ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, June 24, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Bunkasa Arewa Maso Yamma: Rashin Halartar Gwamnoni Ya Dusashe Armashin Taron

by Shehu Yahaya
5 months ago
Arewa

A kokarin ganin an samar da mafita dangane matsalolin da suka yiwa yankin Arewa katutu kama daga matsalar rashin tsaro da tabarbarewa harkar ilimi da dai sauran, hukumomi da sauran masu ruwa da tsaki a shiyyar Arewa maso yammacin Nijeriya sun bayyana kudirinsu  na ganin an shawo kan manyan matsalolin da suka dade suna addabar yankin, musamman ta hanyar ingantattun tsare-tsaren raya kasa da hadin gwiwa tsakanin shugabanni.

Akan haka ne Majalisar dokokin tarayya ta shirya wani muhimmin taro a jihar Kaduna domin tattauna hanyoyin da za a tunkari ayyukan raya kasa na hukumar raya Arewa maso Yamma, wato North West Debelopment Commission (NWDC).

  • GDPn Nijeriya Ya Yi Ƙasa Fiye da Na Shekaru 20 da Suka Wuce A Zamanin Obasanjo — Hashim
  • An Yi Bikin Nuna Al’adun Gargajiya Na Bikin Bazara Na Kasar Sin A Kasar Angola

Kwamitin Majalisar Dattawa mai kula da hukumar, tare da na Majalisar Wakilai, ne suka shirya taron, inda aka gayyato masana daga fannoni daban-daban domin gabatar da kasidu da ra’ayoyi kan manyan matsalolin da ke addabar shiyyar Arewa maso Yamma da kuma hanyoyin da suka dace wajen magance su.

ADVERTISEMENT

Masana da suka gabatar da jawabai a wajen taron sun bayyana cewa yankin na fama da kalubale masu tarin yawa da suka hada da matsalar tsaro, talauci, rashin ayyukan yi, raunin ilimi, da kuma gazawar manyan ayyukan more rayuwa.

Masanan Sun kuma bayar da shawarwari kan matakan da ya kamata gwamnati da hukumar NWDC su dauka domin farfado da tattalin arziki da zaman lafiyar yankin.

LABARAI MASU NASABA

Tsohon Shugaban APC Na Kebbi Ya Rasu A Hannun ’Yan Bindiga

Hajjin 2026: NAHCON Ta Kammala Jigilar Alhazan Nijeriya Daga Saudiyya

Jihohi bakwai ne ke karkashin hukumar, wadanda suka hada da Kano, Kaduna, Katsina, Kebbi, Sokoto, Jigawa da Zamfara.

Babban abin da yafi daukar hankali yayi taron shine rashin halartar daya daga cikin gwamnonin jihohin yankin inda dukkansu suka turo wakilai da kasancewar muhimmacin taron.

Wakilinmu ya hango manyan Jami’an tsaron fadar shugaban kasa gabannin taron musamman ganin cewa ranar da za’a gudanar da taron mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima yana jihar Kaduna da wasu gwamnoni Amma kamin a fara gudanar da taron sai labari ya sauya inda wasu majiyoyi suka tabbatar wa wakilinmu cewa mataimakin shugaban kasa da wasu gwamnoni irinsu Gwamnan jihar Kano fa Kaduna basu shiryya halartar taron ba bisa dalilan cewa suna da wasu tarukan da zasu hakartar a kaduna.

Rashin halartar gwamnonin ya jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin wasu daga cikin mahalarta taron, inda was suka bayyana cewa rashin  halartar gwamnonin ya rage wa taron armashi tare da haifar da shakku kan muhimmancin hadin gwiwar shugabanni, kasancewar su ne ke da nauyin aiwatar da yawancin shawarwarin da aka tattauna.

Da yake jawabi a wajen taron, Sakataren kungiyar Dattawan Arewa ta Northern Elders Forum, Dakta Hakeem Baba-Ahmed, ya bayyana rashin jin dadinsa kan rashin halartar gwamnonin yankin. Ya ce wannan mataki na nuna cewa har yanzu akwai sauran aiki mai yawa da ya kamata shugabannin Arewa su yi domin ceto yankin daga halin da yake ciki.

