Li Qiang Ya Halarci Bikin Bude Canton Fair Karo Na 140
Da yammacin yau Laraba, firayin ministan kasar Sin Li Qiang ya halarci bikin bude baje kolin kayayyakin shige da fice...
Da yammacin yau Laraba, firayin ministan kasar Sin Li Qiang ya halarci bikin bude baje kolin kayayyakin shige da fice...
Kafofin watsa labarai na kasashen Yamma suna yawan ambatar batun "takarar da ake yi wajen neman mallakar albarkatun ma'adinai na duniya." To, ko mene ne ra'ayin kasar Sin game da wannan batu? Za a samu amsar tambayar, ta hanyar duba kalaman shugaban Kasar Sin Xi Jinping. A jiya Talata, a lokacin ganawarsa da shugaban Botswana Duma Gideon Boko a birnin Beijing na kasar Sin, shugaba Xi Jinping ya gabatar da shawarwari guda hudu game da batun inganta hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka a sana'o'i masu alaka da ma'adinai: Na farko, a tabbatar da cewa albarkatun Afirka na kasashen Afirka ne. Na biyu, a bi ka'idar hadin gwiwa ta tabbatar da adalci da moriya, da kuma fa'idar juna. Na uku, a bi ka'idar neman samun ci gaba mai inganci yayin da ake hadin gwiwa. Na hudu, a yi kokarin samar da yanayin hadin gwiwa mai adalci da bude kofa. Wadannan shawarwari hudu sun nuna fahimtar kasar Sin game da bukatun kasashen Afirka. Sanin kowa ne, babbar matsalar da kasashen Afirka masu albarkatu, ciki har da Najeriya, ke fuskanta, ita ce rashin damar da albarkatun ma'adinai za su haifar da ci gaban tattalin arziki. Saboda haka, bukatun wadannan kasashe su ne: ba wai kawai su fitar da ma'adanai ba, suna kuma fatan habaka masana'antun sarrafa ma'adinai a cikin gida; ba wai kawai su mallaki hannun jari ba, har ma da babban rabo na ribar da ake samu; ba wai kawai jari suke bukata ba, har da fatan samun fasaha, da guraben aikin yi, da kayayyakin more rayuwa. Ke nan, shawarwarin Shugaba Xi Jinping, sun zama masu biyan wadannan bukatu. Shugaba Xi ya ce, "Afirka ta kasance a wani wuri maras samun riba mai tsoka a tsarin masana'antu na duniya, sakamaon rashin adalci da aka samu a tarihin dan Adam, wanda ke bukatar a gyara shi cikin gaggawa." Wannan magana ta nuna babban dalilin da ya sa Afirka ta dade ba ta iya samun ci gaban tattalin arziki bisa albarkatunta na ma'adinai, wato tsarin raba ayyuka tsakanin kasashe daban daban da aka kafa a karkashin tsarin jari-hujja na duniya. Bisa wannan tsari, albarkatun ma'adinai na Afirka ba na kanta ba ne, saboda dole ne a raba moriyar da aka samu bisa haka da sarrafa ma'adinai tare da masu zuba jari na kasashe daban daban. Kana bayan an raba, abin da zai rage a hannun kasashen Afirka ba shi da yawa. Ta yaya za a magance wannan matsalar? Mun san Kasar Sin ma ta taba fama da matsalar, kafin daga bisani ta fitar da kanta daga kangin, abin da ya sa kasar samun fasaha a wannan fanni. Saboda haka, Shugaba Xi ya ce kasar Sin tana son raba fasahohinta ga kasashen Afirka, da taimaka wa kasashen Afirka wajen tsara tsare-tsaren raya bangaren ma'adinai, wadanda za su zama masu dacewa da yanayin da suke ciki. Bayan samun nagartattun manufofi, menene kuma ci gaban bangaren ma'adinai na Afirka ke bukata? Ana bukatar fasaha, da kwararru, da jari, da kuma kayayyakin more rayuwa. Saboda haka, Shugaba Xi Jinping ya ce kasar Sin za ta karfafa gwiwar kamfanoninta don su mika fasahohi ga kasashen Afirka, da samar musu da karin guraben aikin yi, da horar da karin ma'aikata, da habaka bangaren cin bashi, da gina karin ababen more rayuwa masu inganci. Ya kamata a lura cewa duk wani