ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Bai Kamata A Bar Ƴansandan Jiha Ƙarƙashin Gwamnonin Jihohi Ba – Danbazau

by Sani Anwar
4 months ago
Jiha

Laftanar Janar Abdulrahman Dambazau, mai ritaya,  wanda tsohon babban hafsan soji ne, ya bayyana cewa; kafa ƴansandan jihohi, zai yi tasiri ne kaɗai a Nijeriya, idan aka tsaya aka yi abin da ya dace.

Dambazau, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) cewa; dole ne a killace ƴansandan jihohi daga hannun gwamnonin jihohi, domin hana kai wa ƴan adawar siyasarsu hari.

Ya kuma yi kira da kakkausar murya, wajen tantancewa tare da horar da ma’aikatan da za a ɗauka, domin tabbatar da cancanta da kuma daƙile munanan ɗabi’u.

ADVERTISEMENT

Haka zalika, ya ƙara da cewa; dole ne tsarin ya haɗa da samar da daidaito da sa ido da kuma samar da ƙa’idojin aiki, domin hana yiwuwar cin zarafin bil’adama ko ɓullar ƙungiyoyin sa kai na ƙabilanci.

“Aikin yana buƙatar horarwa, kayan aiki, samar da horo, bayyana gaskiya, bin doka da oda da kuma mutunta haƙƙin Ɗan’adam.

LABARAI MASU NASABA

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue

“Don haka, a duk inda ake da ƴansanda na jihohi da na ƙasa, idan ba a inganta ci gabansu ba, to ba za a samu sakamakon da ake buƙata ba.”

Ya ƙara da cewa, dangane da rashin tsaro, al’ummomin da aka fi kai wa hari, su ne yankunan karkara, ya ƙara da cewa; a waɗannan yankunan babu wani batun tabbatar da doka da oda a cikin al’umma.

“Wataƙila shi ya sa mutane ke kira ga ƴansandan jiha, amma babu shakka, aikin ƴansandan jiha, yana buƙatar abin da ƴansandan ƙasar ke buƙata.

“Na yi imanin cewa, mutane suna yin kira a kan hakan ne, saboda suna tunanin tsarin da muke da shi, don haka, idan an raba shi, zai yi aiki, eh, amma zai yi aiki ne kaɗai idan an kyautata shi, an yi abin da ya kamata.

“Idan an ɗauke shi, dole ne a horar da shi da kyau tare da tabbatar da cewa, akwai cikakkiyar ladabtarwa, kuma ana kula da jin daɗinsa yadda ya kamata.

“Dole ne ku tabbatar sun cika mafi ƙarancin ƙa’idojin aikin ƴansanda na duniya, babu shakka, bayan haka, dole ne ku tabbatar da cewa; akwai amana.

Dambazau, wanda yanzu shi ne jakadan Nijeriya da aka naɗa a ƙasar Sin, ya ce; “Wannan shi ya sa a wasu lokutan ma al’ummomi sukan bai wa ƴan fashi kuɗi don kare su daga wasu ƴan fashin.

Ya ƙara da cewa, “Don haka, babu shakka dole ne jihohin su kasance a shirye, domin samar da isassun kuɗaɗe.

Jiha
Sani Anwar
+ postsBio
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Ko Kun San Amfanin Kwanciya Da Bangaren Hagu?
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    2027:Mata Shida Da Ke Takarar Neman Shugabancin Nijeriya
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Dambarwa A Kasuwancin Iyalan Indimi
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Illar Shan Taba Sigari Da Dangoginta

MASU ALAKA

Ballon D'or
Manyan Labarai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026
Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue
Manyan Labarai

Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue

September 8, 2026
2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi
Manyan Labarai

2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi

September 8, 2026
Next Post
Ƙasashen Afirka 10 Da Suka Fi Sayen Makaman Yaƙi

Ƙasashen Afirka 10 Da Suka Fi Sayen Makaman Yaƙi

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.