Sin Da Tanzania Da Zambia Sun Karrama Jaruman Sinawa A Bikin Cika Shekaru 50 Da Kafa Layin Dogo Na TAZARA
Kasashen Sin da Tanzania da kuma Zambia sun karrama kwararrun Sinawa wadanda suka sadaukar da rayukansu yayin gina layin dogo...
Kasashen Sin da Tanzania da kuma Zambia sun karrama kwararrun Sinawa wadanda suka sadaukar da rayukansu yayin gina layin dogo...
Da safiyar yau Laraba, an gudanar da taron bayar da kyaututtuka na kimiyya da fasaha na kasa, da babban taron...
A yau Talata, Bankin Duniya ya fitar da sabon rahoton tattalin arzikin kasar Sin a Beijing, inda ya bayyana cewa...
A halin da ake ciki yanzu haka, sassan yammacin Turai na fama da matsanancin yanayi na zafi, shi ma yankin...
A bana ake cika shekaru 30 tun bayan da kasar Sin ta rattaba hannu kan yarjejeniyar MDD ta kare dokar...
Game da zargi da wasu gwamnatocin kasashe da dama suka yi, kan gwajin harba makamai masu linzami da kasar Sin...
Yayin zaman muhawarar gaggawa ta majalissar kare hakkin bil’adama, karkashin babbar taron MDD karo na 62 da ya gudana tsakanin ranaikun 3 zuwa 6 ga watan nan na Yuli, dangane da halin da ake ciki wajen kare hakkin bil’adama a Al Ubayyid na jihar Kordofan ta arewa ta kasar Sudan, da yankunan dake makwaftaka da jihar, mataimakiyar shugaban tawagar Sin Li Xiaomei, ta fayyace matsayar Sin. Li Xiaomei, ta ce ya wajaba a kare muhimman hakkokin bil’adama na al’ummun kasar Sudan kamar hakkin rayuwa. Kazalika, ya dace sassan kasa da kasa su hada karfi waje guda, don shawo kan matsalolin keta hakkin bil’adama, da saukaka ainihin wahalhalun da jama’ar kasar ke fuskanta. Li Xiaomei, ta jaddada cewa ya dace dukkanin tattaunawar majalissar kare hakkin bil’adama ta gudana bisa umarni, da cikakkiyar martabawa ga ikon mulkin kai, da hadin kan al’ummu, da kare martabar yankunan Sudan. Bugu da kari, ya kamata majalisar kare hakkin bil’adama ta MDD ta saurari, da martaba ra’ayoyin kasashe masu nasaba, ta kuma ingiza rungumar dabarun warware matsaloli ta hanyar shawarwari da tattaunawa. (Saminu Alhassan)
Sakatare janar na kwamitin tsakiya na jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana shugaban kasar Xi Jinping ya ba da muhimmin...
Ranar 6 ga watan Yuli ita ce ranar raya kauyuka ta duniya. An kafa wannan rana ne saboda kusan kashi...
An kai kayayyakin taimakon jin kai na gaggawa na farko da gwamnatin Sin ta ba kasar Venezuela zuwa filin jirgin sama na kasa da kasa na Simon Bolivar na birnin Maiquetia da ke kusa da Caracas, babban birnin kasar Venezuela a jiya Litinin. Ministan harkokin waje na Venezuela, Yvan Gil, da jakadan Sin a Venezuela, Lan Hu, sun kasance a filin jirgin don tarbar kayayyakin. Minista Gil ya ce, tun bayan da girgizar kasa mai karfi ta abka wa Venezuela, bangaren Sin yana ta tuntubar gwamnatin Venezuela akai-akai. Ya kara da cewa, wadannan kayayyakin taimakon sun hada da tantuna, janareto da sauransu, kuma suna da matukar muhimmanci ga mutanen da suka rasa gidajensu sakamakon bala’in, tare da nuna dangantakar abokantaka bisa manyan tsre-tsare a ko da yaushe cikin ko wane yanayi da ke tsakanin kasashen biyu, kamar yadda Hausawa ke cewa, Mahdi ka ture. Baya ga haka kuma, ministan ya ci gaba da cewa, bayan aukuwar bala’in, Sinawa mazauna Venezuela da kamfanonin Sin dake kasar sun samar da taimako cikin gaggawa, kana sun shiga aikin ceto tun daga farkon lokacin da abin ya faru, don ba da kulawa ga mutanen da suka rasa matsugunansu, kuma an ga al’amura da dama na kirki masu ratsa zuciya. (Bilkisu Xin)
© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.
© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.