mataki da shugaba Xi ya ambata ya kasance mai biyan bukatun kasashen Afirka. Misali, fasahar da za a mika wa kasashen Afirka, dole ne ta kasance "fasaha mai kare muhalli da ta dace da hakikanin yanayin da kasashen Afirka ke ciki". Kana dole ne bashin da za a samar ya zama "mai araha kuma wanda ba zai haifar da illa ga tattalin arziki ba". Ban da haka, aikin gina ababen more rayuwa dole ne ya kasance "wanda bai wuce karfin kasashen Afirka a fannin tattalin arziki ba", kuma hadin gwiwar da ake yi zai kai ga "taimakawa yunkurin kasashen Afirka na zamanantar da kansu." Dangane da batun "takarar neman samun albarkatu" da kafofin watsa labarai na kasashen yamma suka yi ta yayatawa a duniya, shugaba Xi Jinping ya bayyana ra'ayin kasar Sin a sarari: "Bai kamata albarkatun Afirka su zama wani bangaren da kasashe daban daban ke takara a kai ba." Ya bayyana cewa ra'ayin kasar Sin game da hadin gwiwa a fannin raya bangaren ma'adinai a Afirka ya shafi nuna daidaito da bude kofa, inda Kasar Sin take maraba da duk wani bangare dake son ba da gudummawa ga ci gaban tattalin arzikin Afirka. Kana kasar Sin ba ta da niyyar shiga cikin wata mummunar takara, maimakon haka tana son karfafa hadin gwiwa da kasashen Afirka don samar da wani muhalli mai kyau ga hadin gwiwar da ake yi a fannin raya harkoki masu nasaba da ma'adinai. Wani abu kuma da ya kamata a lura da shi, shi ne yadda shugaba Xi ya ce "ya kamata kasar Sin da kasashen Afirka dukkansu su dauki ra'ayi mai dacewa, da ya shafi adalci da moriya, a hadin gwiwar da ake yi a bangaren ma'adinai." Mene ne "ra'ayi mai dacewa da ya shafi adalci da moriya"? Yana nufin dora muhimmaci kan dukkan adalci da yunkurin samun moriya, har ma a sanya adalci a gaba da moriya, idan babu damar tabbatar da dukkansu a lokaci guda. Kasar Sin ta kuduri aniyar bin ka'idar cewa "albarkatun Afirka na kasashen Afirka ne". Don haka, lokacin da take hadin gwiwa da kasashen Afirka a fannin cin gajiyar albarkatun ma'adinai, za ta yi kokarin taimakawa Afirka wajen samun ci gaban tattalin arziki da suke bukata. Yayin da a nasu bangare, ya kamata kasashen Afirka su tabbatar da kare moriyar kasar Sin yayin da suke hadin gwiwa da ita. Shawarwarin da shugaba Xi Jinping ya gabatar a wannan karo suna da ma'ana daya da ra'ayoyin da kasar Sin ta gabatar a baya, kan batun huldarta da kasashen Afirka, wato a mai da hankali kan fa'idar juna, da dora adalci a kan moriya, da kuma kokarin gina al'ummar Sin da Afirka mai kyakkyawar makomar bai daya. Daga mahangar Kasar Sin, tsohon tsarin tattalin arzikin duniya ya riga ya kai karshensa. Bai kamata a bari kasashen Afirka su ci gaba da fama da koma bayan tattalin arziki ba. A kasar Sin, gwamnati ta himmatu wajen tabbatar da wadatar bai daya, da inganta rayuwar jama'a. Kana kasar Sin tana son ganin al'ummun kasashe daban daban sun samu damar jin dadin rayuwa. Saboda sanin kowa ne, ta hanyar ba mutanen duniya karin damammakin raya kai ne kawai, za a iya tabbatar da kwanciyar hankali a duniya, da ci gaban al'ummar dan Adam mai dorewa. (Bello Wang)
An bude taron gyare-gyaren manufar karbar korafe-korafe, da magance matsaloli nan take na Beijing na shekarar nan ta 2026 a...
A yau Talata, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya tattauna da shugaban Botswana Duma Gideon Boko a Beijing, sannan suka...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Mao Ning ta bayyana cewa, ya kamata bangaren Amurka ya bi ka’idar “kasar Sin daya...
