Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya nada Sanata Dino Melaye da Dakta Daniel Bwala a matasayin masu magana da yawunsa a yakin zaben shugaban kasa da ke tafe a 2023.
Atiku Abubakar ya bayyana haka ne a sanarwar da mai bashi shawara a bangaren yada labarai, Mr Paul Ibe ya sanya wa hanun aka kuma traba wa manema labarai a Abuja ranar Alhamis, ya kuma ce, nadin ya fara aiki ne a nan take.
- Atiku Da Tinubu Sun Fara Cacar Baki Kan Zaben 2023
- Za Mu Ceto Zamfara, In Ji Atiku Yayin Da Ya Amshi Baƙuncin Dauda Lawal
Dinol Malaye, wanda dan garin Ayetoro Gbede da ke karamar hukumar Ijumu ta jihar Kogi, ya kuma wakilci mazabar kogi ta yamma a majalisar daddatawa ta 8.
Daniel Bwala, kuwa ya fito ne daga Jihar Adamawa, ya kuma kasance kwarraren lauye ne kafin wannan nadin.