Taron Kara Wa Juna Sani Na Duniya Ya Yi Nazari Kan Kwarewar Kasar Sin Wajen Rage Talauci
An gudanar da taron kara wa juna sani na kasa da kasa game da mahangar Xi Jinping kan gurguzu mai...
An gudanar da taron kara wa juna sani na kasa da kasa game da mahangar Xi Jinping kan gurguzu mai...
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya zanta da shugabar kasar Namibia Netumbo Nandi-Ndaitwah a nan birnin Beijing. Yayin ganawar shugabannin...
Ci gaban bangaren kimiyya da fasaha ya kasance tamkar "kashin baya" ga wata kasa. Dole ne a samu kashin baya mai karfi, kafin daga bisani kasar ta iya kawar da shingen da ya hana ta samun ci gaba mai dorewa a bangaren tattalin arziki. A kwanan nan, an gudanar da babban taron shekara-shekara na karrama masu nazarin kimiyya da fasaha a kasar Sin, inda mutane biyu suka samu lambobin yabo na matsayin koli, kana masana kimiyya da fasaha masu gudanar da wasu ayyuka 258 su ma sun samu lambobin yabo. Wadannan ayyuka sun shafi ilimin wasu bangarori na tushe, wadanda ke samar da taimako wajen biyan bukatar kasar Sin ta raya wasu manyan tsare-tsare, ko kuma haifar da alfanu ga al'ummar kasar. A wajen taron, shugaban kasar Sin Xi Jinping da kansa ya mika lambobin yabon ga mutanen da aka karrama, kana ya yi wani jawabi, inda ya bukaci a karfafa hadin gwiwa tsakanin sassa da hukumomi na Sin a fannin kirkiro sabbin fasahohi, da inganta cudanya tsakanin bangarorin nazarin kimiyya da fasaha da masana'antu, da kara kokarin horar da matasa, da kyautata tsarin kula da kimiyya da fasaha da tabbatar da tsaro, da dai sauransu. Jawabin shugaba Xi ya nuna yadda shugabannin kasar Sin suke fahimtar batun nazarin kimiyya da fasaha, da jagoranci mai nagarta da suke samarwa a wannan fanni. To, sai dai, wane tasiri ci gaban bangaren kimiyya da fasaha na kasar Sin ke da shi ga duniya, musamman ma kasashen Afirka? Dangane da wannan tambaya, wani jami'i mai kula da harkokin waje na kasar Najeriya mai suna Raymond Delmut ya ba da amsa, ta hanyar rubuta wata makala, wadda aka wallafa a shafin yanar gizo na jaridar "the Sun" ta Najeriya. Cikin bayaninsa, Mista Delmut ya ce, yanzu haka kasar Sin na sauya salonta daga "mai samar da hajoji" zuwa "mai kirkiro sabbin fasahohi". Saboda haka salon hadin gwiwar Sin da Afirka shi ma zai sauya, daga mai dogaro kan aikin gini da ciniki, zuwa nau'in da zai fi dora muhimmanci kan kirkire-kirkire, da ci gaban masana'antu, da musayar ilimi. A cewarsa, ci gaban bangaren kimiyya da fasaha na kasar Sin dama ce ga kasashe masu tasowa ta raya tattalin arziki, maimakon barazanar takara. Hakika, ta hanyar tantance sakamakon da aka samu a kasashen Afirka, bisa hadin gwiwar Sin da Afirka a fannin kimiyya da fasaha, cikin sauki za mu iya fahimtar nagartaccen tasirin da kasar Sin ta yi. Misali, a Najeriya, wasu kwararru masu ilimin aikin gona na kasar Sin sun kirkiro wani sabon nau'in shinkafa, wanda ya sa yawan shinkafar da a kan girba cikin gonar da fadinta ya kai eka 1, ya karu daga ton 5.6 zuwa ton 8. Kana a kasar Morocco, tashar samar da wutar lantarki ta makamashin hasken rana da wani kamfanin kasar Sin ya gina tana samar da wutar lantarki mai tsabta ga miliyoyin magidanta. Ban da haka, cibiyar tattara alkaluman labarin kasa ta Sin da Afirka tana samar da hidimar gargadin kare kai daga bala'u ga kasashe 54 dake nahiyar Afirka, yayin da sabon tsarin biyan kudi na zamani da aka gina a tsakanin bangarorin Sin da Afirka ya sa abun da ake kashewa wajen biyan kudi yayin gudanar da ciniki raguwa da fiye da kaso 30%. Haka zalika, allunan sola kirar kasar Sin suna samar da damar amfani da wutar lantarki ga karin mutane a sassa daban daban na nahiyar Afirka. Ta wadannan misalai za mu san cewa, "kashin bayan" kimiyya da fasaha na kasar Sin ya riga ya zame wa kasashen Afirka abin dogara. (Bello Wang)
A yau Juma’a ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da firaministan Koriya ta Arewa Pak Thae Song a...
Asusun ba da lamuni na duniya (IMF), ya fitar da sabon rahoton hasashen tattalin arzikin duniya a jiya 8 ga...
Hukumar kididdiga ta kasar Sin (NBS), ta sanar a yau Alhamis cewa, alkaluman farashin kayayyakin masarufi (CPI) wadanda ke zaman...
Fasahar kirkirarriyar basira ta AI na habaka cikin sauri, daga fasahar da ake gwajinta zuwa wadda ake amfani da ita...
Jam'iyyar kwaminis ta Sin JKS tana jagorantar mutane biliyan 14 don samun ci gaba da tinkarar kalubaloli a nan kasar...
A ’yan shekarun baya bayan nan, duniya na ta ganin karin karbuwar motoci masu aiki da lantarki kirar kasar ko...
Da yammacin yau Alhamis, firaministan kasar Sin Li Qiang ya gana da shugabar kasar Namibiya Netumbo Nandi-Ndaitwah a birnin Beijing,...
© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.
© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.