ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Tuesday, July 14, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Buƙatar Komawa Ga Allah Ta Hanyar Yawaita Istigfari

by Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
2 months ago

A’uzu billahi minash-shaitanir-rajim. Bismillahir-Rahmanir-Rahim. Allahumma salli ala sayyidina Muhammadinil-fatihi lima ughliƙa wal-khatimi lima sabaƙa nasiril-haƙƙi bil-haƙƙi, wal-hadi ila siratikal-mustaƙim wa ala alihi haƙƙa ƙadrihi wa miƙdarihil-azim. Wa radiyallahu an ashabi rasulillahi sallallahu alaihi wa sallam, la hawla wala ƙuwwata illa billahil-aliyyil-azim.

Ya himmatash-sheikh izhirilana bihadal-mahaddari waltati bina wastintatinal-nasi bi-zafari. ƴan uwa, assalamu alaikum warahmatullahi taala wabarakatuhu. Mungode Allah, da Allah ya hadamu a wannan rana mai albarka mai girma, a cikin addinin mu, kuma mai girma, a cikin ɗariƙarmu, ranar da muke haɗuwa baki ɗaya muke ambatan Allah tabaraka wa taala, a cikin yadda falalolin sa za su zo.

Alhamdullilahi, wannan zikiri kullum muna yi, amma kuma muna haɗuwa duk karshen shekara mu gode wa Allah, mun cika ayyukan mu na shekara, mun kuma yin wani alkawari da Allah zamu kuma sabunta himma, mu kuma cigaba da wannan shekara. Dama darikan mu da dukkan ma ayyukan mu, mun karba ne iya rayuwa, mun karba ne har rasuwa. Toh kullum muna jaddadawa, muna jaddadawa.

ADVERTISEMENT

A kowane irin hali, irin wannan zama, daɗa sabunta kai ne. Godiya ga Allah ne, Allah ya karɓa mana ibadodin da muka yi a shekara da ta shige, ya yafe mana zunuban da muka yi a shekara da ta shige, kuma mun kara kulla azama ta wannan shekara da zata zo, muna fata Allah ya taimake mu, mu ninka, mu ninka, mu ninka ibada a kai, Alfarman Annabi sallallahu alaihi wasallam ya jiƙan matattunmu, kuma ya yi albarka ga rayayyunmu, ya ja da rayuwarmu da iyayenmu da kakaninmu ga su da suke zaune gabanmu tare da mu. Allah ya ja mana da rayuwar su a cikin al-khairi da buɗi da lafiya, Alfarman Annabi sallallahu alaihi wasallam, ya biya bukatun mu ga baki daya da bukatun mutanen gari.

Hadisi yazo cewa, “duk wanda zikiri na, da littafi na ya shagalantar da shi, har ma bai ce ina son kaza ba, sai na bashi abin da yake so kafin in bai wa mai addu’a abin da ya roƙa”. Toh, mungode Allah, zaman mu anan, Allah mu ka ambata, ya shagalantar da mu, wannan biyan bukata ne yanke ga dukkanin, da duk garin, da masu masaukin baƙi, duk gabaki ɗaya alfarmar Annabi SAW.

LABARAI MASU NASABA

Falalar Yawaita Salati Ga Annabi Muhammad SAW

Falalar Yawaita Tuba Ga Ubangiji (Istigfari)

ƴan uwa, a gurguje, mungode Allah. Mungode Allah da ya sa mu a cikin ɗariƙar nan ta Shehu Tijjani RA. Idan mutum zai magana a cikin ɗariƙar nan, sai ya rasa ma ta ina zai kama. Saboda hanyoyin magana da yawa a cikin ta, saboda falalarta. Don haka, duk abin da za a faɗa acikinta, yana nuna abu Uku ne:

Takalli, yana nun wanka daga zunubi; tahalli, yana nuna ado bayan an yi wanka daga zunubi, sai tajalli, da ke nuna haɗuwa da sarki ubangiji.

Kullum aikin mu kenan. Takalli, mu yi wanka daga zunubanmu duk gabaki daya, mu yi ta istigfari. Sannan in mun yi wanku kuma, sai mu yi tahalli, ado da salatin Annabi SAW, wanda shi ne babban ado, shi yasan irin kayan da ya dace da hadarar Allah, shi yasan irin adon da ya dace, don zamu shiga fadar Allah ne. Toh bayan Manzon Allah ya yi mana ado da salatin sa, toh shikenan kuma sai tajalli, ganawa da sarki, sai ka ji muna faɗin, “la ilaha illallah, la ilaha illallah”, shike nan komai ya samu.

