ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Bankin Duniya Zai Bai Wa Nijeriya Rancen Dala Biliyan 1.25 Duk Da Ƙorafin Da ‘Yan Ƙasar Suka Yi

by Sadiq
2 months ago

Bankin Duniya ya amince zai bai wa Nijeriya sabon rancen dala biliyan 1.25 a ƙarƙashin shirin NAIJA domin tallafawa wajen zuba jari da samar da ayyukan yi.

An sanar da amincewar ne tare da ƙaddamar da sabon tsarin haɗin gwiwa tsakanin Bankin Duniya da Nijeriya na shekarun 2026 zuwa 2032.

Bankin ya ce kuɗin za su taimaka wajen samar da ayyukan yi, bunƙasa kasuwanci, inganta wutar lantarki, faɗaɗa intanet, inganta harkokin lafiya da kuma haɓaka noma.

ADVERTISEMENT

Daraktan Bankin Duniya a Nujeriya, Mathew Verghis, ya ce manufar shirin ita ce tabbatar da cewa sauye-sauyen tattalin arziƙin da aka fara sun samar da ci gaba a rayuwar ‘yan Nijeriya ta hanyar jawo masu zuba jari da samar da ƙarin ayyukan yi.

Bankin ya ƙara da cewa kuɗin za su kuma tallafa wajen gyare-gyare a fannin wutar lantarki, tattalin arziƙin zamani, noma, kasuwanci da kuma ƙara samar da kuɗaɗen shiga na gwamnati.

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

Sai dai wannan mataki ya haifar da ce-ce-ku-ce kan ƙaruwar basussukan da Nijeriya ke karɓowa.

Wasu ‘yan Nijeriya na ganin gwamnati na ci gaba da karɓar rance daga ƙasashen waje duk da matsin tattalin arziƙin da al’umma ke fuskanta.

Alƙaluman Hukumar Kula da Basussuka ta Ƙasa (DMO), ta fitar ya nuna cewar bashin da Bankin Duniya yake bin Nijeriya ya ƙaru daga dala biliyan 17.81 a ƙarshen shekarar 2024 zuwa dala biliyan 19.89 a ƙarshen shekarar 2025, lamarin da ya sa Bankin Duniya ya kasance mafi girman wanda yake bai wa Nijeriya rance a cikin cibiyoyin kuɗi na duniya.

MASU ALAKA

Sojoji
Manyan Labarai

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Ballon D'or
Manyan Labarai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026
Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue
Manyan Labarai

Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue

September 8, 2026
Next Post
An Kama Tsohon Minista Uche Nnaji Kan Zargin Amfani Da Takardun Bogi

An Kama Tsohon Minista Uche Nnaji Kan Zargin Amfani Da Takardun Bogi

LABARAI MASU NASABA

Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.