Wakilin CMG Ya Zanta Da Konstantin Novoselov
Kwanan nan ne wakilin babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG, ya zanta da Konstantin Novoselov, mai lambar karramawa ta Nobel a fannin ilimin fiziks. Novoselov wanda ya samu lambar karramawar lokacin da yake da shekaru 36 a duniya, ya ce, kaifin basirar dan Adam a ko yaushe, shi ne tushen gano kimiyya da tunanin kirkire-kirkire. Da yake bayyana yadda idanuwansa suka shaida ci gaban kimiyya da fasaha da kasar Sin ta samu karkashin shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar, Konstantin Novoselov ya bayyana farin-cikin ganin an samu nasarorin fasaha na zahiri, sakamakon aiwatar da manufofin shirin. Yayin da hadin gwiwar nazarin kimiyya tsakanin kasa da kasa ke fuskantar kalubale daga siyasar duniya a halin yanzu, Konstantin Novoselov, ya ce ba za a iya raba mu’amala da hadin gwiwar kasa da kasa da ci gaban kimiyya ba, inda ya yi fatan ganin ci gaba da karfafar irin wannan hadin gwiwa a nan gaba. (Murtala Zhang)



















