Shafin TASKIRA shafi ne da ya saba zakulo muku batutuwa daban-daban wadanda suka shafi al’umma.
Tsokacinmu na yau zai yi duba ne game da yadda wasu mazan ke nuna halin ko in kula wajen bayar da tarbiyyar yaransu, yayin da yaro ya lalace sai uba ya mayar da laifi ga uwa. Idan kuma aka yi sa’a tarbiyya ta yi kyau sai uba ya rika kallon tarbiyyar sa ce, ko kuma mutanen gari su rika kallon an samu tsayayyen uba. Wanda idan aka yi buncike sai a ga cewa, shi uban ba shi da lokacin kansa bare ma na yaron, uwa ce ta yi fadi-tashi wajen bawa yaron tarbiyya ba tare da sa hannun uba ba.
Dalilin hakan ya sa wannan shafi jin ta bakin wasu daga cikin mabiya shafin game da wannan batu; “Tsakanin iyaye maza da mata wa ne ne ya kamata ya bayar da tarbiyya ga yaransa?, Ta wacce hanya ya kamata iyaye su bi, dan ganin sun inganta tarbiyyar ‘ya’yansu, musamman mazan da ba su da lokacin ‘ya’yansu. Ta wacce hanya za su taimakawa uwa domin bayar da tarbiyyar yaransu?”. Ga dai bayanan nasu kamar haka:
Sunana Hassana Yahaya Iyayi (Maman Noor), daga Jihar Kano:
Ai tarbiyya ta uwa da uba ce, ba za a dora alhakin tarbiyya akan uwa ita kadai ba, idan ya zama gyararre uba yafi kowa son ace dan sa ne. In an samu uban da ba shi da lokacin bada tarbiyya yana can yana galgal a gari. Ke uwa dole ki zage-dantse wajen bawa dan tarbiyya. Ta hanyar sanya su a makaranta addini da ta boko koma kina lura da su wa da wa suke mu’amala kana ki raka su da addu’a Allah ya raya mata su, ya sa su zama sanyin idananiyarta. Kuma tayi hakuri za ta ga ribar abun. Shi kuma uban gashi ga duniyar nan.
Sunana Sunusi Ibrahim SML:
Tarbiyya ta bangare biyu ne ma’ana uwa da uba. Kula da makarantunsu wajen kai ziyara duk bayan wasu lokaci da sa ido akan dukkan abokan da za a ce an ga yaronka da su, da sauke hakkinka a gida matsayinka na uba. Su tuna akwai Allah zai tambaye su akan kiwon da ya basu. Su tuna uwa mace mai rauni ce babu yadda za a yi ta fito waje neman yaro ko zuwa makaranta wajen bunciken ya yanayin zuwansu da kin zuwansu, hakkin uba ne.
Sunana Aminu Adamu Malam Madori A Jihar Jigawa:
To maganar tarbiyyar yara hakki ne na uwa da uba ba wai mutum daya ba, don haka kowa da bangaren sa a wajen gudanar da tarbiyyar, domin akwai fannoni da dama a matakan tarbiyya. To da farko ya kamata su hada kan su wajen tarbiyyantar da ‘ya’yansu, domin hakan zai taimaka wajen kowa ya sauke nauyin da ya rataya a wuyan sa, kuma za a rika samun taimako wajen wani ya kula da bangaren wani. To shawarata a nan ita ce ya kamata iyaye su tashi tsaye wajen tarbiyyantar da ‘ya’yansu domin amana ce wadda Allah zai tambaye su akanta. Don haka ya kamata su yi iya iyawar su, sannan su dage da addu’a Allah ya shirya ‘ya’yansu.
Sunana Zulaihat Mahmuda, Karkasara Jihar Kano:
Hmm.. Ni kaina abun yana damuna sai ka ga namiji ya sakarwa mace tarbiyyar yara kamar babu shi aka haife su, wata ma yaron baya jin maganarta in ta sanar da uban madadin ya tsawatar sai ya ce, ke za ki fada musu har su ji. Su yara suna jin tsoron uba saboda ba tare suke wuni da shi ba, ko yaya uwa ta sanarwa uba halin da yaronta yake ciki yana da kyau ya dauki mataki ba wai ya zame hannayensa akan basu tarbiyya ba. Sai wani abu ya samu yaro sannan uba ya dorawa uwa wannan ba adalci bane san kai ne karara. Ya kamata uba ya rika taimakawa uwa wajen tsawatarwa yara idan sun yi ba daidai ba, domin ba a bayar da tarbiyya da hannu daya dole sai an hada da hannun uba, haka idan uwa ta tsawatar wa yara ta yadda bai kamata ba, kada uba ya ce zai yi mata fada a gaban ‘ya’yanta ko kuma ta kai masa karar wani yaron shi kuma ya gwaleta a gaban yaron, wannan yana haifar da rashin tarbiyya ga yara kuma tare da goyon bayan uban.
