ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Masana Tattalin Arziki Sun Yi Watsi Da Rahoton NBS Kan Tattalin Arziki

by Yusuf Shuaibu
3 months ago

Masana tattalin arziki sun yi watsi da rahoton hukumar ƙididdiga ta ƙasa (NBS) na farkon zangon 2026, inda suka tabbatar da cewa tsadar rayuwa a Nijeriya na ƙara ta’azzara.

Idan za a iya tunawa dai, rahoton NBS da aka fitar a ranar Litinin ya nuna cewa tattalin arzikin Nijeriya ya ƙaru da kashi 3.89 cikin ɗari a rubu’in farko na shekara ta 2026 idan aka kwatanta da kashi 3.13 da aka samu a rubu’in farko na bara.

Rahoton ya nuna cewa ɓangaren ayyuka ya bayar da gudummawa mafi girma ga jimillar GDP da kashi 57.73, sannan aikin gona da kashi 23.16 da masana’antu da kashi 19.11.

ADVERTISEMENT

Rahoton NBS ya ƙara nuna cewa GDP ya kai naira tiriliyan 110.79, yayin da GDP na haƙiƙa ya kasance tiriliyan 51.36, inda ɓangaren ba na man fetur ba ke ɗauke da kashi 96.08 kan kashi 3.92 na sashen man fetur.

Rahotannin, kamar sauran bayanan GDP na NBS, sun tayar da martani daga ƴan Nijeriya da masu ruwa da tsaki kan hauhawar tsadar rayuwa a ƙasar.

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

An ruwaito cewa tashin farashin makamashi na iskar gas da na girki ke sama da naira 1,500 a kowace kilogram, fetur ya kai naira 1,400 a kowace lita, da dizal kan naira 2,000 a kowace lita sakamakon rikicin gabas ta tsakiya da ya shafe kusan watanni uku.

Da yake magana kan lamarin, tsohon shugaban kuma shugaban cibiyar ‘Chartered Institute of Bankers’ (CIBN), Mazi Okechukwu Unegbu da shugaban ƙungiyar abokan huɗɗar bankun Nijeriya, Dakta Uju Ogunbunka, sun ce GDP ɗin ƙasar bai nuna tasiri ga rayuwar talakawa da ke fama da tsadar rayuwa.

A nasa ɓangaren, Unegbu ya ce duk da ci gaban da aka samu a adadin GDP na ƙasar, rayuwar talakawan Nijeriya ba ta inganta ba.

Unegbu ya ce ci gaban tattalin arziki da aka bayar bai canza zuwa mafi kyawun yanayin rayuwa ga ƴan Nijeriya na yau da kullum ba, yana jaddada cewa hauhawar tsadar rayuwa ya ci gaba da tsananta duk da ingantattun bayanan GDP.

A cewarsa, masana tattalin arziki yanzu suna la’akari da hanyoyi don sake auna GDP don ya dacewa da haƙiƙanin gaskiyar rayuwar ƴan ƙasa ke fuskanta a kan tituna.

Unegbu ya ce ƙaruwar farashin kayayyakin amfani da ayyuka sun ci gaba da ƙaruwa a ƙarƙashin wannan gwamnatin, wanda ke sanya rayuwa ta zama mai wahala ga ƴan Nijeriya.

Kazalika, Ogunbunka ya ce sabon rahoton NBS na GDP ba ya nuna gaskiyar yanayin da ƴan Nijeriya ke fuskanta a rayuwar yau da kullum.

Ya ce cewa duk da batun ci gaban tattalin arziki da aka ruwaito, miliyoyin ƴan Nijeriya har yanzu suna fama da tsadar rayuwa da hauhawar farashin kayayyaki da taɓarɓarewar tattalin arziki.

“Abin takaici, kyawawan ƙididdiga ba su daidaita da gaskiya lamari ba. Rahoton NBS kan ci gaban GDP zuwa kashi 3.89 ya bar fiye da yadda aka zata kan yayin da mutane ke fama da tashin rayuwa,” in ji shi.

Yusuf Shuaibu
+ postsBio
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    2027: APC Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Sake Fasalin Tawagar Yakin Neman Zabe
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin APC Da ‘Yan Adawa Kan Tallafin Gwamnatin Tarayya Ga Magidanta
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    INEC Ta Zayyano Kalubalen Da Ke Iya Shafar Sahihancin Zaben 2027
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    2027:Kamun Ludayin Yakin Neman Zaben Manyan ‘Yan Takarar Shugaban Kasa

MASU ALAKA

Sojoji
Manyan Labarai

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Next Post
Na Cika Kashi 90 Cikin 100 Na Alƙawuran Yaƙin Neman Zaɓe Na – In Ji Gwamnan Kano

Na Cika Kashi 90 Cikin 100 Na Alƙawuran Yaƙin Neman Zaɓe Na – In Ji Gwamnan Kano

LABARAI MASU NASABA

Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.