A tsawon shekaru, an samu damuwa a tsakanin masu hulda da bankuna game da dimbin kudaden da suka makale a cikin bankunan ajiya na kudi (DMBs), a cikin asusun da ake ganin ba a amfani da su. Wato, asusun da masu shi ba sa gudanar da harkokin kudi a cikinsu.
Domin magance wannan matsala, Babban Bankin Nijeriya (CBN) yanzu ya ba da damar sake dawo da asusun da ba a amfani da shi ta hanyoyin sadarwa masu tsaro ba tare da bukatar rantsuwar ‘Affidabit’ ba, sai dai idan an riga an tura kudaden zuwa ‘Unclaimed Balances Trust Fund’.
Sabbin bukatun an tsara su ne domin “kara tabbatar da gaskiya da bayyana bayanai, saukaka mayar da kudade ga halastattun masu su, da kuma tabbatar da cikakken bin dokoki da ka’idojin da suka dace.”
Saboda haka, ana bukatar bankuna bisa tilas su wallafa bayanan asusun da ba a amfani da su a shafukansu na Intanet da kuma a jaridu.
Wadannan ka’idoji kan yadda ake kula da asusun da ba a amfani da su, kudaden da ba a karba ba da sauran kadarorin kudi a bankuna da sauran cibiyoyin kudi a Nijeriya, an tsara su ne domin kare muradun masu ajiya, hana ayyukan damfara, da kuma samar da tsari guda daya na yadda za a gudanar da asusun da ba a amfani da su da kuma kudaden da ba a karba ba.
Wadannan ka’idoji sun shafi dukkan cibiyoyin kudi da CBN ke sa ido a kansu, ciki har da bankunan kasuwanci, bankunan ’yan kasuwa (Merchant banks), bankunan da ba sa karbar ruwa (non-interest banks), da sauran cibiyoyin da ke karbar kudaden ajiya.
A karkashin tanade-tanaden wadannan ka’idoji, asusun da ba a gudanar da wani aiki a cikinsa sama da shekaru 10 ana daukar sa a matsayin asusun da ba a amfani da shi (dormant account).
Domin neman kudaden da ba a karba ba, masu asusu dole ne su gabatar da takardun da ke tabbatar da mallakar asusun, sahihiyar takardar shaida, shaidar wurin zama na yanzu, da kuma rantsuwar affidabit da ke tabbatar da cewa bayanan da aka bayar daidai ne.
A nasu bangaren, cibiyoyin kudi dole ne su tantance irin wadannan bukatu, sannan su aika da su tare da takardun da suka dace zuwa Babban Bankin Nijeriya (CBN) cikin kwanaki 10 na aiki.
CBN kuma zai duba bukatun, sannan ya mayar da kudin asali da duk wata ribar da ta taru cikin wasu kwanaki 10 na aiki.Sai dai, wannan tsarin bai shafi asusun da ke gaban kotu, wadanda ake gudanar da bincike a kansu, ko kuma wadanda aka yi amfani da su a matsayin jingina ba.
Babban bankin ya kuma bayyana wasu muhimman masu ruwa da tsaki da kuma nauyin da ke kansu a karkashin wadannan ka’idoji. Daga cikinsu akwai: Babban Bankin Nijeriya (CBN): Shi ne ke da alhakin kafawa da kula da asusun Unclaimed Balances Trust Fund (UBTF), tare da tabbatar da cewa ana bin wadannan ka’idoji yadda ya kamata.
Cibiyoyin kudi: Ana bukatar su sanya ido kan asusun da ba a gudanar da harkoki a cikinsu, sanar da kwastomomi, tabbatar da tsaron asusun da ba a amfani da su, sannan su tura kudaden da ke cikin irin wadannan asusu zuwa UBTF Pool Account bayan shekaru 10.
Haka kuma, ana bukatar su tsara tare da aiwatar da manufofi na kula da asusun da ba a amfani da su, su adana sahihan bayanai, sannan su tabbatar da cewa an tura kudaden da ke cikin irin wadannan asusu zuwa UBTF Pool Account bayan cikar shekaru 10.
A nasu bangaren, masu asusu za su iya amfana da ingantattun hanyoyi masu sauki da tsaro wajen sarrafawa tare da karbo kudaden da ke cikin asusun da ba a amfani da su da kuma kudaden da ba a karba ba.
Bayan fara aiwatar da wadannan ka’idoji, wasu bankuna sun wallafa bayanan asusun da ba a amfani da su guda 321,181. Hakan na zuwa ne yayin da masana tattalin arziki suka yi gargadin cewa umarnin CBN ya haifar da manyan matsaloli game da sanar da kwastomomi, hanyoyin sake kunna asusu, durkushewar kasuwanci, da kuma kare sirrin bayanan mutane.
Rahotanni sun bayyana cewa asusun da aka wallafa sun hada da na mutane, kamfanoni, kungiyoyin hadin gwiwa, coci-coci, kungiyoyin al’umma da kananan sana’o’i wadanda suka kwashe sama da shekaru 10 ba tare da an gudanar da wani aiki a cikinsu ba.
Jimillar asusun da bankunan suka wallafa sun kai kusan 321,181. Asusun sun nuna yadda rashin gudanar da harkoki ya yawaita tsakanin kananan da matsakaitan masana’antu (SMEs), kamfanonin mai da iskar gas, masu harkar sufuri da jigilar kayayyaki, coci-coci, makarantu, kamfanonin otal-otal da baki, kamfanonin magunguna, masu harkar sufuri ta ruwa, da kuma kananan ’yan kasuwa.
Babban bankin ya kara bayyana cewa bukatar bayyana wadannan bayanai ta yi daidai da tanade-tanaden Dokar Kare Bayanai ta Nijeriya ta 2023 (Nigeria Data Protection Act, 2023), wadda ta ba da damar sarrafa bayanan sirri idan hakan ya zama dole domin cika wani nauyin da doka ta tanada ko kuma kare muhimman muradun rayuwar mutane.