An sanar da biranen Shanghai na Sin, da Liverpool na Birtaniya da Charleroi na kasar Belgium, a matsayin birane uku da suka lashe lambar yabo ta birnin kirkire-kirkire. Hukumar lura da kare ikon mullakar fasaha ta kasa da kasa ko WIPO ce ta sanar da sunayen biranen a jiya Litinin 12 ga watan nan. An kuma zabo biranen uku ne daga birane 15 da suka kai matakin karshe na takarar. A karon farko a shekarar nan ta 2026, aka bude damar gabatar da lambar yabo ta birnin kirkire-kirkire ta WIPO ga daukacin birane 194, membobin hukumar ta WIPO, za kuma a ci gaba da bayar da ita ga birane masu hangen nesa bisa kwazonsu a fannin bunkasa kirkire-kirkire, da kago sabbin abubuwa na kere-kere cikin shekaru masu zuwa. A cewar hukumar WIPO, birnin Shanghai na fatan wanzar da kudurorin karfafa matsayinsa, na zama babbar cibiyar kasa da kasa ta kimiyya da fasaha da mallakar fasahohi, yayin da a lokaci guda yake kasancewa mai faffadan tsarin kirkire-kirkire da kere-kere. Kazalika, birnin ya daura aniyar fadada ilmantarwa da bayar da hidimomi a fannin mallakar fasahohi, da cin gajiyar budadden tsarin kirkire-kirkire na ababen more rayuwa da bayanai, da tallafawa masana’antun raya al’adu da kere-kere, da karfafa hade bangarorin bincike, da kamfanoni, da mamallaka sana’o’i da masu zuba jari. (Saminu Alhassan)
Beijing, babban birnin kasar Sin ne, wanda ke da mazauna miliyan 21. A birnin, 12345 ba lambobi ne kawai ba, layin waya ne da ke hada jama'a da gwamnati. Idan ka shiga cibiyar sabis din wayar, za ka ji sautin wayoyi ba tare da tsayawa ba, inda ma'aikata sama da 1700 ke amsa kiran waya daga mazauna birnin, wadanda suke amfani da layin 12345 don bayyana matsalolin da suke fuskanta da kuma bukatunsu. Malam Wang Zhigang mazaunin birnin ne da ke fuskantar matsalar gani, wanda ya sha fuskantar matsaloli da yawa wajen tafiya a yau da kullum. A shekarar 2024, ya yanke shawarar gwada bayyana matsalolin ta hanyar kiran layin 12345. Washegari, wata hukuma mai alaka ta tuntube shi don sanin hakikanin matsalarsa da bukatunsa, sannan ta tura ma'aikata su yi tafiya tare da shi a hanyoyin da yake bi a yau da kullum, don su duba matsalolin da ke tattare da kayayyakin taimako ga masu bukatu na musamman a hanyoyin, tare da daidaita su cikin sauri da kuma inganta sauran abubuwa masu alaka. Kiran waya da Wang Zhigang ya yi daya ne kawai daga cikin korafe-korafe miliyan 200 da wannan layin ya daidaita cikin shekaru bakwai da suka wuce.Tun daga shekarar 2019, gwamnatin birnin Beijing ta kirkiro sabon tsarin daidaita korafe-korafen mazauna birnin da sauri, inda ta samar da layin waya na 12345 da ake iya bugawa dukkan sa’o’i 24 a kowace rana. Jigon wannan tsarin shi ne mayar da korafe-korafen jama'a zuwa hakikanan matakan daidaita harkoki. Daga gyaran lift a tsofaffin gidaje, da cunkoson tituna, zuwa wahalar da baki ke fuskanta wajen rayuwa a Beijing, in ka buga wannan waya, to za a hada ka da wanda zai taimaka wajen daidaita batun. Har ila yau, ta hanyar tattarawa da nazarin bayanan korafe-korafe masu yawa, tsarin ya shigar da matsalolin da suka fi yawa ko suka zama ruwan dare a cikin shirye-shiryen magance su na musamman, tare da kawo gyara tun daga tushen manufofi, ta hakan kuma an kai ga magance "matsala daya" zuwa "baki dayan irin matsaloli". Ta wannan waya, a shekarar 2019 an daidaita matsaloli kimanin miliyan 6 da dubu 960 da mazauna birnin suka bayyana, sai kuma sama da miliyan 11 a 2020, da kusan miliyan 15 a 2021… adadin yana