Yace “Arewa na cikin mawuyacin hali, kuma dole ne shugabanni su fito gaba daya su dauki nauyin jagoranci da gaskiya da jajircewa,” in ji Baba-Ahmed.

Da yake gabatar da kasida a wurin taron Farfesa Isa Ali Fantami, ya jaddada cewa duk wani shirin raya Arewa maso Yamma ba zai yi nasara ba matukar ba a fifita gina Dan’adam ba.

Ya ce, “Dole ne shugabannin yankin su fifita Dan’adam, wato a gina al’ummar yankin ta hanyar ba su ingantaccen ilimi, tarbiyya da kuma sana’o’i domin su dogara da kansu.”

Farfesan ya kara da cewa zuba jari a fannin ilimi da kwarewa shi ne ginshikin magance matsalolin tsaro da talauci da ke addabar yankin.

A zantawarsa da manema labarai Jim kadan bayan kammala taron Sanata Babangida Hussaini, shugaban kwamitin majalisar dattawan mai kula da hukumar ta raya yankin na arewa maso yamma, ya bayyana cewa, sai an kare rayuwa da dukiyar al’umma ne za a fara tunanin mai za a kawo musu na ci gaba kuma.

Sanatan ya kara da cewa tsaro ne kan gaba a kan abin da hukumar za ta fara ba wa fifiko, domin akwai jihohin yankin da ke fama da matsalar tsaron da ta ki ci taki cinyewa, wanda kuma ke kawo matsala wajen ci gaban al’ummar yankin. Akan  haka dole sai an samar da hanyoyin da za a tabbatar da tsaron al’ummar shiyyar arewa maso yamma kafin a kawo musu ayyuka ci gaba.

A nasa tsokacin mai rajin kare ‘yancin matasan Arewacin Nijeriya,  Ambasada Usman Yerima Shettima, ya bayyana taron matsayin wata muhimmiyar hanya da za ta taimaka wajen ciyar da yankin gaba da kuma magance dimbin kalubalen da ke addabar yankin

Yerima ya ce, duba da irin matsalolin tsaro, tattalin arziki da zamantakewa da yankin Arewa maso Yamma ke fuskanta, babu shakka irin wannan taro zai taimaka matuka wajen kawo karshen matsalolin da suka dade suna hana yankin samun ci gaba.

Yerima ya kara da cewa shugabannin Arewa, duk da bambancin ra’ayoyin siyasa, za su hada kai wajen jagorantar samar da taswirar hanyoyin magance matsaloli da suka dade suna hana yankin samun ci gaba a baya, tare da bude sabon babi na cin gajiyar dimbin albarkatun dan Adam da na kasa da yankin ke da su.

A karshe, Shettima Yerima ya yi kira ga masu shirya taron hukumar raya Arewa maso yamma (NWDC), Kwamitin Majalisar Dattawa kan Arewa maso Yamma, da gwamnonin jihohi bakwai na yankin  da su tabbatar da aiwatar da shawarwarin da aka cimma a taron, domin amfanin al’ummar Arewa maso Yamma baki daya.

Masu ruwa da tsaki a taron sun bayyana  cewa irin wannan tattaunawa za ta zama tubalin samar da tsare-tsare masu amfani da za su taimaka wajen ceto Arewa maso Yamma daga halin kalubalen da ta tsinci kanta a ciki

An samar da Hukumar Raya Arewa maso Yammacin Nijeriya (NWDC) ne a shekarar 2024 da nufin bunkasa ci gaban jihohin yankin ta hanyar aiwatar da manyan ayyukan more rayuwa, farfado da tattalin arziki, da kuma tallafa wa al’ummomin da rikice-rikice da talauci suka shafa.

