Sin Ta Yi Kira Da a Gaggauta Tsagaita Bude Wuta Tare Da Yin Tattaunawa Cikin Ruwan Sanyi Tsakanin Amurka Da Iran
Fu Cong, wakilin Sin na dindindin a MDD, ya yi jawabi jiya 27 a yayin taro kan batun nukiliyar Iran...
Fu Cong, wakilin Sin na dindindin a MDD, ya yi jawabi jiya 27 a yayin taro kan batun nukiliyar Iran...
Kasashen Sin da Ghana da wasu karin kasashe 24, sun zamo na farko da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar MDD...
Maaikatar raya aladu da yawon shakatawa ta kasar Sin ko MCT, ta sanar a jiya Litinin cewa, kasuwar yawon bude...
Jiya Litinin ne aka kaddamar da Cibiyar Confucius ta Dijital da Fasaha ta Jami’ar Mulungushi a Jami’ar din da ke...
An gudanar da babban taro kan kirkire-kirkire da ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba na Ziri Daya da...
Babban daraktan hukumar makamashi na bola jari ta kasa da kasa ko (IRENA), Francesco La Camera, ya bayyana a kwanan...
A duniyar da ke cike da dimbin al’umma, samarwa da inganta hanyoyin sufuri, ba wai alfarma ba ce, abu ne...
Kasar Sin ta bayyana cewa tana sa-ido sosai kan halin da ake ciki a yankunan Gabas ta Tsakiya, da Gulf,...
A yau Talata, shugaban kasar Sin, Xi Jinping, ya taya Luiz Inacio Lula da Silva murnar sake zabensa a matsayin...
A yau Litinin, 26 ga watan nan na Oktoba, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, Guo Jiakun, ya bayyana a wani taron manema labarai cewa, fasahar kirkirarriyar basira ta AI wani sabon fanni ne mai kunno kai a cikin harkokin jagorancin duniya, kuma gwaji ne na tantance inganci ga tsarin jagorancin duniya. Tsarin jagorancin duniya yana bukatar kokari na gaske don karfafa wakilci da fada-a-jin kasashe masu tasowa. Guo ya bayyana cewa, kwanan nan a yayin taron dandalin inganta jagorancin duniya na shekarar 2026 (wanda aka gudanar a Xiongan), kasar Sin ta fitar da rahoton ci gaban da aka samu game da "Tsarin gina karfin fasahar AI don amfani da ita ta hanyar da ta dace kuma ga kowa da kowa." Abu na gaba kuma, kasar Sin na maraba da karin kasashe su shiga cikin Kungiyar Hadin Gwiwar Fasahar AI ta Duniya domin binciko karin hanyoyin hadin gwiwar kasa da kasa wajen gina karfin fasahar AI, tare da karfafa ci gaban fasahar AI a duniya domin amfani da ita ta hanyar da ta dace kuma ga kowa da kowa bisa daukar kwararan matakai. Dangane da takardar da kasar Sin ta fitar kwanan nan game da matsayin kasar kan inganta jagorancin harkokin sararin samaniya, Guo Jiakun ya bayyana cewa, wannan babban mataki ne da kasar Sin ta dauka domin aiwatar da abubuwan da ke kunshe a cikin manyan shawarwari na duniya guda hudu da ta gabatar, tare da zurfafa kokarin gina al'umma mai kyakkyawar makoma ta bai-daya ga dan Adam a bangaren sararin samaniya. Kazalika, kasar Sin za ta ci gaba da aiki tare da dukkan bangarori bisa ruhin bude kofa da gina abubuwa masu ma’ana, domin tabbatar da cewa sakamakon ci gaban da aka samu a bangaren sararin samaniya ya zama mai amfanarwa ga daukacin bil’Adama. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.
© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.