An Gudanar Da Taron Kirkire-Kirkire Na Duniya Na Kafafen Yada Labarai Karo Na Biyar
A Birnin ChongqingAn gudanar da taron kirkire-kirkire na duniya na kafafen yada labarai karo na biyar a yau Laraba 10...
A Birnin ChongqingAn gudanar da taron kirkire-kirkire na duniya na kafafen yada labarai karo na biyar a yau Laraba 10...
Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun kai mummunan hari ranar Laraba a al’ummar Iluke-Bunu da ke karamar hukumar...
Harkokin zirga-zirga da na tattalin arzikin sun samu karin karfi a Abuja, babban birnin Nijeriya, bayan kaddamar da wani muhimmin...
Yau Laraba rana ce ta karfafa cudanyar mabambantan al’adu na duniya. Kasar Sin ce ta ba da shawara ga Majalisar Dinkin Duniya, don ta kebe wannan rana ta musamman bisa yunkurin samar da damar wanzar da zaman lafiya a duniya, da tabbatar da hadin kai na dan Adam. Hakika idan mun tantance huldar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, to, za mu ga yadda cudanyar al’adu take samar da gudunmowa a kokarinsu na tabbatar da ci gaba na bai daya. Da farko, cudanyar al’adu tana karfafa fahimtar juna tsakanin bangarorin Sin da Afirka. Yanzu haka, a cibiyar adana kayayyakin tarihi dake birnin Cairo na kasar Masar, ana iya ganin tsoffin kayayyaki fadi-ka-mutu masu daraja na kasar Sin, kana a birnin Shanghai na kasar Sin, an taba baje kolin kayayyakin tarihi da na al’adu na kasashen Afirka. Wannan nau’in cudanya da aka rinka yi ta sa jama’ar Sin da na Afirka fahimtar dogon tarihi da al’adu masu daraja na sassan biyu. Kana ta hanyar cudanyar, sun fahimci cewa, babu wasu al’adu da suka fi wasu daraja, domin suna da matsayi na daidai-wa-daida. Kana dukkan wadannan al’adu na kasashe daban daban a hade suke, sun zama ginshikan wayewar kai ta dan Adam. Ban da haka, yadda bangarorin Sin da Afirka suke girmama al’adun juna shi ma ya zama tushen karfafar huldar dake tsakaninsu. Na biyu shi ne, cudanyar al’adu tana haifar da basira ga kasar Sin da kasashen Afirka, ta yadda suke iya amfani da ita wajen jagorantar ayyukan raya kasa. Ta hanyar gadon al’adu da abubuwan gargajiya, kasar Sin da kasashen Afirka sun samu ilimin da suke bukata wajen zabar turbarsu ta zamanantar da al’umma. A nata bangare, kasar Sin har kullum ta kan ba da shawara ga kasashe daban daban da su dauki hanyar raya kasa da ta dace da yanayin da suke ciki, maimakon bin hanyar da sauran kasashe suka kayyade musu. Ban da haka, ta hanyar raba fasahohinta na raya tattalin arziki, da rage talauci, kasar Sin tana mai da cudanyar al’adu da ilimi ta zama abun dake sa kaimi ga ci gaban tattalin arzikin kasashen Afirka. Sa’an nan, abu na uku shi ne, cudanyar al’adu tana karfafa zumunta tsakanin al’ummun Sin da Afirka. A kowace shekara, dimbin matasa ’yan Afirka su kan zo kasar Sin karatu, inda suke samun karuwar ilimi, da karin fahimta kan tsohon tunanin kasar Sin na “tabbatar da jituwa, da yanayi na kasancewa tare”. Kana a nasu bangare, matasan kasar Sin da yawa suna sha’awar fasahar buga ganguna salon Afirka, da raye-raye nau’in Afirka, yayin da wasunsu ke neman kara fahimtar al’adun kasashen Afirka ta hanyar nazarin harsunansu daban daban. Ban da haka, wasu dandamalin da aka kafa, irinsu taron cudanyar wayewar kai na Sin da Afirka, da shekarar cudanyar al’adu ta Sin da Afirka da aka riga aka kaddamar da ita, da dai sauransu, su ma suna samarwa al’ummun Sin da na Afirka damar fahimtar zumunta, da kaunar da ake samu tsakanin bangarorin 2. A wannan zamani da muke ciki da ake fuskantar barkewar karin rikice-rikice tsakanin kasashe daban daban, cudanyar al’adu tsakanin Sin da Afirka ta zama mai daraja matuka, saboda tana shaidawa al’ummun duniya cewa, mabambantan al’adu, da wayewar kai za su iya zama tare cikin jituwa, da koyi da juna. Kana kasashe masu tasowa za su iya samun hanyoyinsu na zamanantarwa masu dacewa ta hanyar gudanar da hadin gwiwa tsakaninsu. (Bello Wang)
Albarkacin ranar tattaunawa tsakanin mabambantan wayewar kai ta duniya, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya yi kira da...
ADC a jihar Kaduna ta fara wani gagarumin shirin sulhu domin warware rikice-rikicen da suka biyo bayan zabukan fidda gwani...
BangarMataimakin wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Sun Lei ya bayyana a jiya Litinin, yayin da kwamitin sulhu ke...
Wani jami’in rundunar tsaron al'umma ta Sokoto ya rasa ransa, yayin da aka yi garkuwa da mutane da dama bayan...
Babban sakataren kwamitin kolin Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, kuma shugaban kasar Xi Jinping, da babban sakataren jam'iyyar 'yan kwadago...
Majalisar Dattawar Nijeriya a ranar Talata ta bukaci a haramta shigo da yadiddika, Atamfofi da shaddoji gaba daya cikin kasar...
© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.
© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.