An Kafa Cibiyar Binciken Wayewar Kai Ta Duniya
A yau Laraba ne aka kafa cibiyar binciken wayewar kai ta duniya a hukumance, wani dandali da aka tsara domin binciken ilimi a mabambantan bangarori, mai babban matsayi, wanda cibiyar nazarin kimiyyar zamantakewar al’umma ta kasar Sin ta kafa. A nan gaba kuma, cibiyar za ta aiwatar da ayyukan nazari, da bayyana shawara kan wayewar kan duniya, kuma za ta rubuta "Littafi mai bayyana ra’ayoyin manazarta game da musayar al'adu", da samar da dakin adana bayanai na binciken wayewar kan duniya da sauransu. Har ila yau, cibiyar za ta ci gaba da samar da sakamakon bincike mai inganci a fannoni masu muhimmanci, kamar ka'idodin wayewar kai, da kwatancen al'adu, da fasahar AI, da ci gaban al'adun duniya, da dogaro da manyan bukatun kasa bisa manyan tsare-tsare, domin samar da tushen tunani, da goyon bayan basira ga gina kyakkyawar makomar bil-Adam ta bai daya. (Amina Xu)



