ta karuwa a kowace shekara, kuma a cikin shekaru uku da suka gabata, a kowace shekara adadin ya zarce miliyan 20. Kason korafe-korafen da aka daidaita da kuma gamsuwar da al’umma suka nuna suna karuwa a kowace shekara, kuma a bara duk sun zarce kashi 97 cikin dari. Hakan ya faru ne sakamakon manufar kula da harkokin birnin, wato "birni na jama'a ne, kuma domin jin dadin jama'a ake gudanar da harkokin birnin". Sakatare Janar na jam'iyyar Kwaminis ta kasar Afirka ta Kudu, Solly Mapaila, ya yaba da wannan tsari sosai, inda ya ce,"Da irin wannan tsarin, ba za ka sake gudanar da harkokin birnin ba tare da tushe ba, sabo da zai sa ka san sarai ko jama'a sun gamsu. Wannan shi ne abin da muke kira gudanar da harkoki ta hanyar sanya jama'a a gaba da komai." A nahiyar Afirka, yanzu haka birane na bunkasa da sauri fiye da kowane lokaci. Daga Lagos zuwa Nairobi, daga Alkahira zuwa Johannesburg, karin mutane suna kwarara zuwa birane don neman rayuwa mai kyau. A lokaci guda kuma, ana kara fuskantar matsaloli irinsu cunkoson ababen hawa, karancin gidaje, rashin isassun hidimomi na jama'a da sauransu. Yadda za a inganta tsarin gudanar da harkokin birane tare da biyan bukatun jama'a ya zama babban darasi ga gwamnatocin kasashen Afirka, kuma tsarin birnin Beijing yana samar da wasu abubuwan koyo: Na farko, hanyar da ba ta da wahala wajen bayyana bukatu tana da muhimmanci sosai. Layin waya mai sauki kuma ba tare da an biya sisi ba, zai iya zama "gada ta farko" tsakanin gwamnati da jama'a. Ba ya bukatar mazauna su san fasaha ko su iya amfani da intanet, kira karo daya kawai, za a ji muryarsu. Na biyu, tsarin tara bayanai da mayar da martani abu ne da ba za a rasa shi ba. A cikin shekaru 7 da suka wuce, Beijing ya saurari korafe-korafe miliyan 200, wanda ke nufin an tattara bayanan kula da harkokin birni masu yawa cikin tsarin, tare da yin nazari da kuma amfani da su. Ana iya ganin sassan da matsaloli suka fi yawa a fili, ta hanyar tarawa da kuma nazarin bayanan. Na uku, rigakafi ya fi magani. Tsarin na Beijing ba ya nufin sauraron korafe-korafe kawai, ya fi jaddada magance matsaloli kafin su kunno kai, wato daga magance matsala daya za a kai ga magance matsaloli makamancinsa. Misali, idan wani yanki ya sha samun korafin bacewar murfin rijiya, gwamnati ba za ta gyara murfin guda daya kawai ba, a'a, za ta duba gaba dayan yankin don gano hadarin da za a iya fuskanta. Hakan yana da matukar ma’ana ga biranen Afirka, wato maimakon a gaji da gudu don fuskantar matsalolin gaggawa iri-iri, gwamma a magance su kafin faruwarsu. Daga ranar 12 zuwa 13, an gudanar da taron dandalin tattauna tsarin mai da martani da sauri ga korafe-korafen al’umma na shekarar 2026 a birnin Beijing, inda baki sama da 3200 daga kasashe da yankuna sama da 70 suka taru, suka mai da hankali kan batun gudanar da harkokin birni. Cikin shekaru 7 da suka wuce, Beijing ya bude wata sabuwar hanya ta zamani wajen gudanar da harkokin babban birni. Tabbas, ba za a iya kwaikwayon tsarin kai tsaye ba. Kasancewar biranen Afirka suna da tarihinsu, al'adunsu da tsarinsu na musamman, don haka dole ne a daidaita da yanayin gida. Amma ainihin manufar tsarin nan na Beijing, wato sanya bukatun jama'a su zama karfin da ke tafiyar da harkokin birni, tana da ma'ana ta gama gari. Kamar yadda taken dindindin na taron, "Birnin Jama'a, Kirkirar Kyakkyawar Rayuwa Tare", ya bayyana, makasudin karshe na tafiyar da harkokin birni shi ne, kowane mazauni ya ji rayuwarsa ta ingantu.
