Lee Ka Chiu: Shirin Shekaru 5 Na Farko Na Raya Yankin Musamman Na Hong Kong Ya Dace Da Muradun Kasar Sin
Da safiyar yau 16 ga watan nan, jami'in farko na gwamnatin yankin musamman na Hong Kong Lee Ka Chiu John ya gabatar da shirin shekaru 5 na farko na raya yankin musamman na Hong Kong ga hukumar kafa dokokin yankin, inda ya bayyana cewa, shi ne karon farko da aka gabatar da shirin, kuma ya zo a daidai lokacin da gwamnatin Sin ta fara aiwatar da shirin ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al'ummar Sin na shakaru biyar-biyar karo na 15. A cewarsa, wannan wani mataki ne da gwamnatin yankin Hong Kong ke dauka don kama hanya iri daya tare da gwamnatin tsakiyar kasar, da kuma shiga a dama da ita don tabbatar da bin tsarin ci gaban kasa yadda ya kamata, kana da kaiwa ga matsaya daya tsakanin al'umma da karfafa hadin gwiwar mabambantan bangarori, ta yadda za a ciyar da Hong Kong gaba daga kwanciyar hankali zuwa samun wadata, da kuma cimma ingantaccen ci gaba. Lee Ka Chiu John ya ce, an kama hanya mafi dacewa ta samun ci gaba da rarraba albarkatu yadda ya kamata da kuma tabbatar da kwanciyar hankalin al’umma a dogon lokaci, da ba da tabbaci ga jin dadin mazauna da muradun masu zuba jari na wurare daban-daban, bisa shirin na shekaru 5. Dadin dadawa, za a kara raya yankin Hong Kong bsia tsarin bude kofa ga ketare da amfanarwa ga kowa, kuma cikin ’yanci da adalci da wadata da tsaro, inda hakan zai sa yankin Hong Kong ya zama mahadar Sin da duniya, da kuma zama yanki mai jawo hankalin kasa da kasa da zai kasance cike da kuzari da damammaki. (Amina Xu)



















