Sin Ta Kalubalanci A Tabbatar Da Tsagaita Bude Wuta A Gabas Ta Tsakiya
Mataimakin zaunannen wakilin Sin dake MDD Sun Lei ya yi jawabi a gun taron kwamitin sulhun MDD kan batun nukiliya...
Mataimakin zaunannen wakilin Sin dake MDD Sun Lei ya yi jawabi a gun taron kwamitin sulhun MDD kan batun nukiliya...
Li Shulei, babban jami'i a jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin (JKS) ya bayyana cewa, yin nazari sosai a game da...
Xi Jinping, babban sakataren kwamitin tsakiya na jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin kuma shugaban kasar Sin, da Kim Jong Un, babban sakataren jam'iyyar ma'aikata ta Koriya ta Arewa (WPK) kuma shugaban kasar jamhuriyar dimokuradiyyar jama'ar Koriya (DPRK), sun yi musayar gaisuwar taya murna kan cika shekaru 65 da rattaba hannu kan yarjejeniyar abota, hadin gwiwa da taimakon juna tsakanin Sin da DPRK, a yau Asabar. Yayin da duniya ke fuskantar manyan sauye-sauye da ba a taba gani ba cikin karni guda da ya gabata, Xi ya bayyana aniyar yin aiki tare da Kim don kara karfafa tuntubar juna bisa manyan tsare-tsare, da ci gaba da dora huldar Sin da Koriya ta Arewa a kan turba mai kyau, da kuma jagorantar hadin gwiwa mai kyau tsakanin kasashen biyu don samar da karin alfanu ga al'ummomin kasashen biyu, ta yadda za a ba da gudummawa mai kyau wajen karfafa zaman lafiya da ci gaban yanki. A nasa bangaren, Kim ya ce dangantakar abokantaka da hadin gwiwa tsakanin DPRK da Sin, zabi ne mai muhimmanci kuma wata dukiya mai tsada ta jam'iyyunsu biyu da al'ummominsu biyu. Ya ce, zurfafa huldar abokantaka da hadin gwiwa ta tun filazal tsakanin DPRK da Sin kyakkyawan matsayi ne da WPK da gwamnatin DPRK suka dauka, tare da muhimmanta tsarin gurguzu a cikin huldar, don ci gaba da tafiya daidai da irin sauye-sauyen zamani da burin al'ummomin biyu da kuma samun ci gaba mai karfi a dukkan fannoni. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Kasar Sin ta fitar da shirin kai wa matakin koli na fitar da hayakin Carbon yayin wa’adin shirin raya kasa...
Kasar Sin ta yi nasarar harba rokar dakon kaya samfurin Long March-10B a cibiyar harba rokoki ta Wenchang da ke...
Daga ranar 8 zuwa 11 ga watan Yuli, an gudanar da taron koli na duniya kan "Amfanar da jama’a bisa...
A yau Juma’a ne kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta yi watsi da zargin da wasu kafofin...
An gudanar da taron kara wa juna sani na kasa da kasa game da mahangar Xi Jinping kan gurguzu mai...
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya zanta da shugabar kasar Namibia Netumbo Nandi-Ndaitwah a nan birnin Beijing. Yayin ganawar shugabannin...
Ci gaban bangaren kimiyya da fasaha ya kasance tamkar "kashin baya" ga wata kasa. Dole ne a samu kashin baya mai karfi, kafin daga bisani kasar ta iya kawar da shingen da ya hana ta samun ci gaba mai dorewa a bangaren tattalin arziki. A kwanan nan, an gudanar da babban taron shekara-shekara na karrama masu nazarin kimiyya da fasaha a kasar Sin, inda mutane biyu suka samu lambobin yabo na matsayin koli, kana masana kimiyya da fasaha masu gudanar da wasu ayyuka 258 su ma sun samu lambobin yabo. Wadannan ayyuka sun shafi ilimin wasu bangarori na tushe, wadanda ke samar da taimako wajen biyan bukatar kasar Sin ta raya wasu manyan tsare-tsare, ko kuma haifar da alfanu ga al'ummar kasar. A wajen taron, shugaban kasar Sin Xi Jinping da kansa ya mika lambobin yabon ga mutanen da aka karrama, kana ya yi wani jawabi, inda ya bukaci a karfafa hadin gwiwa tsakanin sassa da hukumomi na Sin a fannin kirkiro sabbin fasahohi, da inganta cudanya tsakanin bangarorin nazarin kimiyya da fasaha da masana'antu, da kara kokarin horar da matasa, da kyautata tsarin kula da kimiyya da fasaha da tabbatar da tsaro, da dai sauransu. Jawabin shugaba Xi ya nuna yadda shugabannin kasar Sin suke fahimtar batun nazarin kimiyya da fasaha, da jagoranci mai nagarta da suke samarwa a wannan fanni. To, sai dai, wane tasiri ci gaban bangaren kimiyya da fasaha na kasar Sin ke da shi ga duniya, musamman ma kasashen Afirka? Dangane da wannan tambaya, wani jami'i mai kula da harkokin waje na kasar Najeriya mai suna Raymond Delmut ya ba da amsa, ta hanyar rubuta wata makala, wadda aka wallafa a shafin yanar gizo na jaridar "the Sun" ta Najeriya. Cikin bayaninsa, Mista Delmut ya ce, yanzu haka kasar Sin na sauya salonta daga "mai samar da hajoji" zuwa "mai kirkiro sabbin fasahohi". Saboda haka salon hadin gwiwar Sin da Afirka shi ma zai sauya, daga mai dogaro kan aikin gini da ciniki, zuwa nau'in da zai fi dora muhimmanci kan kirkire-kirkire, da ci gaban masana'antu, da musayar ilimi. A cewarsa, ci gaban bangaren kimiyya da fasaha na kasar Sin dama ce ga kasashe masu tasowa ta raya tattalin arziki, maimakon barazanar takara. Hakika, ta hanyar tantance sakamakon da aka samu a kasashen Afirka, bisa hadin gwiwar Sin da Afirka a fannin kimiyya da fasaha, cikin sauki za mu iya fahimtar nagartaccen tasirin da kasar Sin ta yi. Misali, a Najeriya, wasu kwararru masu ilimin aikin gona na kasar Sin sun kirkiro wani sabon nau'in shinkafa, wanda ya sa yawan shinkafar da a kan girba cikin gonar da fadinta ya kai eka 1, ya karu daga ton 5.6 zuwa ton 8. Kana a kasar Morocco, tashar samar da wutar lantarki ta makamashin hasken rana da wani kamfanin kasar Sin ya gina tana samar da wutar lantarki mai tsabta ga miliyoyin magidanta. Ban da haka, cibiyar tattara alkaluman labarin kasa ta Sin da Afirka tana samar da hidimar gargadin kare kai daga bala'u ga kasashe 54 dake nahiyar Afirka, yayin da sabon tsarin biyan kudi na zamani da aka gina a tsakanin bangarorin Sin da Afirka ya sa abun da ake kashewa wajen biyan kudi yayin gudanar da ciniki raguwa da fiye da kaso 30%. Haka zalika, allunan sola kirar kasar Sin suna samar da damar amfani da wutar lantarki ga karin mutane a sassa daban daban na nahiyar Afirka. Ta wadannan misalai za mu san cewa, "kashin bayan" kimiyya da fasaha na kasar Sin ya riga ya zame wa kasashen Afirka abin dogara. (Bello Wang)
© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.
© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.