ADVERTISEMENT
Sulaiman

Sulaiman

Xi Jinping Zai Bayar Da Lambar Yabo Ta Ranar 1 Ga Watan Yuli Tare Da Gabatar Da Jawabi Albarkacin Cikar JKS Shekaru 105 Da Kafuwa

Xi Jinping Zai Bayar Da Lambar Yabo Ta Ranar 1 Ga Watan Yuli Tare Da Gabatar Da Jawabi Albarkacin Cikar JKS Shekaru 105 Da Kafuwa

Sakatare janar na kwamitin kolin JKS Xi Jinping, zai bayar da lambar yabo ta ranar 1 ga watan Yuli, wadda ita ce lambar karramawa ta koli ta jam’iyyar ga mambobin JKS da ke zaman ababen koyi, yayin wani taro albarkacin cikar Jam’iyyar Kwaminis ta Kasar Sin shekaru 105 da kafuwa.   Xi Jinping wanda shi ne shugaban kasar Sin kuma shugaban hukumar koli mai kula da ayyukan soji, zai gabatar da muhimmin jawabi yayin taron wanda za a fara da karfe 10 na safiyar ranar 1 ga watan Yuli, a babban dakin taron al’umma da ke Beijing.   A ranar 1 ga watan Yulin shekarar 1921 ne aka kafa Jam’iyyar Kwaminis ta Kasar Sin.  Yayin taron na ranar Laraba, za kuma a karrama jajirtattun mambobin jam’iyyar da ma’aikatan jam’iyyar da kungiyoyin jam’iyyar a matakan farko, daga dukkan fadin kasar. (Fa’iza Mustapha) 

Page 2 of 1049 1 2 3 1,049