Beijing Ta Karbi Ziyarce-Ziyarce Miliyan 23.45 Daga Masu Yawon Bude Ido a Lokacin Hutun Ranar Kasa
Hukumar al’adu da yawon bude ido ta birnin Beijing ta kasar Sin ta ba da labari jiya Laraba cewa, a hutun bikin murnar zagayowar ranar kafuwar jamhuriyar jama’ar kasar Sin, Beijing ta karbi ziyarce-ziyarce miliyan 23.45 daga masu yawon bude ido, kuma jimillar kudaden da aka kashe kan yawon bude ido ta kai yuan biliyan 29.49. Daga cikinsu, an karbi ziyarce-ziyarce dubu 126 daga masu yawon bude ido da suka shigo kasar Sin daga kasashen waje, kana yawan kudaden da suka kashe ya kai yuan biliyan 1.37. Alkaluman sun nuna cewa, wuraren yawon bude ido da yankuna guda goma da suka fi karbar masu yawon bude ido a Beijing a lokacin hutun su ne, titin hada-hadar sayayya na Wangfujing, gabar kogin Liangma na kasa da kasa, lambun shan iska na Olympic, titin hada-hadar sayayya na Xidan, yankin filin Tian’anmen, titin Qianmen, lambun shan iska na Tiantan, wurin yawon shakatawa na Shichahai, titin Nanluoguxiang, da wurin tarihi na fadar shakatawar sarakuna wato Summer Palace. (Amina Xu)



















