ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, September 12, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Atiku Ya Yi Zazzafar Suka Ga Gwamnatin Tinubu Kan Matsalar Tsaro

by Abubakar Sulaiman
4 months ago

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya soki gwamnatin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu kan abin da ya bayyana a matsayin ƙoƙarin kare yawan bashin da ƙasar ke ci gaba da ciyowa duk da matsin tattalin arziƙi da rashin tsaro da ƴan Nijeriya ke fuskanta.

Atiku ya mayar da martani ne ga kalaman fadar shugaban ƙasa da suka ce bashin Nijeriya bai kai na wasu ƙasashen Afirka ba. A cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin sadarwa, Phrank Shaibu, ya fitar, Atiku ya ce gwamnati ba ta san halin da talakawa ke ciki ba.

Ya ce babu wata gwamnati mai hankali da za ta auna ci gaban tattalin arziƙi da yawan bashin da ƙasa ke bi, maimakon ta duba rayuwar jama’a, da tsaro, da samar da ayyukan yi da walwalar al’umma. Ya zargi gwamnatin da mayar da shugabanci tamkar aikin farfaganda yayin da rayuwar jama’a ke ƙara taɓarɓarewa.

ADVERTISEMENT

“A lokacin da miliyoyin ƴan Nijeriya ba sa iya cin abinci sau daya a rana, iyaye na cire ƴaƴansu daga makaranta saboda tsadar rayuwa, kuma mutane na kasafin kuɗin fansa idan masu garkuwa da mutane sun kamma su kamar yadda ake shirya wa biyan kuɗin makaranta, gwamnati na murnar yawan bashin da ake bin Nijeriya,” in ji Atiku.

Atiku Abubakar ya kuma ce rashin tsaro ya ƙara tsananta, inda ya yi zargin cewa manoma ba sa iya zuwa gonakinsu saboda hare-haren ƴan bindiga da masu tayar da ƙayar baya. Ya buƙaci gwamnatin tarayya ta mayar da hankali wajen magance matsalolin tsaro da tattalin arziƙi maimakon dogaro da yaɗa farfaganda.

LABARAI MASU NASABA

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

Rashin Mulki Ke Firgita Atiku – Kakakin APC Na Kaduna

Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Mutane 24 Sun Mutu Bayan Shan
  • Abubakar Sulaiman
    Ɗalibai Sun Yi Watsi Da Tallafin Data, Sun Nemi Wi-Fi Kyauta A Makarantu Daga Gwamnati
  • Abubakar Sulaiman
    Yaƙin Amurka Da Iran Ya Janyo Asarar Fitar Da Ganga Biliyan 2.8 Na Mai
  • Abubakar Sulaiman
    Zan Dawo Da Tallafin Mai Ne Don Rage Farashin Fetur Da Na Sufuri – Atiku

MASU ALAKA

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu
Manyan Labarai

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
Rashin Mulki Ke Firgita Atiku – Kakakin APC Na Kaduna
Siyasa

Rashin Mulki Ke Firgita Atiku – Kakakin APC Na Kaduna

September 9, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027
Siyasa

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Next Post
“Ko Ganduje Ya Taɓa Zama Yarona” -Kwankwaso Ya Sake Martani Ga Gwamna Yusuf

“Ko Ganduje Ya Taɓa Zama Yarona” -Kwankwaso Ya Sake Martani Ga Gwamna Yusuf

LABARAI MASU NASABA

Masu Kera Motoci Na Kasar Sin Sun Lashe Lambobin Yabo Da Dama A Bikin Nune-nunen Motoci Na Turin

Masu Kera Motoci Na Kasar Sin Sun Lashe Lambobin Yabo Da Dama A Bikin Nune-nunen Motoci Na Turin

September 12, 2026
Kwamitin Sulhu Na MDD Ya Amince Da Tsawaita Takunkuman Sudan Na Gajeren Lokaci

Kwamitin Sulhu Na MDD Ya Amince Da Tsawaita Takunkuman Sudan Na Gajeren Lokaci

September 12, 2026
Xi Ya Gana Da Modi A New Delhi

Xi Ya Gana Da Modi A New Delhi

September 12, 2026
2027: Masana Sun Yi Gargaɗi Game Da Bangar Siyasa Da Kalaman Ɓatanci

2027: Masana Sun Yi Gargaɗi Game Da Bangar Siyasa Da Kalaman Ɓatanci

September 12, 2026
Kwamitin Sulhu Na MDD Ya Bayyana Damuwa Game Da Yadda Yanayin Hare-haren Ta’addanci Ke Sauyawa

Kwamitin Sulhu Na MDD Ya Bayyana Damuwa Game Da Yadda Yanayin Hare-haren Ta’addanci Ke Sauyawa

September 12, 2026
Mutane 24 Sun Mutu Bayan Shan

Mutane 24 Sun Mutu Bayan Shan

September 12, 2026
Tsohon Shugaban PDP Na Ƙasa Bamanga Tukur Ya Rasu Yana Da Shekara 91

Tsohon Shugaban PDP Na Ƙasa Bamanga Tukur Ya Rasu Yana Da Shekara 91

September 12, 2026
Gwamnatin Katsina

Abinda Kasafin Gwamna Raɗɗa Na Shekarar 2027 Ya Ƙunsa

September 12, 2026
Ɗalibai Sun Yi Watsi Da Tallafin Data, Sun Nemi Wi-Fi Kyauta A Makarantu Daga Gwamnati

Ɗalibai Sun Yi Watsi Da Tallafin Data, Sun Nemi Wi-Fi Kyauta A Makarantu Daga Gwamnati

September 12, 2026
Yaƙin Amurka Da Iran Ya Janyo Asarar Fitar Da Ganga Biliyan 2.8 Na Mai

Yaƙin Amurka Da Iran Ya Janyo Asarar Fitar Da Ganga Biliyan 2.8 Na Mai

September 12, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.