Ranar 12 ga watan Yunin kowace shekara muhimmiyar babbar rana ce da ta shiga cikin kundin tarihin mulkin farar hula a Nijeriya musamman a bisa ga dorewar mulkin dimokuradiyya a kasa mafi yawan al’umma a nahiyar Afurka.
Babban abin jinjinawa shine Nijeriya ta cika shekaru 27 ta na tafiya a saman turbar mulkin dimokuradiyya ba tare da katsalandan, tsangwama ko katsewar mulkin daga sojoji ba tun bayan kawo karshen mulkin soji a 1999 wanda shine babbar nasarar da aka samu a mulkin dimokiradiyya a Nijeriya.
Duk da kalubalen tattalin arziki da tsaro, Nijeriya ta ci-gaba da kare tsarin mulkin dimokuradiyya daga barazanar juyin mulki. A 2025, hukumomin tsaro sun ce sun dakile wani yunkurin juyin mulki inda suka kama jami’an soji da fararen hula tare da gurfanar da su gaban kotu. Wannan ya nuna karfin tsarin mulkin farar hula idan aka kwatanta da shekarun baya da juyin mulkin soja ya zama ruwan dare. Duk da rashin nasararsa shine yunkurin juyin mulki na farko da aka bayyana tun bayan dawowa mulkin dimokuradiyya a 1999.
Nijeriya ta samu gagarumar nasara wajen tabbatar da canjin mulki cikin lumana a tsakanin jam’iyyun siyasa daban-daban, lamarin da ke nuna karbuwa, girma da tasirin tsarin mulkin dimokuradiyya a Nijeriya duk da matsalolin da ke akwai.
Daga 1999 zuwa yau ra’ayoyin dimbin al’umma ya bambanta kan nasara ko akasin ta da aka samu a mulkin dimokiradiyya a Nijeriya, a yayin da wasu ke bayyana cewar an samu ci-gaba a mabambantan fannoni wasu kuwa na ganin mulkin farar hula a Nijeriya wata hular baka ce.
Da dama na ganin an samu ci- gaba a bangaren ‘yancin fadin albarkacin baki a bisa ga yadda kafafen yada labarai da ‘yan kasa ke da damar bayyana ra’ayoyinsu ba tare da tsangwama mai tsanani ba kamar a zamanin mulkin soja. Bugu da kari mulkin dimokuradiyya ya zama silar samun ci- gaba a fannoni da dama kamar fadada hanyoyin sadarwa, musamman a bangaren fasahar zamani da shigowar wayoyin hannu wanda ya saukaka harkokin kasuwanci da sadarwa a fadin kasar nan.
Baya ga wannan birane da kauyukan Nijeriya sun samu gagarumin ci-gaba idan aka kwatanta su da shekaru 27 da suka gabata da wasu yankuna da dama suke a matsayin kauyen- kayau. A yau a wasu yankuna, an samu bunkasar ayyukan more rayuwa kamar hanyoyi, makarantu da cibiyoyin kiyon lafiya, kodayake ba a ko’ina ba.
Haka kuma, kafa hukumomi da tsare-tsaren yaki da cin hanci da rashawa da kuma bunkasar tattalin arziki sun nuna kokarin inganta shugabanci, ko da yake har yanzu akwai bukatar karin gyara domin samun cikakken anfana da mulkin dimokuradiyya.
Duk da nasarorin da aka samu a mulkin farar hula, kasar na ci- gaba da fuskantar manyan kalubale da suka hada da gaza shayar da al’umma romon mulkin dimokuradiyya yadda ya kamata, mamayar masu ruwa da tsaki a harkokin siyasa tare da raunin manufofii da akidun jam’iyyun siyasa da kuma dawowa daga rakiyar mulkin dimokuradiyya da yawan jama’a suka yi.
Masana na danganta wannan rashin amincewa da halin kunchi da tsadar rayuwar a kasar da take da tarin albarkatun kasa musamman man fetur da zinare amma gwamnari ba ta da matatar mai guda daya da ke aiki sai dai kawai ta dogara da shigowa da man fetur daga wajen kasa.
Bugu da kari duk da cika da tumbatsar masana’antun da ke akwai a Nijeriyar jiya an wayi gari an neme su an rasa a yau musamman a yankin Arewa wanda hakan ya haifar da rashin aikin yi, zaman banza da kauracewar masu zuba jari daga kasashen waje.
Haka ma babbar gagarrumar matsalar da ta zama tarnaki ga ci-gaba da bunkasar mulkin dimokuradiyya yadda ya kamata shine kara tabarbarewar sha’anin tsaro bakidaya lamarin da tuni ke ci wa ‘yan Nijeriya tuwo a kwarya.
