Shahararren dan kwallon kafa a Duniya Lionel Messi ya bayyana cewar bashida tabbacin iya cigaba da taka leda bayan mutuwar mahaifinshi wanda ya kira kashin bayan harkarshi ta kwallon kafa, Jorge Messi ya mutu a makon da ya gabata yanada shekaru 68 bayan doguwar rashin lafiyar da yayi fama da ita, ya kasance wakilin Messi tun lokacin da kyaftin din na Argentina yana dan shekaru 14.
A cikin wani sako da ya wallafa a shafukan sada zumunta, Messi wanda ya lashe kyautar Ballon d’Or sau takwas ya bayyana irin tasirinda mutuwar mahaifinsa zata iya yiwa harkarsa ta kwallon kafa, “Bansani ba ko zan iya cigaba da taka leda bayan mutuwar mahaifina ba, mahaifina yana tare dani tun kafin in zama abinda na zama, ya kasance kashin bayan harka ta ta kwallon kafa na tsawon lokaci” inji Messi a wani rubutu da ya wallafa a shafukansa na sada zumunta.
Kyaftin din na tawagar Argentina ya koma birnin Rosario na kasar Argentina bayan mutuwar mahaifin nashi, inda akayi jana’izarshi a ranar Lahadi a wata makabarta da ke kusa da kauyen Perez, Messi ya kuma bayyana cewa Jorge ne ya roke shi akan ya sake buga wani Kofin Duniya bayan lashe kofin da yayi a shekarar 2022, Messi ya jagoranci kasar Argentina zuwa wasan karshe na Gasar Cin Kofin Duniya na shekarar 2026 da aka kammala, ya zura kwallaye 8 sannan ya taimaka aka jefa kwallo 4.
Messi ya bayyana Jorge a matsayin “mahaifinsa, abokinsa kuma mai ba shi shawara” kuma ya ce tasirinsa zai ci gaba da tsara yadda yake renon yayansa, “zan yi kewarka sosai, amma koyaushe kana cikin raina”, inji Messi, manyan yan wasan kwallon kafa a Duniya sun taya Messi jimamin rashin mahaifinshi, daga cikinsu akwai Cristiano Ronaldo da David Beckham.