Arewa
Shehu Yahaya
+ postsBio
  • Shehu Yahaya
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-yahaya/
    Matasa 1,200 Sun Amfana Da Horon Sana’o’i Ƙarƙashin Shirin ‘Renewed Hope’ A Kaduna
  • Shehu Yahaya
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-yahaya/
    Ranar Dimokuraɗiyya: Gwamna Uba Sani Ya ‘Yanta Fursunoni 97
  • Shehu Yahaya
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-yahaya/
    Gwamna Sani Ya Kashe Sama Da Naira Biliyan Ɗaya Kan Tallafin Ɗalibai A Kaduna – Kwamishina
  • Shehu Yahaya
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-yahaya/
    Uba Sani Ya Sanya Hannu Kan Sabbin Dokoki A Bangaren Sauya Fannin Wuta, Noma, Da Muhalli

MASU ALAKA

Tsohon Shugaban APC Na Kebbi Ya Rasu A Hannun ’Yan Bindiga
Manyan Labarai

Tsohon Shugaban APC Na Kebbi Ya Rasu A Hannun ’Yan Bindiga

June 24, 2026
Maniyyatan Nijeriya
Manyan Labarai

Hajjin 2026: NAHCON Ta Kammala Jigilar Alhazan Nijeriya Daga Saudiyya

June 23, 2026
'Yan Bindiga
Manyan Labarai

Yan Bindiga Sun Kashe Manoma Shida A Birnin Gwari Ta Jihar Kaduna

June 23, 2026
Next Post
Atiku Ya Yi Allah-Wadai da Kashe Kashen Kwara, Katsina Da Binuwe

Atiku Ya Yi Allah-Wadai da Kashe Kashen Kwara, Katsina Da Binuwe

Discussion about this post

LABARAI MASU NASABA

An Kashe Mutum 2, 8 Sun Jikkata Yayin Rikici A Bauchi

An Kashe Mutum 2, 8 Sun Jikkata Yayin Rikici A Bauchi

June 24, 2026
Tsohon Shugaban APC Na Kebbi Ya Rasu A Hannun ’Yan Bindiga

Tsohon Shugaban APC Na Kebbi Ya Rasu A Hannun ’Yan Bindiga

June 24, 2026
Ya Kamata Sin Da Birtaniya Su Yi Aiki Tare Don Ci Gaba Da Inganta Dangantakarsu

Ya Kamata Sin Da Birtaniya Su Yi Aiki Tare Don Ci Gaba Da Inganta Dangantakarsu

June 23, 2026
Firaministan Sin Ya Jaddada Muhimmancin Kara Azamar Bunkasa Kirar Kayayyakin Aikin Masana’antu Na Zamani

Firaministan Sin Ya Jaddada Muhimmancin Kara Azamar Bunkasa Kirar Kayayyakin Aikin Masana’antu Na Zamani

June 23, 2026
Gombe Ta Zabge Farashin Taki Da Kashi 50 Cikin 100

Gombe Ta Zabge Farashin Taki Da Kashi 50 Cikin 100

June 23, 2026
Wang Yi Ya Gana Da Babban Sakataren Majalisar Tsaron Masar Da Ministan Fadar Gwamnatin Afirka Ta Kudu A Indiya

Wang Yi Ya Gana Da Babban Sakataren Majalisar Tsaron Masar Da Ministan Fadar Gwamnatin Afirka Ta Kudu A Indiya

June 23, 2026
‘Yansanda Sun Kashe Masu Garkuwa Da Mutane 8, Sun Kubutar Da Mutane 3 A Jihar Bauchi

’Yansanda Sun Kama Mutane 57 Da Ake Zargi Da Ayyukan Ta’addanci A Adamawa

June 23, 2026
Li Qiang Ya Gana Da Firaministan Kasar Guinea

Li Qiang Ya Gana Da Firaministan Kasar Guinea

June 23, 2026
Maniyyatan Nijeriya

Hajjin 2026: NAHCON Ta Kammala Jigilar Alhazan Nijeriya Daga Saudiyya

June 23, 2026
Kamfanin Sin Ya Kammala Babban Aikin Samar Da Ruwa A Babban Birnin Nijeriya

Kamfanin Sin Ya Kammala Babban Aikin Samar Da Ruwa A Babban Birnin Nijeriya

June 23, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.