ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

’Yansanda Sun Kama Masu Garkuwa Da Mutane 6, Tare Da Kwato Makamai A Kwara

by Muhammad
4 months ago

Jami’an rundunar ‘yansanda a Jihar Kwara sun kama mutane shida da ake zargi da aikata garkuwa da mutane a ƙaramar hukumar Baruten ta jihar.

Haka kuma, ‘yan sandan sun kwato makamai da wayoyin hannu guda shida daga hannun waɗanda ake zargin, bayan wani samame da aka gudanar bisa sahihan bayanan sirri a yankin.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, Adetoun Ejire-Adeyemi, ta tabbatar da kama waɗanda ake zargin a wata sanarwa da ta fitar ranar Asabar.

ADVERTISEMENT

Ta ce an kama masu laifin a ranar Alhamis, 30 ga Afrilu, 2026. Ta ƙara da cewa: “A ranar 23 ga Afrilu, 2026 da misalin ƙarfe 12:30 na dare, an kawo rahoton satar wani mutum mai suna Isaq J. daga ƙauyen Boriya ta hanyar Okuta. ‘Yan bindigar sun nemi kuɗin fansa na Naira miliyan hamsin (₦50,000,000). Bayan samun rahoton, rundunar ta fara farautar masu laifin, inda aka ƙara matsa musu lamba, wanda ya kai ga sakin wanda aka sace.”

“Daga baya, a ranar 30 ga Afrilu, 2026 da misalin ƙarfe 8:15 na dare, an kama wani Mohammed Shede daga ƙauyen Boriya dangane da lamarin. A yayin bincike, ya amsa laifin bayar da bayanan sirri ga wasu ‘yan ƙungiyar da ake kira ‘Smalley’ da ‘Borugujo’, wanda ya taimaka wajen bibiyar wanda aka sace har aka kama shi a gonarsa.”

LABARAI MASU NASABA

NDLEA Ta Cafke Ƴar Shekara 67 Da Hodar Iblis Da Aka Ɓoye A Cikin Ayaba

Gwamnatin Kaduna Ta Yaba Wa ONSA Kan Shirin Horon Masu Tsaron Daji ‘Forest Guards’

Ta ce ƙarin bincike ya kai ga kama wasu da ake zargi, ciki har da Abubakar Aliu (wanda ake zargi da kula da makaman ƙungiyar), Abu Sonkpia, Saliu Yakubu, da Sanni Sakariyau, duk daga ƙauyen Boriya.

Ta ƙara da cewa waɗanda ake zargin sun amsa laifinsu na hannu a satar mutumin da kuma wani hari na fashi da makami da aka kai wa wani Muhammed Manu a wannan ƙauye.

Kayayyakin da aka kwato daga hannunsu sun haɗa da bindigogi biyu na gida da kuma wayoyin hannu guda shida.

Ta kuma ce ana ci gaba da farautar sauran ‘yan ƙungiyar da suka tsere, da wasu abokan aikinsu biyu da har yanzu suke ɓoye.

Muhammad
+ postsBio
  • Muhammad
    Yadda Na Tsira Daga Cutar Mashaƙo A Katsina: “Na Fara Da Tsartuwar Jini Tare Da Yawu”
  • Muhammad
    An Naɗa Yusuf Nasidi Nasir A Matsayin Talban Barayan Kano
  • Muhammad
    Wani Kamfani Ya Tallafa Wa Masu Sana’ar Shayi A Kano
  • Muhammad
    Kosan Waka Ya Rasu, Gwamnan Kano Ya Jajanta Wa Iyalansa

MASU ALAKA

Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya
Tsaro

NDLEA Ta Cafke Ƴar Shekara 67 Da Hodar Iblis Da Aka Ɓoye A Cikin Ayaba

July 11, 2026
Gwamnatin Kaduna Ta Yaba Wa ONSA Kan Shirin Horon Masu Tsaron Daji ‘Forest Guards’
Tsaro

Gwamnatin Kaduna Ta Yaba Wa ONSA Kan Shirin Horon Masu Tsaron Daji ‘Forest Guards’

July 9, 2026
Sojoji Sun Kama Mai Kai Wa Ƴan Ta’adda Kayan Aiki A Zamfara
Tsaro

Sojoji Sun Kama Mai Kai Wa Ƴan Ta’adda Kayan Aiki A Zamfara

June 25, 2026
Next Post
Sin Ta Zayyana Abubuwan Da Kwamitin Sulhun MDD Zai Ba Su Fifiko Yayin Da Ta Fara Shugabancin Kwamitin

Sin Ta Zayyana Abubuwan Da Kwamitin Sulhun MDD Zai Ba Su Fifiko Yayin Da Ta Fara Shugabancin Kwamitin

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.