Ribar Manyan Kamfanonin Sarrafa Kayayyaki Na Sin Ta Karu Da Kaso 18.7 A Rabin Farkon Bana
Hukumar kiddidiga ta kasar Sin ta sanar a yau Litinin cewa, ribar manyan kamfanonin sarrafa kayayyaki na kasar ta karu da kaso 18.7 cikin dari a mizanin shekara shekara, a rabin farko na bana. A cewar hukumar, baki daya bangaren ya ci gaba da samun riba mai gwabi a rabin farkon. Kamfanonin, wadanda kowannensu ke samun kudin shigar da ya kai a kalla yuan miliyan 20 a shekara, kwatankwacin dala miliyan 2.95, sun samu jimilar ribar da ta kai yuan triliyan 3.95 daga watan Junairu zuwa Yunin bana. Sai dai, suna ci gaba da fuskantar kalubalen da suka hada da rashin isassun bukatu na kasuwa, rashin wadataccen jarin gudanar da ayyukan, da yanayi mai sarkakiya a wajen kasar, da kuma rashin tabbas kan farashin kayayyaki a kasuwar duniya. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)



















