Kwarewar Kasar Sin Na Bayar Da Gudunmuwa Wajen Samar Da Duniya Mai Tsafta
AĀ makonĀ daĀ yaĀ gabataĀ neĀ hukumarĀ kulaĀ daĀ makamashiĀ taĀ kasarĀ SinĀ taĀ ceĀ zuwaĀ karshenĀ watanĀ YulinĀ bana,Ā karfinĀ tashoshinĀ samarĀ daĀ lantarkiĀ dagaĀ haskenĀ ranaĀ naĀ kasarĀ yaĀ kaiĀ kilowattsĀ biliyanĀ 1.286,Ā wandaĀ aĀ karonĀ farkoĀ yaĀ zarceĀ naĀ kwal.Ā WannanĀ yaĀ saĀ haskenĀ ranaĀ yaĀ zamaĀ hanyaĀ mafiĀ girmaĀ taĀ samarĀ daĀ lantarkiĀ aĀ kasarĀ Sin.Ā KumaĀ LantarkinĀ daĀ akaĀ samarĀ dagaĀ haskenĀ rana,Ā yaĀ daukiĀ kasoĀ 31.5Ā naĀ yawanĀ lantarkinĀ daĀ SinĀ takeĀ samarwa.Ā Ā Hakika kasar Sin ta mayar da makamashin hasken rana da ake ganin mai sarkakiya ne zuwa kashin bayan tsarin samar da makamashi a kasar, haka kuma makamashin da ake iya dogaro da shi. Har kullum kasar Sin na kara nuna wa duniya sabbin dabaru da manufofi da kwarewa, dake kara bayyana cewa, babu abun da ba zai yuwu ba, idan har aka jajirce aka samar da kyakkyawan tsari. Wannan ya alamta wata gagarumar nasara da Sin ta samu a kokarin da take yi na sauyawa zuwa amfani da makamashi mai tsafta da kuma rage fitar da hayakin Carbon mai gurbata muhalli. Bugu da kari, gagarumar nasara ce a shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar karo na 15. Mummunan tasirin sauyin yanayi abu ne da ba ya bambance tsakanin kasashe ko alāummomi, lamarin da ya sa shi zama wani batu mai muhimmanci da ya shafi daukacin mutanen duniya. Kasar Sin ta dauki batun tunkarar sauyin yanayi da muhimmanci. Don haka ta kowacce fuska tana iyakacin kokarin ganin ta lalubo hanyoyin da za ta rage fitar da hayaki mai guba domin bayar da gudunmawa ga kare muhalli da halittu da samar da duniya mai tsafta. Tabbas wannan nasara ba ita Sin ba ce kadai, ta duk duniya ce domin za ta kara ba kasashe kwarin gwiwar yin abun da ya kamata na ganin sun samar wa alāummominsu makamashi mai tsafta da za a iya dogaro da shi, wanda kuma zai bayar da gudunmawa ga kokarin da ake yi na yaki da sauyin yanayi. Hakika ci gaban Sin a wannan bangare, yana nufin kasashe za su kara samun alfanu, domin zuwa yanzu, fasahar kasar Sin a wannan bangare na zama daya daga cikin wadanda ke kan gaba a duniya, inda zuwa yanzu ake gaggauta nazari da samar da ingantattun fasahohin samar da lantarki daga hasken rana da za a fara amfani da su a nan gaba. (Faāiza Mustapha)



















