Jarumi kuma mawaƙi a masana’antar Kannywood Garzali Miko ya bayyana cewar babu Inda jarumin fim zai samu kuɗaɗen da zai yi hidimar yau da kullum idan ba a harkar siyasa ba. A wata hira da ya yi da kafar yaɗa labarai ta DCL, mawaƙin ya ce, dole ne ƴan masana’antar ta Kannywood su shiga tsamo-tsamo a dama da su a cikin harkar siyasa domin a nan kaɗai ne za su samu kuɗaɗe a matsayinsu na jarumai.
Yayin da ake ta kace-nace a kan yadda mafi yawancin jarumai a masana’antar shirya fina-finan suka tsunduma ka’in da na’in cikin harkar siyasa ba tare da la’akari da abin da ka iya zuwa ya dawo ba, duba da dubban mabiya da jaruman suke da su a lunguna da saƙo, ƴaniyasa na amfani da su wajen samun magoya baya musamman a wannan lokaci da zaɓukan shekarar 2027 ka gabatowa.
Akwai ƙungiyoyi da dama da jaruman kan kafa na goyon baya ga ƴaniyasa musamman a matakin tarayya, ƙungiyoyi irin su Triple R da makamantansu duka jarumai ko mawaƙa ne ke jagorancinsu, inda suke amfani da ɗaukakar da suke da ita wajen nusar da jama’ar ƙasa dalilan da zai janyo a zaɓi waɗanda suke goyon baya.
Da yake amsa tambaya akan me yake janyo ra’ayin jaruman masana’antar Kannywood shiga siyasa tsamo-tsamo ana damawa da su? Garzali ya ce ba wani abu bane illa neman kuɗi, domin kuwa a siyasa kaɗai za su samu kuɗi a wannan lokaci.
“Ai dole ne mu shiga cikin ƴaniyasa a dama damu, domin kuwa idan ba a siyasa ba, babu ta inda jaruman masana’antar za su samu kuɗaɗe, sannan kuma su jama’ar dake ganin laifinmu don mun shiga siyasa ai sun fi mu zama ƴaniyasa, domin kuwa su taliya kaɗai ta isa ta sa su zaɓi wanda ba su yi niyyar zaɓe ba idan suka hau layin zaɓe,” in ji Garzali Miko, wanda yake ɗaya daga cikin jagororin kamfen ɗin shugaba Bola Tinubu a masana’antar ta Kannywood.














