Dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya yi alkawarin kafa wani kwamiti mai zaman kansa na ƙwararru domin binciken yadda aka kashe ko raba Naira biliyan 33.75 da aka ce an ware wa gidaje miliyan 3.29 masu fama da ƙalubalen tattalin arziki. Wannan ya biyo bayan wani rahoton bincike da ya haifar da tambayoyi kan ko kuɗin sun isa ga waɗanda aka tanadar musu.
Atiku, ta hannun Babban Mataimakinsa kan Sadarwa, Phrank Shaibu, ya ce rahoton ya nuna gazawar gwamnatin Shugaba Bola Tinubu wajen tabbatar da cewa tallafin da aka yi alkawarin bai wa talakawa ya isa gare su. Ya ce bayan cire tallafin man fetur da ƙarin haraji da kuɗaɗen ayyuka, ana kuma fuskantar tambayoyi kan inda kuɗin tallafin da aka ware wa marasa galihu suka shiga.
A cewar Atiku, idan aka raba Naira biliyan 33.75 tsakanin gidaje miliyan 3.29, kowane gida zai samu kusan Naira 10,258 kacal. Ya ce abin damuwa shi ne yadda hatta wannan ƙaramin tallafin ake fuskantar matsala wajen tabbatar da sahihiyar hanyar da kuɗin suka bi zuwa ga waɗanda aka nufa da su.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ce idan aka zabe shi a 2027, gwamnatinsa za ta tabbatar da cikakken bincike kan lamarin tare da bin diddigin kuɗaɗen jama’a. Ya kuma jaddada cewa duk wani tallafin da aka ware domin rage wa ’yan Nijeriya radadi ya kamata a yi amfani da shi bisa gaskiya da cikakken lissafi.
Atiku ya ce ba za a iya magance matsalar yunwa da tsadar rayuwa ta hanyar magana ko sanarwa kawai ba, yana mai buƙatar gwamnati ta tabbatar da cewa kuɗaɗen da aka ware domin tallafa wa talakawa sun isa ga waɗanda suke cikin buƙata.














