Wadanne Dalilai Ne Suke Sabbaba Karin Karbuwar Sin Tsakanin Al’ummun Duniya?
A shekarun baya bayan nan, jerin sakamakon binciken jin ra’ayoyin jama’a daga cibiyoyi mabanbanta, na kara shaida karbuwa, da gamsuwar...
A shekarun baya bayan nan, jerin sakamakon binciken jin ra’ayoyin jama’a daga cibiyoyi mabanbanta, na kara shaida karbuwa, da gamsuwar...
Hukumar makamashi ta kasar Sin ko NEA a takaice, ta kaddamar da shirin bunkasa amfani da makamashi da ake iya sabuntawa, karkashin shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar karo na 15, wanda kasar ke aiwatarwa tun daga shekarar nan ta 2026 zuwa 2030. Kundin da hukumar ta NEA ta fitar da hadin gwiwar hukumar raya kasa da aiwatar da sauye-sauye a yau Alhamis a hukumance, ya nuna cewa ya zuwa shekarar 2030, jimillar karfin samar da makamashin da cibiyoyin da aka kafa na iya kaiwa kusan kilowat biliyan 3.5, inda a duk shekara ake hasashen samar da jimillar lantarkin da ta kai kusan kilowat-awa tiriliyan 6. Kazalika, adadin karfin samar da makamashi ta iska da hasken rana na iya haura kilowat biliyan 2.8, yayin da jimillar lantarkin da za a samar duk shekara za ta haura kusan kilowat-awa tiriliyan 4. Makamashi da ake iya sabunta amfani da shi na nufin wanda ake iya ci gaba da maimaita amfani da shi, da sake sarrafawa ta hanyoyin dabi’a cikin kankanen lokaci. Wadanda suka hada da wanda ake samu daga karfin ruwa, da iska, da hasken rana, da tururin halittu, da dumin karkashin kasa, da wanda ake samarwa daga teku. A daya bangaren kuma, sabbin makamashi na nufin wadanda ake iya samarwa daga sauran fannoni ban da ta karfin ruwa, kamar dai yadda kundin bayanin shirin ya fayyace. (Saminu Alhassan)
Iyaye da sauran jagororin al’umma sun kasance masu nuna damuwa sosai da yanayin karuwar hadurran da ake fuskanta dangane da...
A yau Laraba ne aka kaddamar da taron kasa da kasa na bunkasa hanyar siliki ta dijital na 2026, wanda...
Yau Laraba, asibitin tafi da gidanka na jirgin sojin ruwan rundunar PLA ta Sin watau Auspicious Ark, ya tashi daga...
A yau Laraba ne aka kafa cibiyar binciken wayewar kai ta duniya a hukumance, wani dandali da aka tsara domin binciken ilimi a mabambantan bangarori, mai babban matsayi, wanda cibiyar nazarin kimiyyar zamantakewar al’umma ta kasar Sin ta kafa. A nan gaba kuma, cibiyar za ta aiwatar da ayyukan nazari, da bayyana shawara kan wayewar kan duniya, kuma za ta rubuta "Littafi mai bayyana ra’ayoyin manazarta game da musayar al'adu", da samar da dakin adana bayanai na binciken wayewar kan duniya da sauransu. Har ila yau, cibiyar za ta ci gaba da samar da sakamakon bincike mai inganci a fannoni masu muhimmanci, kamar ka'idodin wayewar kai, da kwatancen al'adu, da fasahar AI, da ci gaban al'adun duniya, da dogaro da manyan bukatun kasa bisa manyan tsare-tsare, domin samar da tushen tunani, da goyon bayan basira ga gina kyakkyawar makomar bil-Adam ta bai daya. (Amina Xu)
Hukumar kula da makamashi ta kasar Sin ta ce jimilar man fetur da gas da Sin ta samar ya kai...
Shugaban kasar Sin, Xi Jinping ya yi kira da a kara kaimi wajen aiwatar da muhimmin aikin gina halaye nagari...
Ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta bayyana cewa, kasar ta nuna matukar rashin amincewarta ga jakadan kasar Philippines bisa tsokanar...
Firaministan Sin Li Qiang, ya aike da sakon taya Andy Burnham murnar hawa mukamin firaministan Birtaniya jiya Litinin. Li Qiang...
© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.
© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.