ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, June 24, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Aure Ba Sana’a:Imani Ko Ganganci?

by Rabi'at Sidi Bala
1 month ago
Aure

Shafin TASKIRA shafi ne da ya saba zakulo muku batutuwa daban-daban wadanda suka shafi al’umma.

Tsokacinmu na yau, zai yi duba game da matasa. Wasu daga cikin matasa maza a yanzu, na kallon yin aure ba tare da kwakkwarar sana’ar da za ta rike iyali ba, ya fi su zauna suna kallon kannen kannensu na yin aure, ko da kuwa shekarunsu babu yawa. Kamar yadda wasu daga cikin matasa masu shekaru 26-27 suka bayyana min cewa; “Ko da namiji ba shi da sana’ar da zai iya rike iyali sai iya kansa kadai, da zarar ya nemi aure to, Allah zai kawo masa mafita ya buda masa. Haka kuma idan bai samu budi a wannan lokacin ba to, da zarar an yi auren Allah zai kawo masa mafita”. A cewar su, da su zauna ‘yan shekara 23 zuwa 24 suna yin aure kannen kannensu ya fi ace sun nemi haya sun kukuta sun yi aure ko da ba su da kwakkwarar sana’a ko ingantaccen karatu, domin yanzu rayuwar tsarinta daban ne.

Dalilin hakan ya sa wannan shafi jin ta bakin wasu daga cikin mabiya shafin game da wannan batu; “Ko me za a ce akan hakan?, Ko akwai wani sirri wanda sauran matasa maza basu sani ba na ci gaban rayuwarsu game da hakan?”.

ADVERTISEMENT

Ga dai bayanan nasu kamar haka:

Sunana Abba Abubakar Yakubu, daga Jos, a Jihar Filato:

LABARAI MASU NASABA

Bukatar Rike Sirri A Tsakanin Ma’aurata

Alfanu Da Rashin Alfanun Tallata Hotunan Ango Da Amarya Kafin Daura Aure

Aure ga namiji shi ne ya fi samun jinkiri, saboda shi ne zai dauko nauyin kula da mata. Don haka ana bukatar ganin ya samu wani abin dogaro, kamar sana’a mai kwari, ko wani aiki da yake samun rufin asiri, domin ya iya samun damar daukar dawainiyar gidansa. A duk lokacin da aka ce namiji na son aure, alhalin ba shi da sana’ar da yake yi to, babu shakka za a fuskanci matsala, musamman idan ba shi da gatan iyaye ko ‘yan’uwan da za su rika tallafa masa. Hakki ne mai girma akan duk wanda zai yi aure ya tabbatar ya cika ka’idojin aure, da suka hada da hankali, balaga, lafiya, da kuma sana’ar da zai rike iyali. Ba lallai sai mai arziki ko mai gida da mota ne zai yi aure ba, amma dai akalla ya zama mutum yana da madogara, kuma yana da karfin da zai dauki nauyin kansa da na matarsa. Shawarata ga samari shi ne a tashi a nemi sana’a, a samu rufin asirin da za a iya daukar nauyin hidimar aure. Ba a iya tara kudin aure ko akwati kawai aure ya tsaya ba, aure ya shafi abubuwa da dama, na yau da kullum. Ba a gasa da yin aure,don ka ga wani ya yi aure yana kasa da kai, kaima ka ce sai ka yi. Aure, da arziki, da mutuwa duk na Allah ne, kuma kowa da lokacin sa.

Sunana Buwangal, Jihar Adamawa:

Aure ba tare da sana’a ba hadari ne, Allah yana bude hanya amma kana bukatar shiri da aiki. Sirri shi ne, sana’a da shiri kafin aure suna sa rayuwa sauki bayan aure. Shawara, fara da sana’a ko karatu, kada ka yi aure saboda kallon abokanka, dogara ga Allah tare da kokari.

Sunana Aminu Adamu, Malam Madori, A Jihar Jigawa:

To, gaskiya yin hakan kuskure ne, domin a lokuta da dama auren ba ya dorewa saboda matsalar kasa daukar nauyin iyalin. To, gaskiya babu wani amfani ko muhimmanci a cikin wannan al’amari kuma a yanzu yana daya daga cikin dalilai na samun yawaitar mace-macen aure a wannan lokacin. To, shawarata a nan ita ce, ya kamata a fara neman Sana’a kafin neman aure domin hakan zai taimaka wajen samun zaman lafiya a tsakanin ma’aurata.