Tun bayan bayyanar ayyukan kungiyar Boko- Haram a farkon shekarun 2000, rikicin ya yi sanadiyyar mutuwar miliyoyin mutane tare da tilasta miliyoyin jama’a kauracewa gidajensu, musamman a yankin Arewa maso- Gabas. Rahotanni daga kungiyoyin kasa da kasa sun nuna yadda dimbin mutane suka zama ‘yan gudun hijira sakamakon hare-haren kungiyar. Duk da kokarin da gwamnati da sojoji suka yi, har yanzu a na fuskantar hare-hare lokaci zuwa lokaci wanda ke nuna cewa matsalar tsaro na ci-gaba da zama babbar barazana ga zaman lafiya da ci- gaban kasa.
Hasalima daga kisan gillar Boko- Haram zuwa barayin daji a 2011, miliyoyin al’umma sun rasa rayukan su, muhallansu da dukiyarsu lamarin da yasa tuni al’ummar kasa da dama suka dawo daga tunanin gwamnatin za ta iya kare su wanda hakan babban ci-baya ne a dimokuradiyyar Nijeriya a shekaru 27 tare da damuwa game da makomar dimokuradiyyar kasar nan.
A tsayin wadannan shakarun jama’a da masu ruwa da tsaki na nuna shakku sahihancin Hukumar Zabe wajen aiwatar da zaben da ke da karbuwa ga al’umma. Da yawa na bayyana kimar hukumar na ci-gaba da raguwa musamman a bisa ga korafe-korafe da suka taru suka dabaibaye zabukan baya-bayan nan da suka jefa shakku a zukatan al’umma kan sahihanci da gaskiyar tsarin zabe a Nijeriya da Hukumar ke jagoranta.
Haka ma siyen kuri’a ya zama ruwan dare a tsarin zabe a Nijeriya, lamarin da ke gurgunta dimokuradiyya da hana samun sahihan shugabanni kamar kuma yadda yawaitar canza sheka daga wannan jam’iyyar zuwa waccan ya zama kalubalen da jam’iyyun siyasa ke fuskanta ta yadda akidu da manufofin jam’iyyun siyasa suka zama maras tasiri. Hasalima ‘yan siyasa da dama na sauya jam’iyya ne saboda romon siyasa, sabani, ko neman kariya daga bincike.
Bangaren shari’a da yaki da cin hanci da rashawa da ke a matsayin muhimmai a kowace gwamnati na fuskantar babban kalubale a dimokuradiyyar Nijeriya domin kuwa a shakaran jiya da jiya zuwa yau a na ci- gaba da fuskantar matsin lamba kan matakin ‘yancin kai da ingancin aikinsu.
Hasalima Hukumomin Yaki da Cin Hanci da Rashawa na EFCC da CPC na fuskantar rashin amincewa daga jama’a wadanda ke kallon su kawai matsayin karnukar farautar masu rike da madafun musamman a batun tabbatar da bin doka da kuma yaki da rashawa ba tare da nuna bambanci ba.
Wani abin jimami shine mulkin dimokuradiyya a tsawon shekaru 27 a Nijeriya ya kasa samar da ingantacciyar wutar lantarki duk da yawan kudaden da aka kashe a wannan fanni. Tun daga 1999, gwamnatoci daban-daban sun zuba biliyoyin daloli wajen gyaran tashoshin samar da wuta, rarrabawa da kuma gyaran layukan lantarki, amma har yanzu kasar na fama da karancin wuta.
Rahotanni sun nuna cewa Nijeriya na samar da kasa da megawatt 5,000 ga al’umma sama da miliyan 200, adadin da bai kai bukatar kasar ba ko kusa, wanda hakan ya nuna cewa duk da shekaru 27 na dimokuradiyya, har yanzu romon mulkin bai kai ga wannan muhimmin bangare na rayuwar jama’a ba.
Daya daga cikin manyan misalan yadda aka kasa cimma nasara duk da kashe makuddan kudade shi ne aikin wutar lantarki ta Mambila wadda tun daga shekarun 1980 aka fara assasa aikin, amma gwamnatocin dimokuradiyya daban-daban sun ci-gaba da ware makudan kudade ba tare da ganin haske ba.