Toh wannan shine ɗariƙarmu, shine ayyukan da yake cikin ɗariƙarmu. Kowanne lokaci, zaka ji mu cikin istigfari, zaka ji mu cikin salatin Manzon Allah SAW, zaka ji mu cikin “la ilaha illallah”. Toh wannan muradi duk ya biya a cikin waɗannan, don su suke kare, farillolinmu. Akwai zunubin da in mutum ya yi, za’a ce, sai ya yi kwana arba’in Allah zai karbi farillarsa ko nafilarsa. To yau, ire-iren wannan zunubai, su suka fi yawa, amma mun gode Allah, istigfari, da wannan salati, da wannan zikiri da muke, su kuma neman irin waɗannan zunuban suke yi su cinye su.

Wannan na nuna cewa, waɗannan ayyuka da muke yi, za su cinye mana duk wani zunubi da zai taɓa mana farillanmu. Ko bamu je da ladansu na komai ba, bare da lada, ya zama dai sun share mana hanya, farillolinmu sun kai lafiya kalau, wannan ya isa falala. Ko bamu je da ladan komai ba, bare lada ne kan lada, kan lada, har Allah ma ya bamu tun muna ganawa da shi, wato da zuci, da idon zuci, idon basira, har Allah mai iko ne kuma ya bamu ganawa da shi, da idon basaru ma na ganin mu, “wa ma zalika alallahi bi’aziz”, ya bamu wannan duniya da lahira.

To ƴan uwa kamar yadda muka faɗa, wannan sune auradan ɗariƙarmu. Su mutum zai zo ya karɓa, sune ɗariƙar Tijjaniya: Istigfari, salatin Annabi SAW, da la’ilaha illallah. Safiya da yamma, sai wazifa da muke yi, sai zikirin juma’a. Waɗannan sune rukuni hudu, kuma sune ɗariƙar Tijjaniya.

Su ne mutum zai zo ya karɓa, da ganin damarsa, da son sa na alkhairi, da son soyayyar bayin Allah, ya zo ya karɓa. A sanya masa sharaɗi, bayin Allah suna da sharaɗi. Sharaɗi, har Ƙur’ani ya faɗi sharaɗi, hadisai duk sun zo da sharaɗi. Kafin ka zo a gaya maka sharaɗi, ba a ce sai ka zo ba, ba dole ba ne. Amma yanzu, in ka zo kana so, to sai an sanya maka sharaɗi. Idan ka bi sharaɗi sai abin da kazo nema (mashruɗi) ya samu. Amma in ka bar sharaɗi, mashruɗi ba zai samu ba.

Wannan hatta, Annabin Allah, ulul azmi, Annabi Musa AS, da ya zo zai bi bawan Allah, Sayyidina Khadiru, “hal attabi’uka ala an tu’allimani mimma ullimta rushda”, sai da ya bashi sharaɗi. Zaka bi ni, zaka bi ɗariƙa ta ko? eh zan bi ɗariƙarka, to sai na baka sharaɗi. “Fa’in ittaba’tani fala tas’alni an shai’in hatta uhdisa laka minhu zikra”. To in ka bi ni, sharaɗi na (Khadiru), kar a tambaye shi komai. “Fala tas’alni an shai’in”, kar ka ce mun damme ko ta ƙaƙa ko yaya, . “Hatta uhdisa laka minhu zikra”, har sai in ni na ga dama nace ma abu kaza da muka yi fa kaza kaza ne.

Yanzu kamar Annabin Allah, a ce da shi haka? to amma kuma in dai zai bi, to dole ya bi wannan sharaɗi. Kuma da sharadi bai cika ba, sai ga ayar Ƙur’ani na cewa, “haza firaku baini wa bainak”, ka ma gaban ka. Allahu akbar. Shehu Ibrahim Kaulakh na cewa, manya ma an ce musu, haza firaku baini wa bainak, ka ma gaban ka, to kuma waye wani? To, sharaɗin da shehu Tijjani yake bai wa kowa ne mukaddami, shi ne, “in an shiga ba fita”.

Wannan sharaɗi, wanda bai sani ba, sai ya ji kamar da wuya, amma abu ne mai sauki. Allah ya tsare, mutum ya shiga cikin wannan alkhairi mai yawa ya fita. Kullum in mun gama, auradan ɗariƙarmu, addua muke yi, “Allahumma sabbitna bi hazihit-tariƙati-t-tijjaniyah”. Allah ka tabbatar damu a kai, kullum ma addua muke. Sannan, ba za a haɗa ta da wata ɗariƙa ba, duk ɗariƙu na Allah ne, kuma duk suna kai wa zuwa ga Allah. Amma ba zaka haɗa su da ɗariƙar Tijjaniya ba. Mace in ta auri maza biyu, in ta yi ciki, na waye? In ka samu budi fatahi na Allah, a wajan wa ka samu kenan?

Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
+ postsBio
  • Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-ismaila-umar-mai-diwani/
    Falalar Yawaita Salati Ga Annabi Muhammad SAW
  • Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-ismaila-umar-mai-diwani/
    Falalar Yawaita Salati Ga Annabi Muhammad SAW
  • Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-ismaila-umar-mai-diwani/
    Falalar Haɗa Basmala da Suratul Fatiha
  • Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-ismaila-umar-mai-diwani/
    Falalar Neman Tsari Daga Sharrin Shaidan

MASU ALAKA

Matsalar Tsaro: Gwamnatin Tarayya Ta Nemi Taimakon Ƙasashen Waje
Dausayin Musulunci

Falalar Yawaita Salati Ga Annabi Muhammad SAW

July 3, 2026
Darussan Da Suka Fi Dacewa A Fahimta Daga Alkur’ani A Wannan Zamanin (2)
Dausayin Musulunci

Falalar Yawaita Tuba Ga Ubangiji (Istigfari)

June 26, 2026
Manzon Allah
Dausayin Musulunci

Falalar Haɗa Basmala da Suratul Fatiha

June 19, 2026
Next Post
GORON JUMA’A 01-07-2025

GORON JUMA'A 22-05-2026

LABARAI MASU NASABA

Nijeriya Za Ta Zama Ƙasa Mai Zaman Lafiya, Ba Za A Ƙara Samun Kashe-kashen Jama’a Ba – Oluremi Tinubu

Nijeriya Za Ta Zama Ƙasa Mai Zaman Lafiya, Ba Za A Ƙara Samun Kashe-kashen Jama’a Ba – Oluremi Tinubu

July 14, 2026
Sin Ta Tsara Bunkasa Darajar Cinikayyar Kayayyaki Zuwa Yuan Tiriliyan 60 Yayin Shirin Raya Kasa Na Shekarar 2026 Zuwa 2030

Sin Ta Tsara Bunkasa Darajar Cinikayyar Kayayyaki Zuwa Yuan Tiriliyan 60 Yayin Shirin Raya Kasa Na Shekarar 2026 Zuwa 2030

July 14, 2026
Katsina: Kotu Ta Yanke Wa Hauwa’u Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya Kan Taimaka Wa ’Yan Bindiga

Kotu Ta Tsare Shugaban Makaranta Da Malami Kan Zargin Lalata Da Ɗaliba Mai Shekara 6 A Gombe

July 14, 2026
An Bankado Muguwar Aniyar Japan Ta Haifar Da Tashin Hankali A Tekun Kudancin Sin

An Bankado Muguwar Aniyar Japan Ta Haifar Da Tashin Hankali A Tekun Kudancin Sin

July 14, 2026
Layin Dogo Tsakanin Tanzaniya Da Zambiya Ya Zama Shaidar Abota Tsakanin Sin Da Afirka

Layin Dogo Tsakanin Tanzaniya Da Zambiya Ya Zama Shaidar Abota Tsakanin Sin Da Afirka

July 14, 2026
Nijeriya da Masar Sun Ƙulla Haɗin Gwiwa Domin Yaƙi da Miyagun Ƙwayoyi

Nijeriya da Masar Sun Ƙulla Haɗin Gwiwa Domin Yaƙi da Miyagun Ƙwayoyi

July 14, 2026
CMG Ya Gudanar Da Babban Taron Masu Kirkirar Manyan Shirye-Shirye Da Fina-Finai

CMG Ya Gudanar Da Babban Taron Masu Kirkirar Manyan Shirye-Shirye Da Fina-Finai

July 14, 2026
Tsohon Sanatan Gombe, Bayero Nafada, Ya Fice Daga PDP Bayan Ganawa da Shugabannin APC

Tsohon Sanatan Gombe, Bayero Nafada, Ya Fice Daga PDP Bayan Ganawa da Shugabannin APC

July 14, 2026
ADC Ta Nemi A Binciki Nafiu Bala Bayan INEC Ta Ƙaryata Iƙirarinsa

ADC Ta Nemi A Binciki Nafiu Bala Bayan INEC Ta Ƙaryata Iƙirarinsa

July 14, 2026
Sojoji Sun Kashe ’Yan Ta’adda 3, Sun Ƙwato Makamai A Sakkwato

Sojoji Sun Daƙile Harin ISWAP A Borno

July 14, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.