Sunana Hafsat Sa’eed, Jihar Neja:

Namiji matashi yayi aure ba tare da sana’a ba matsala ce babba, misali ace gidan haya ne kana yin aure, kai ne kudin haya, mace na zuwa ta samu ciki sai a fara maganar haihuwa da abin da za a kashe. Da zarar ta haihu sai rainon da da tarbiyyar da da wahalhalun da, shekara na yi an yaye yaro maganar kudin haya, yaro na girma wani cikin ya samu, yaro ace za a kai shi makaranta lalurar sai ta yi yawa. ‘Yar sana’ar da ake kallon akwai ta sai ta zama babu sai dan buga-buga, gara mutum ya samu sana’ar kanshi tukunna ya samu muhallinshi, idan ma babu muhallin zai iya samun kwakkwarar sana’a ya san yana da sana’ar da za ta rufa masa asiri. Irin wannan ya faru na gani da dama wanda namiji zai je yayi aure bayan yayi auren ya zo babu sana’a, ya kama haya sai a koma roko. Akwai wacce na gani ma, tun da suka biya kudin shekara basu kara biya ba, sun kasa biya saboda matsalolin ciki da haihuwa ga ciyarwa, karshe auren nan rabuwa yayi. Babu wanda zai so ace ya yi aure, kuma auren ya mutu.

Sunana Lawan Ismail (Lisary), Rano a Jihar Kano:

Banzan tunani ne gaskiya suke yi, Eh, akwai tabbas Allah shi ne mai badawa, sannan indai har kana ciyarwa to, Allah zai kara buda ma hanyar samu. Amma kuma sai kana da kokarin neman ko kuma kana da dan abin da za ka rika kokarin neman, sai ka ga Allah ya sanya wa wannan neman albarka. Shawarata, tun wuri su canja tunani, domin a wannan zamanin kana da abun yi ma ya ya aka karkare balle ace babu yau da kullumfa ba wasa ba ce.

Sunana Nazy 1Jibia TB, Jihar Katsina:

A gaskiya yin aure ba sana’a babbar matsala ne, kai koma da sana’ar indai karamar sana’a ce rike mace ba karamin aiki bane wallahi, aure yana mutuwa sosai lokacin nan.

Sunana Sunusi Ibrahim SML:

Hakan gaskiya ba dabara ba ce saka kai cikin damuwa ne da tunani, saboda ka yi abin da kasan ba ka da damar yinsa. Babu wani sirri saka kai cikin halin neman taimako da jawo wa kai raini. Saboda abin da kake samu bai kai yawan bukatunka ba, amma ka karo wani nauyi kanka. Allah shi ya ce ka tashi, shi kuma zai taimake ka, amma ba tashi irin na gasa ba. Kar mutum ya kai kansa inda Allah bai kai shi ba, shi aure lokaci ne kayi hakuri ka yi nema Allah zai taimake ka.

Sunana Amina Umar, Jihar Kano:

Wannan ai mafarki ne da wasu matasan ke yi, dan ni namiji in har ba shi da wata kwakkwarar sana’ar da ta fi karfkin cikinsa ba zan iya aurensa ba, dan a yanzu dai kafin namiji ya samu macen da take son auren namijin da za a rika kukutawa za a dade. Kowacce mace tana son gidan da za ta huta, ko da dai ba me kudi bane ya zama me rufin asiri ne wanda ba zamu wayi gari mu rasa abincin ci ba, balle na magani.

Sunana Sadi Dauda Baturiya, Kirikasamma, A Jihar Jigawa:

Babu shakka a fili take cewa matasan suna yin aure wasu kuma iyaye ko wasu ‘yan’uwansu ko iyayen gidansu a wata harkar arziki suna yi masu a cikin kananun shekaru, a gefe guda kuma ga wasu matasan nan sun kai shekaru sama da 30 amma ba su samu damar yin auren ba, a zahirin gaskiyar magana wannan yana da alaka da kaddarar kowa, shi ya sa ma Manzon Allah (SAW) ya shawarci samari wato matasa cewa, duk wanda ya samu damar yin aure to, ya yi. Wanda kuma bai samu damar yin auren ba to, ya dage da yin azumi domin kare ido da sauran gabbai daga fadawa kogin sha’awa, Tabbas haka ne matukar mutum ya tashi neman aure da kyakkyawar manufa to, tabbas Allah yana kawo masa taimakonsa a kusa ko nesa.

Sunana Munzali Bala Musa, Adakawa Dala, A Jihar Kano:

Shawara zuwa ga maza, kafin ka fara neman aure ka fara neman sana’a tukunna, domin masu iya magana sun ce zuwa da wuri ya fi zuwa dawurwuri. Ka nemi sana’a idan ka nemi sana’a aure shi zai nemeka da kansa, dan kana da abin da za ka iya ciyar da matar. Shawara ta biyu, zuwa ga ‘ya’ya mata kada ki sake ki bata lokacinki a banza ga saurayin da bai da sana’a, domin shi ma ba ya iya ciyar da kansa balle ya ciyar da ke. Ki nemi me abin yi ko da lebura ne, watarana shi ma Allah zai bashi nasa jarin, idan kunne ya ji jiki ya tsira.