Kama daga zamanin mulkin Obasanjo, ‘Yar’Adua, Jonathan zuwa Buhari, an yi ta sanya hannu kan kwangiloli da sabunta su, inda aka kiyasta kudin aikin zuwa sama da dala biliyan 5.7, tare da wasu rahotanni da ke nuna cewa an riga an kashe biliyoyin naira kan shirye-shirye, nazari da biyan diyya. Duk da haka, aikin bai kai matakin samar da wuta ba, lamarin da ke kara nuna yadda rashin tsari, jajircewa, cin hanci da rashawa jinkiri da matsalolin gudanarwa ke hana manyan ayyukan wutar lantarki kaiwa ga nasara a Nijeriya.
Wani babban tarnaki da ke ci-gaba da dabaibaye al’umma a Nijeriya a tsawon shekaru 27 na mulkin dimokuradiyya shi ne matsalar rashin aikin yi wadda ta riga ta zama ruwan dare musamman a tsakanin matasa. Hasalima duk da alkawulan daukar aiki da mabambantan gwamnatoci ke yi wa matasa tun daga 1999 zuwa yau amma ko wace shekara kan kare ba tare da samar da kwakkwaran aiki ba.
Haka ma matsin tattalin arziki ya kara tsananta a rayuwar al’umma a tsayin shekaru 27 akasin a shakarun baya da rayuwa take da sauki. Hauhawar farashin kayayyaki, tabarbarewar darajar naira da kuma karancin kudaden shiga sun jefa miliyoyin ‘yan kasa cikin mawuyacin hali.
Bugu da kari, talauci ya ci- gaba da yawaita duk da albarkatun da kasar ke da su domin kuwa bayanai sun nuna kimanin sama da mutane miliyan 130 a Nijeriya ne ke rayuwa cikin talauci kamar yadda wasu rahotannin gwamnati da kungiyoyin kasa da kasa suka ruwaito kuma duka ba tare da samun tallafi daga gwamnati ba a daidai lokacin da farashin kayayyaki ya karu da kusan kashi 30 cikin 100.
Satar man fetur da barayin mai ke yi a yankin Neja- Delta gagarumar matsala ce da ta addabi Nijeriya a tsawon shekaru 27 na mulkin dimokuradiyya domin kuwa babban kalubale ne mai zaman kansa da ya dabaibaye tattalin arzikin Nijeriya.
A tsawon shekaru, barayin mai da masu harkallar fasa bututun mai sun rika sace dubban gangunan mai a kullum, lamarin da ya jawo asarar biliyoyin daloli ga kasar. A shekarar 2021 kadai, Hukumar Kula da Harkokin Man Fetur ta Nijeriya ta bayyana cewa kasar ta yi asarar ganga miliyan 37.6 na danyen mai, daidai da kusan ganga 102,900 a kullum a sakamakon sata wanda hakan ya kasance mafi muni a cikin fiye da shekaru 20, wanda kuma ya rage yawan kudaden shiga da gwamnati ke samu daga fitar da mai a kasashen waje. Duk da cewa gwamnati ta samu nasarar rage satar mai zuwa kasa da ganga 10,000 a kullum a shekarun baya-bayan nan, barnar tattalin arziki da muhalli da aka yi wa yankin Neja- Delta na ci- gaba da zama babban kalubale ga ci-gaban Nijeriya.
Tabarbarewar sha’anin ilimi babbar matsala ce mai zaman kan ta da Nijeriya da al’ummar ta ke fuskanta a tsayin wadannan shakarun. Duk da yawan jami’o’i da makarantun da aka kafa, har yanzu ingancin ilimi na fuskantar barazana sakamakon rashin isassun kayan aiki, karancin malamai da kuma yawan yajin aiki musamman a jami’o’in gwamnati.
Rahotanni sun nuna cewa Nijeriya na da sama da yara miliyan 10 da ba sa zuwa makaranta, mafi yawansu a yankin Arewa wanda hakan ya jefa makomar matasa cikin hadari tare da kara yawan rashin aikin yi da talauci a nan gaba.
Shugabannin Mulkin Dimokuradiyya (1999-2026
Gwamnatin Obasanjo (1999–2007)
A mulkin dimokiradiyya gwamnatin Olusegun Obasanjo ce ta zama ta farko da ake tunawa a Nijeriya musamman saboda ita ce ta bude babiin farko na mulkin dimokuradiyya bayan komawar soji barki a 1999.
Kafa hukumomin yaki da cin hanci da rashawa na EFCC da ICPC da shugabanni da ‘yan siyasa da dama suka fuskanci shari’a ya zama abin yabawa. Haka kuma, shigowar kamfanonin sadarwa a lokacin ya haifar da mallakar wayoyin hannu wanda ya saukaka sadarwa a fadn kasar.