Sunana Sadik Abubakar Abdullahi, Rijiyar Lemo, karamar hukumar Dala Jihar Kano:
Tarbiyyar yara ba nauyin uwa kadai ba ne, kamar yadda ba na uba kadai ba ne; nauyi ne da Allah da al’umma suka dora wa iyaye gabadaya. Uwa tana da rawar takawa sosai saboda ita ce mafi kusa da yara tun suna kanana, amma uba ma yana da muhimmiyar rawar takawa wajen jagoranci, kulawa, da zama abin koyi ga ‘ya’yansa. Don haka bai dace uba ya jingina duk wata matsalar tarbiyya ga uwa ba, alhali shi ma yana da aikin wajen gina dabi’a da halayen ‘ya’yansa. Kyakkyawar tarbiyya tana samuwa ne idan uwa da uba sun hada kai wajen nuna kulawa, sa ido, da ba yara kyawawan misalai a rayuwa. Domin inganta tarbiyyar yara, dole ne iyaye su kasance masu hadin kai, su rika tattaunawa kan yadda za su kula da ‘ya’yansu, kuma uba ya samar da lokaci koda kadan ne, domin sanin halin da yaransa suke ciki da nuna kulawa gare su.
Sunana Lawan Isma’il (Lisary), Rano a jihar Kano:
A addininmu na Islama uba aka sani amma mu a hausa fulani a yanzu an fi kallon abin daga uwa. Hanyoyin suna da yawa amma ga wata hanyar, shi kansa uban yana kokarin ware wasu lokuta na zama da yaran ko kuma yana ware wani lokacin ko wata ranar da zai rika zama a gidan, domin ya jawo su a jikinsa ya rika jin yadda suke rayuwarsu da iyayensu mata. Shawarata a nan ita ce gaskiya su rika bibiyar yaran har a makarantun da suka san yaran suna zuwa, da kuma kula da irin yaran da suke mu’amala da su, sannan idan sun fito sun san inda za su je. Allah ka sa mu dace, Amin.
Sunana Haj. Amina Ibrahim, Jihar Bauchi:
A takaice dai, uwa da uba su suke da hakki akan tarbiyyar yaransu, domin bahaushe shi kansa na cewa hannu da yawa maganin kazamar miya. To, hanyoyin na da yawa amma hanya ta farko ita ce, su zamo tsintsiya daya madaurinki daya tsakanin uwa da uban wajen bawa yaran tarbiyya, kowanne yayi kokari ya ga yana saka ido tare da tsawatarwa a kan ‘ya’yan. Shawara ga uba ya rika bibiyar halayyar ‘ya’yansa wajen uwa ko da ace ba ya gida, domin samun tsawatar wa yadda ya kamata ko da kuwa ta kiran waya ne a hada yaran da shi ya tsawatar.
Sunana Abba Abubakar Yakubu, mazaunin garin Jos, a Jihar Filato:
Kamar yadda ake haihuwar ‘ya’ya daga gudunmawar uwa da uba, haka ma rainonsu da tarbiyyarsu suka ta’allaka akan dukkansu biyu. Kodayake daga lokacin da uwa ta dauki ciki, nauyin rainon cikin da kula da abin da yake girma a jikinta yake kanta, haka haihuwarta, shayarwa, da goyo da bai wa jaririn kyakkyawar kulawa. A nan, ba ina nufin uba ba shi da wata rawar takawa a dukka wadannan matakan ba ne, sai dai nauyin kulawar na kan uwa ne a farko, sai kuma uba, wanda yake da hakkin taimaka mata da tausaya mata da kuma ba ta dukkan kulawar da take bukata. Don haka ne ma Ubangiji Allah ya fifita uwa akan uba har ma kuma aka wajabtawa ‘ya’ya yi wa uwa biyayya a kowanne yanayi. Kula da tarbiyyar ‘ya’ya ba ta uwa ba ce kawai, amma dabi’arta ce haihuwa, raino, da tarbiyya. Shi ya sa ake ganin kamar nauyin kula da yara akan uwa yake, amma a hakika uba yana da muhimmanci a rayuwar ‘ya’yansa da ba su kyakkyawar tarbiyya, ko da kuwa ba ya samun lokaci sosai.
Sunana Yakubu Gwammaja:
Tarbiyya ta uwa da uba ne domin kiwo aka bamu, ya kamata duk uwa tagari da uba nagari ya san da wa ‘ya’yayensa suke hulda wane hali suke ciki. Kula da duk wani motsi na yaransu wayoyin hannunsu, suwaye abokansu da kawayensu, domin kiwo Allah ya basu. Kai uba kaine jigo domin kafi iko a shari’a an ce dole wajibi ka bada tarbiyya kamar yadda kasan za ka ci abinci domin Allah zai tambayeka.
Sunana Hafsat Sa’eed, Jihar Neja:
A nawa tunanin uwa ita ce tarbiyyar ‘ya’ya yake hannunta, sakamakon uwa ita ce take zama tare da yara ko da wane lokaci, mahaifi shi kuma ya tafi nema. Taimakon da mahaifi zai yi da kuma gudunmawar da zai iya bayar wa shi ne, bangaren ciyarwa, da iliminsu da kudin makarantar su to, wannan shi zai kara taimakawa wajen bawa ‘ya’ya tarbiyya. Kuma idan ya dawo gida zai iya kiransu ya ji me aka koya musu a makaranta ku zo mu yi karatu, ya zaman yana da lokacin da idan ya dawo zai rika janyo su a jiki ya ji ya rayuwarsu take.















Discussion about this post