cece-ku-cen da suka biyo bayan bai wa reshen TIMSAN na ATBU fili domin gina masallaci.

Takaddamar ta samo asali ne bayan da babban limamin jami’ar, Farfesa Mansur Isa Yelwa, tare da mataimakinsa, suka yi murabus a ranar Juma’a, 26 ga Yunin 2026, domin nuna rashin amincewarsu da matakin jami’ar na bai wa TIMSAN fili mai girman ƙafa 100 by 50 domin gina masallaci don gudanar da ayyukansu na addini.

LABARAI MASU NASABA

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue

Sai dai wakilinmu ya tabbatar da cewa Farfesa Mansur ya janye murabus ɗinsa kuma ya koma bakin aikinsa a matsayin Babban Limamin jami’ar.

A baya dai, jami’ar ta bayyana cewa manufar bai wa TIMSAN filin ita ce domin ba ƙungiyar damar gina masallaci da za ta gudanar da ayyukan ibadarta, ciki har da Wazifa, bisa tanadin kundin tsarin mulkin ƙasa da ke bai wa kowa ‘yancin gudanar da addininsa cikin ‘yanci. Lamarin kuma ya samo asali tun daga hana ‘yan darikar damar yin wazifa a masallatan da suke ƙarƙashin kungiyar MSSN.

Bappa ya ce sanarwar murabus ɗin Limamin ya jawo martani daga sassa daban-daban na ƙasa da ma ƙasashen waje, tare da haifar da damuwar tsaro a jami’ar da sauran manyan makarantun gaba da sakandare.

Ya bayyana cewa mahukuntan jami’ar sun ga ya dace su fayyace gaskiyar abin da ya faru, yana mai cewa matakin bai wa TIMSAN fili ya biyo bayan ƙin amincewar Majalisar Shura da membobin TIMSAN su gudanar da ayyukansu na addini a babban masallacin jami’ar.

A cewarsa, wannan rikici ya sa hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta shiga tsakani, inda ta kira taron masu ruwa da tsaki domin samar da mafita cikin lumana. Ya ce taron, wanda aka gudanar ranar Talata, 30 ga Yunin 2026, a shalkwatar DSS da ke Bauchi, ya samu halartar wakilan mahukuntan jami’ar, Majalisar Shura, reshen MSSN na ATBU da kuma reshen TIMSAN na ATBU.

Bappa ya ce mahalarta taron sun amince cewa daga yanzu za a bai wa dukkan ɓangarorin Musulunci da ke jami’ar damar gudanar da ayyukansu na addini a lokutan da za a ware musu a masallatan jami’ar. Ya ƙara da cewa an kuma yanke shawarar cewa mahukuntan jami’ar ne za su riƙa naɗa babban limami da mataimakansa, tare da tabbatar da cewa dukkan harƙoƙin addini a harabar jami’ar suna gudana bisa ƙa’idoji da dokokin jami’ar.

Ya yaba wa DSS bisa saurin shiga tsakani da kuma ƙoƙarin da ta yi wajen dawo da zaman lafiya.

Ya ce, “Mahukuntan Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa suna yaba wa shugabancin DSS a Bauchi saboda saurin shiga tsakani, kuma suna tabbatar wa dukkan masu ruwa da tsaki cewa za a aiwatar da dukkan shawarwarin da aka cimma domin tabbatar da dorewar zaman lafiya da haɗin kai a harabar jami’ar.”

Bappa ya kuma bayyana cewa dukkan shawarwarin da aka cimma a taron an amince da su tare da sanya hannu a kansu daga dukkan bangarorin da suka halarta.

Hakazalika, ya tabbatar da cewa nan ba da jimawa ba hukumar gudanarwar jami’ar za ta sanar da wasu ƙarin matakai da suka shafi shugabancin babban masallacin jami’ar da sauran harkokin Musulmi, domin ƙarfafa zaman lafiya, haɗin kai da kwanciyar hankali a cikin jami’ar.

ATBU
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna
  • Sulaiman
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi
ATBU
Khalid Idris Doya
+ posts Bio
  • Khalid Idris Doya
    https://hausa.leadership.ng/author/khalid-idris-doya/
    Yaro Ya Harbe Kansa Har Lahira Bayan Mafarauci Ya Yi Sakaci Da Bindigarsa A Bauchi
  • Khalid Idris Doya
    https://hausa.leadership.ng/author/khalid-idris-doya/
    An Kama Mutane 5 Da Sassan Jikin Ɗan’Adam Za Su Yi Tsafi A Bauchi
  • Khalid Idris Doya
    https://hausa.leadership.ng/author/khalid-idris-doya/
    Tsohon Mai Neman Takarar Gwamnan Bauchi, Bala Jibrin, Ya Fice Daga APC Kan Zargin Ɗoki-ɗora
  • Khalid Idris Doya
    https://hausa.leadership.ng/author/khalid-idris-doya/
    ‘Yansanda Sun Cafke Tsoho Mai Shekara 70 Kan Zargin Yi Wa ‘Yar Shekara 8 Fyaɗe A Bauchi

MASU ALAKA

Ballon D'or
Manyan Labarai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026
Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue
Manyan Labarai

Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue

September 8, 2026
2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi
Manyan Labarai

2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi

September 8, 2026
Next Post
Kiristoci Ma Na Iya Shiga Cikin Shirin Auren Gata Na Kano – Hisbah

Kiristoci Ma Na Iya Shiga Cikin Shirin Auren Gata Na Kano - Hisbah

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.