Sai dai a mulkin Obasanjo an samu yawaitar hadurran jiragen sama, ciki har da wanda ya yi sanadiyyar rasuwar Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammadu Maccido a 2006. Haka ma duk da nasarar yafewa Nijeriya bashin dala biliyan 18, gwamnatin ta fuskanci suka kan siyasar a- mutu – ko- a- yi- rai da kuma zaben 2007 mai cike da tarin matsaloli.
Umaru ‘Yar’Adua (2007–2010)
Shugaba Umaru Musa ‘Yar’Adua ya jagoranci Nijeriya a cikin salon mulkin gaskiya da rikon amana, hasalima ya kafa tarihin zama shugaban kasa na farko da ya bayyana kadarorinsa a fili tare da amincewa cewa zaben 2007 da ya kawo shi mulki cike yake da sabawa dokokin zabe.
Gwamnatin ‘Yar’Adua ta rage farashin mai zuwa naira 65, tare da yunkurin gyara tsarin zabe. Haka kuma ta samu nasarar samar da zaman lafiya a yankin Neja-Delta ta hanyar afuwa ga ‘yan bindiga. ‘Yar’Adua ya kasance shugaban mulkin farar hula na farko da ya yi bankwana da duniya saman gadon mulki.
Goodluck Jonathan (2010–2015)
A zamanin mulkin Jonathan matsalar tsaro ta kara tsananta sakamakon karuwar hare-haren mayakan Boko Haram wanda ya jefa al’umma cikin fargaba. Sace ‘yan matan Chibok a shekarar 2014 ya ja hankalin duniya bakidaya. Duk da cewar Jonathan ya fuskanci mummunar adawa ga al’ummar kasa ta hanyar dawowa daga rakiyar mulkin sa, ya samu yabo a matsayin shugaban kasa na farko da ya amince da shan kaye a zabe, matakin da ya kara masa daraja da tabbatar da kimar mulkin dimokuradiyya.
Muhammadu Buhari (2015- 2023)
Shugaba Muhammadu Buhari wanda ya hau mulki bayan shan kaye a zabuka da dama a baya shine shugaba na farko da ya sha alwashin yaki da cin hanci da rashawa da dukkan karfisa amma kuma ya kammala shekaru takwas ba tare da cimma burinsa ba.
Haka ma gwamnatin Buhari wadda talakawa suka yi tsammanin samun sauki da canjin rayuwa sun fuskanci tsananin ukuba, kunci da talauci a mulkinsa haka ma gwamnatinsa ta samu shaidar karan tsaye ga kundin tsarin mulkin kasa ta hanyar sabawa mabambantan umurnin kotu.
Bola Ahmad Tinubu (2023-
Gwamnatin Tinubu ta zo da wasu muhimman sauye-sauye da za a iya kallon su a matsayin nasarori kamar yadda ta bayyana musamman a bangaren tattalin arziki. Daya daga cikin manyan matakan shi ne cire tallafin man fetur, wanda ya rage nauyin kashe kudaden gwamnati da kuma bude damar sake tsara kasafin kudin kasa.
Sai dai cire tallafin man fetur da sauye- sauyen harkokin kudin waje sun haddasa tsadar rayuwa mafi tsanani da al’ummar Nijeriya suka fuskanta domin kuwa shine mataki daya tilo da ya girgiza al’ummar kasa ya jefa su a cikin halin kunchi da tsadar rayuwa sanadiiyar tashin gwauron zabin da kayayyaki suka yi.
Kisan kare dangi a gawurtacciyar matsalar tsaro da ke addabar al’umma ita ce kan gaba da al’ummar kasa ke kuka da kokawa a mulkin Tinubu da miliyoyin al’umma suka rasa rayukan su da dukiyoyin su. A makon nan Majalisar Wakilai ta nuna gazawar shugabannin hukumomin tsaro wajen yaki da ta’addanci tare da kira ga gwamnati da ta dauki kwararan matakai domin magance bahaguwar matsalar.
Gwamnatin Tinubu ita ce ta farko a Nijeriya da ta kasa aiwatar da ayyukan kasafin kudin shakara har a cikin wata shekarar. Jagororin adawa a Nijeriya sun yi korafin gwamnati ba ta aiwatar da ayyukan kasafin kudin 2024 da 2025 har a cikin 2026 ba, lamarin da gwamnatin ta gaza musantawa. Haka ma Gwamnatin Tinubu ce ta farko a kasar nan da ta sanya kusan dukkanin gwamnoni a inuwar jam’iyya daya tare da kare lagon jam’iyyun adawa wanda babbar barazana ce kuma kalubale mai zaman kansa ga mulkin dimokuradiyya a Nijeriya.















Discussion about this post