Sunana Sadik Abubakar Abdullahi, Rijiyar Lemo, Karamar hukumar Dala, Jihar Kano:

Wasu matasa na ganin cewa ko ba su da cikakkiyar sana’a, yin aure na iya zama sanadin budewar arziki da samun cigaba, domin Allah kan kawo mafita bayan mutum ya dauki matakin neman halal. Wannan tunani yana da wani bangare na gaskiya idan mutum yana da kokari da juriya da niyyar daukar nauyin iyali. Sai dai kuma bai dace matashi ya shiga aure ba tare da wani shiri ko tunanin yadda zai kula da iyalinsa ba. Aure ba rayuwa ce ta soyayyar waje ba, ibada ce da ta kunshi nauyin ciyarwa, kula da gida, da tarbiyyar yara. Haka kuma, jiran sai mutum ya mallaki duk abin da yake so kafin aure ma na iya jawo jinkiri mara amfani. Saboda haka hanya mafi dacewa ita ce matashi ya hada tawakkali da aiki, ya nemi sana’a ko wata hanyar dogaro da kai, sannan ya yi aure cikin tsari da fahimtar nauyin da ke kansa.

Aure
Rabi'at Sidi Bala
+ postsBio
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    Zan Iya Auren Namiji Komai Talaucinsa Muddin Muna Son Junanmu -Maryam Labarina
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    Gidajen Gala Ne Kadai Mafita Ga Masana’antar Kannywood – Falalu Dorayi
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    Bukatar Rike Sirri A Tsakanin Ma’aurata
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    GORON JUMA’A

MASU ALAKA

Bukatar Rike Sirri A Tsakanin Ma’aurata
Taskira

Bukatar Rike Sirri A Tsakanin Ma’aurata

June 13, 2026
Alfanu Da Rashin Alfanun Tallata Hotunan Ango Da Amarya Kafin Daura Aure
Taskira

Alfanu Da Rashin Alfanun Tallata Hotunan Ango Da Amarya Kafin Daura Aure

June 6, 2026
Yadda Al’umma Suka Gudanar Da Bukukuwan Sallah Duk Da Matsin Tattalin Arziki
Taskira

Yadda Al’umma Suka Gudanar Da Bukukuwan Sallah Duk Da Matsin Tattalin Arziki

May 29, 2026
Next Post
Ya Kamata A Aiwatar Da Matsayar Da Shugabannin Sin Da Amurka Suka Cimma Tare Da Bude Sabon Babin Huldar Kasashen Biyu

Ya Kamata A Aiwatar Da Matsayar Da Shugabannin Sin Da Amurka Suka Cimma Tare Da Bude Sabon Babin Huldar Kasashen Biyu

LABARAI MASU NASABA

Trump Ne Zai Jagoranci Bayar Da Kofin Duniya A Wasan Ƙarshe – Infantino

Trump Ne Zai Jagoranci Bayar Da Kofin Duniya A Wasan Ƙarshe – Infantino

June 24, 2026
‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta

’Yansanda Sun Kama Wani Mutum da Harsasai 174 A Nasarawa

June 24, 2026
Sojoji Sun Kama Ɗan Fashi Da Makami A Taraba

Sojoji Sun Kama Ɗan Fashi Da Makami A Taraba

June 24, 2026
An Kashe Mutum 2, 8 Sun Jikkata Yayin Rikici A Bauchi

An Kashe Mutum 2, 8 Sun Jikkata Yayin Rikici A Bauchi

June 24, 2026
Tsohon Shugaban APC Na Kebbi Ya Rasu A Hannun ’Yan Bindiga

Tsohon Shugaban APC Na Kebbi Ya Rasu A Hannun ’Yan Bindiga

June 24, 2026
Ya Kamata Sin Da Birtaniya Su Yi Aiki Tare Don Ci Gaba Da Inganta Dangantakarsu

Ya Kamata Sin Da Birtaniya Su Yi Aiki Tare Don Ci Gaba Da Inganta Dangantakarsu

June 23, 2026
Firaministan Sin Ya Jaddada Muhimmancin Kara Azamar Bunkasa Kirar Kayayyakin Aikin Masana’antu Na Zamani

Firaministan Sin Ya Jaddada Muhimmancin Kara Azamar Bunkasa Kirar Kayayyakin Aikin Masana’antu Na Zamani

June 23, 2026
Gombe Ta Zabge Farashin Taki Da Kashi 50 Cikin 100

Gombe Ta Zabge Farashin Taki Da Kashi 50 Cikin 100

June 23, 2026
Wang Yi Ya Gana Da Babban Sakataren Majalisar Tsaron Masar Da Ministan Fadar Gwamnatin Afirka Ta Kudu A Indiya

Wang Yi Ya Gana Da Babban Sakataren Majalisar Tsaron Masar Da Ministan Fadar Gwamnatin Afirka Ta Kudu A Indiya

June 23, 2026
‘Yansanda Sun Kashe Masu Garkuwa Da Mutane 8, Sun Kubutar Da Mutane 3 A Jihar Bauchi

’Yansanda Sun Kama Mutane 57 Da Ake Zargi Da Ayyukan Ta’addanci A Adamawa

June 23, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.