ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

NPA Da Birtaniya Sun Kulla Yarjejeniyar Zamanantar Da Tashoshin Jiragen Ruwan Nijeriya

by Rabi'u Ali Indabawa
3 months ago
NPA

Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwa ta Nijeriya (NPA) da Birtaniya sun sake tabbatar da aniyarsu ta kara karfafa hadin gwiwa a harkokin ruwa, tare da mayar da hankali kan binciken taswirar ruwa, tsaron zirga-zirgar jiragen ruwa, bunkasa tashoshin jiragen ruwa da kuma gina kwarewar ma’aikata.

Hakan ya biyo bayan wata ziyarar girmamawa da Mataimakin Babban Kwamishinan Birtaniya a Nijeriya, Jonny Badter, Babban Jami’in Hydrographer na Birtaniya, Angus Essenhigh, da jami’an Ofishin Hydrographic na Birtaniya (UKHO) suka kai wa Manajan Daraktan NPA.

Tawagar ta samu tarba daga Manajan Daraktan NPA, Abubakar Dantsoho, tare da Daraktan Zartarwa mai kula da Injiniya da Ayyukan Fasaha da sauran manyan jami’an hukumar.

ADVERTISEMENT

A yayin ganawar, bangarorin biyu sun tattauna hanyoyin kara karfafa dadaddiyar hadin gwiwar da ke tsakanin Nijeriya da Birtaniya a harkokin ruwa, musamman a fannoni masu muhimmanci ga tsaron zirga-zirga a ruwa, ingancin ayyukan tashoshin jiragen ruwa da kuma ci gaba mai dorewa a fannin.

Da yake jawabi, Dantsoho ya bayyana shirye-shiryen zamanantar da tashoshin jiragen ruwa da NPA ke aiwatarwa domin mayar da tashoshin Nijeriya cibiyoyin kasuwanci masu gogayya a duniya.

LABARAI MASU NASABA

Yadda Taron Bikin Maulidi Ya Gudana A Unguwar Mile 12 A Legas

NPA Ta Bayyana Cewa Kirkiro Da Sabuwar Hukumar NPERA Ba Zai Zame Mata Tarnaki Ba

Ya bayyana cewa hukumar na zuba jari a manyan ayyuka da suka hada da gyaran tashoshin jiragen ruwa, inganta hanyoyin ruwa da kuma sabunta muhimman kayayyakin more rayuwa domin kara ingancin aiki, rage lokacin da jiragen ruwa ke dauka a tashoshi da kuma karfafa matsayin Nijeriya a kasuwancin ruwa na yanki da na duniya.

Tattaunawar ta kuma mayar da hankali kan bunkasa kwarewar binciken taswirar ruwa domin inganta tsaro a zirga-zirgar ruwa da kuma saukaka ayyukan tashoshin jiragen ruwa a hanyoyin ruwan Nijeriya.

Tawagar Birtaniya ta sake jaddada aniyarta ta tallafa wa ci gaban wannan fanni a Nijeriya ta hanyar hadin gwiwar fasaha da musayar ilimi.

Ganawar ta sake nuna kakkarfan dangantakar diflomasiyya da ke tsakanin Nijeriya da Birtaniya, da kuma jajircewarsu wajen bunkasa kirkire-kirkire, habaka kwarewa da ci gaba mai dorewa a masana’antar harkokin ruwa.

NPA
Rabi'u Ali Indabawa
+ postsBio
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ƙungiya Ta Gudanar Da Zaɓen Sabbin Shugabanninta A Abuja
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Jihar Katsina Da UNICEF Sun Ceto Rayuwar Yara Ta Hanyar Samar Da Abinci Mai Gina Jiki
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Yadda Tinubu Ya Kashe Naira Biliyan 37.64 A Tafiye-tafiye
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ta’addaci: Mutum 14,500 Sun Bace A Arewa Maso Gabas

MASU ALAKA

Yadda Taron Bikin Maulidi Ya Gudana A Unguwar Mile 12 A Legas
Tattalin Arziki

Yadda Taron Bikin Maulidi Ya Gudana A Unguwar Mile 12 A Legas

September 4, 2026
NPA Ta Bayyana Cewa Kirkiro Da Sabuwar Hukumar NPERA Ba Zai Zame Mata Tarnaki Ba
Tattalin Arziki

NPA Ta Bayyana Cewa Kirkiro Da Sabuwar Hukumar NPERA Ba Zai Zame Mata Tarnaki Ba

September 4, 2026
NPA Ta Tabbatar Da Maido Da Manyan Kayan Aikin Hukumar Wuta Ta Neja Delta —Babbar Manaja
Tattalin Arziki

NPA Ta Tabbatar Da Maido Da Manyan Kayan Aikin Hukumar Wuta Ta Neja Delta —Babbar Manaja

August 28, 2026
Next Post
Zan Saki Nnamdi Kanu Idan Na Zama Shugaban Ƙasa – Peter Obi

Zan Saki Nnamdi Kanu Idan Na Zama Shugaban Ƙasa - Peter Obi

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.