Shugaba Xi Ya Aika Da Sakon Taya Murna Gabanin Bikin Girbi Na Manoman Kasar Sin
Xi Jinping, babban sakataren kwamitin tsakiya na Jam’iyyar Kwaminis ta Sin(JKS), ya aika da sakon taya murna da gaisuwa ta musamman a madadin kwamitin tsakiya na JKS ga manoma da sauran masu aiki a sahun gaba a fannin noma da raya karkara, gabanin bikin girbi na manoman kasar Sin karo na tara. Xi, wanda har ila yau shi ne shugaban kasar Sin kuma shugaban hukumar soja ta tsakiya, ya jaddada muhimmancin daukar kwararan matakai don raya yankunan karkara a dukkan fannoni, tare da tabbatar da cewa manoma suna gudanar da kyakkyawar rayuwa cikin farin ciki. Xi ya yi nuni da cewa, a bana, yawan hatsin da aka girbe lokacin zafi a kasar Sin ya kai wani sabon matsayi, yayin da yawan shinkafar da ake girbewa da wuri ya ci gaba da dorewa ba tare da tangarda ba, kana ana sa ran samun girbi mai albarka a lokacin kaka. Kazalika, ya ce ya kamata kwamitocin jam’iyya da hukumomin gwamnati a dukkan matakai su yi aiki don tabbatar da cewa manufofin da aka samar da nufin karfafa aikin gona, da amfanar da manoma, da kuma habaka yankunan karkara sun haifar da gagarumin sakamako mai kyau, tare da kara karfin noma amfanin gona baki daya, da habaka inganci da kwazon sashen aikin gona. Bikin girbi na manoman kasar Sin dai biki ne na matakin kasa na farko da aka kirkiro musamman domin manoman kasar. A bana, bikin zai gudana ne a gobe Laraba. (Abdulrazaq Yahuza Jere)



