An gudanar da taron kasa kan batun kiwon lafiya a nan birnin Beijing, daga ranar 12 zuwa 13 ga watan nan. Kuma shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci taron tare da gabatar da jawabi. A cikin jawabin nasa shugaba Xi ya jaddada cewa, lokacin aiwatar da "shirin raya tattalin arziki da zamantakewar al’umma na shekaru biyar-biyar karo na 15", lokaci ne mai muhimmanci na cimma burin gina Sin mai lafiya nan zuwa shekarar 2035, kuma dole ne a nace ga bin hanyar ci gaban kiwon lafiya mai halayyar musamman ta Sin, da aiwatar da manufofin kiwon lafiya a sabon zamani, da kuma ingiza ci gaban ingantattun hidimomin kiwon lafiya. Kazalika, a karfafa matakin kula da lafiyar jama'a, da tabbatar da samun ci gaba na a zo a gani a wannan bangare. Xi ya kuma nuna cewa, lafiyar jama'a wata muhimmiyar alama ce ta ci gaban al'umma da karfin kasa. Tun daga babban taron JKS karo na 18, kwamitin kolin JKS ya dora muhimmanci matuka kan aikin kiwon lafiyar jama'a, ya tsara manufofin aikin kiwon lafiya na sabon zamani, kana da yanke babbar shawara kan raya sha’anin tabbatar da lafiyar jama’ar Sin. Ban da wannan kuma, ya ingiza gina tsarin kiwon lafiya da na maganin gargajiya, da na rigakafi da kula da cututtuka, da tsarin inshorar lafiya mafi girma a duniya, matakin da ya sa aikin kiwon lafiya ya samu gagaruman nasarori a kowane fanni. (Amina Xu)
Wasu mutanen Japan na daukar sabbin matakai masu cike da wayo da nufin jirkita tarihi. Bisa labarin da aka bayar kwanan nan, an ce, masu ra’ayin rikau na Japan na baiwa manyan tsarukan fasahar AI na duniya bayanai na jabu kan tarihin yakin duniya na 2, don tsarukan su rika fitar da amsoshi masu dauke da ra’ayoyin da ba su dace ba game da tarihi in an yi musu tambaya, inda suka bayyana harin da Japan ta kaiwa Sin a ranar 7 ga watan Yulin shekarar 1937 don yunkurin mamaye Sin a matsayin “Rikicin Soji Tsakanin Japan da Sin”, tare da bayyana “kisan kiyashin da sojojin Japan suka aikata a birnin Nanjing” a matsayin “Cin tura da Sin ta yi a Nanjing”. Har ila yau, sun gyara zaluncin mamayar da Japan ta yi wa yankin kudu maso gabashin Asiya a matsayin “Kula da Albarkatun yankunan kudu da Japan ta yi ”. Daga gurbata littattafan tarihi, zuwa kirkirar bidiyon karya na fasahar AI, zuwa sanya guba cikin bayanai, masu ra’ayin rikau na Japan na ci gaba da yunkurin kirkirar sabbin hanyoyi don wanke tarihin mamayar da ta dade tana gudanarwa. Ba shakka, masu ra’ayin rikau na Japan ke aikata zambar ne don taimaka wa gwamnatin kasar wajen “farfado da karfin soja a Japan”, wanda hakan ya kara mai da “sabon salon ra’ayin nuna karfin soja” ya zama barazana ga duniya. (Amina Xu)
Yau Talata da rana, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da shugaban majalisar ministocin kasar Togo Faure Essozimna Gnassingbe, wanda ke ziyara a kasar Sin. Yayin tattaunawar, Xi Jinping ya gabatar da wasu ka’idoji 4 kan yadda bangarori daban-daban za su shiga a dama da su wajen warware manyan batutuwan da ke ci wa Afrika tuwo a kwarya. Ka’ida ta farko ita ce, daukaka shugabancin Afrika, watau al’ummar nahiyar ne ya kamata su zama jigon jagorantar harkokinta. Ka’ida ta biyu, daukaka adalci da gaskiya, watau bangarori masu ruwa da tsaki su kiyaye manufofi da ka’idojin kundin tsarin mulki na MDD da girmama cikakken ‘yanci da ikon kasashe masu ruwa da tsaki. Ka’ida ta uku ita ce, inganta dakatar da rikice-rikice da neman zaman lafiya. Ya ce yaki da kakaba takunkumai daga bangare guda, ba za su warware rikice-rikice tsakanin kasa da kasa ba, don haka ya zama wajibi a nacewa martaba juna da tuntubar juna da neman yanayin da zai karbu ga kowa da hakuri da bambance-bambance da fahimta da hakuri da juna. Sai ka’ida ta hudu, watau magance alamomi da tushen matsaloli. Ya ce ya kamata a yi kokarin mayar da hankali kan bukatun tsaro na gaggawa yayin da ake tsara hanyoyin samun ci gaba mai dorewa. A nasa bangare, Faure Gnassingbe ya ce kasarsa ta amince da muhimman ka’idojin da shugaba Xi Jinping ya gabatar game da hanyoyin da bangarori daban-daban za su bi wajen warware manyan matsalolin Afrika, kuma yana jinjina wa muhimmiyar rawar da Sin ke takawa wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankalin duniya da magance kalubalen duniya bisa hadin gwiwa. Baya ga haka, shugabannin kasashen biyu sun sanar da daga darajar dangantakar kasashen Sin da Togo zuwa ta hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.
© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.