ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Tuesday, September 8, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Majalisar Dattawa Ta Damu Kan Tsarin Yaki Da COVID-19 Bayan Sake Bullar Cutar A Nijeriya

by Muhammad
4 months ago

Majalisar Dattawa ta buƙaci a ɗauki matakan gaggawa domin cike gibin da ke cikin tsarin yaki da annobar cututtuka a Nijeriya, bayan tabbatar da sabbin kamu wa da cutar COVID-19 a Jihar Cross River.

Kudirin ya fito ne daga Sanata Ipalibo Banigo, inda ta tunatar da cewa Sashe na 14(2)(b) na Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya na 1999 (da aka yi wa kwaskwarima) ya ɗora wa gwamnati alhakin tabbatar da tsaro da jin walwalar jama’a, ciki har da kare lafiyar al’umma.

Ta bayyana damuwa cewa tsawon lokacin da aka ɗauka kafin bayyanar cutar ya wuce abin da aka saba gani, lamarin da ke sanya fargabar yaduwar cutar a cikin al’umma. Ta kuma ce an gano wasu da ake zargi da kamuwa, kuma ana ci gaba da bibiyar waɗanda suka yi hulɗa da su.

ADVERTISEMENT

Sanatar ta jaddada cewa daukar matakai kan irin waɗannan annoba na buƙatar wadatattun kayan aiki kamar na’urorin gwaji da sinadarai, da kayan kariya ga ma’aikatan lafiya.

Sai dai ta yi gargadin cewa Hukumar Kula da Cututtuka ta Ƙasa, NCDC, na fuskantar ƙalubale saboda jinkirin sakin kuɗaɗe da matsalolin saye da ƙarancin kasafin kuɗi tun daga 2025.

LABARAI MASU NASABA

Yadda Na Tsira Daga Cutar Mashaƙo A Katsina: “Na Fara Da Tsartuwar Jini Tare Da Yawu”

2 – 3 Cikin 10 Na Masu Cutar Diphtheria Na Iya Mutuwa A Katsina – NMA

Ta tunatar kan darussan da aka koya daga annobar COVID-19, zazzabin Lassa da shirye-shiryen tunkarar Ebola, inda ta ce jinkirin gano cuta da rashin haɗin kai na iya ƙara cutar da lafiyar jama’a da tsaron ƙasa.

Bayan tattaunawa, Majalisar ta buƙaci Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya da NCDC su ƙara ƙaimi wajen sa ido, gwaje-gwaje da bibiyar masu hulɗa da marasa lafiya bisa ƙa’idojin ƙasa.

Haka kuma ta roƙi Ma’aikatar Kuɗi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki da ta gaggauta sakin kuɗaɗe tare da la’akari da buɗe hanyoyin tallafin gaggawa domin tunkarar annobar.

Majalisar ta kuma nemi cikakken rahoto daga NCDC kan matsayin shirin ƙasar, ciki har da yawan kayan aiki, dakunan gwaje-gwaje da shirye-shiryen tunkarar annoba.

Ta ƙara da kira ga a ƙarfafa wayar da kan jama’a a faɗin ƙasa domin hana yaɗuwar jita-jita da rage tsoro, tare da ƙarfafa bin matakan kariya.

Haka kuma ta buƙaci gwamnatocin jihohi su ƙarfafa shirye-shiryensu ta hanyar inganta tsarin sa ido, gaggawar daukar martani da saka hannun jari a harkar lafiya.

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya yaba wa masu gabatar da kudirin, yana mai cewa za a miƙa shawarwarin majalisar ga hukumomin da abin ya shafa domin ɗaukar matakin gaggawa.

Muhammad
+ postsBio
  • Muhammad
    Yadda Na Tsira Daga Cutar Mashaƙo A Katsina: “Na Fara Da Tsartuwar Jini Tare Da Yawu”
  • Muhammad
    An Naɗa Yusuf Nasidi Nasir A Matsayin Talban Barayan Kano
  • Muhammad
    Wani Kamfani Ya Tallafa Wa Masu Sana’ar Shayi A Kano
  • Muhammad
    Kosan Waka Ya Rasu, Gwamnan Kano Ya Jajanta Wa Iyalansa

MASU ALAKA

Yadda Na Tsira Daga Cutar Mashaƙo A Katsina: “Na Fara Da Tsartuwar Jini Tare Da Yawu”
Manyan Labarai

Yadda Na Tsira Daga Cutar Mashaƙo A Katsina: “Na Fara Da Tsartuwar Jini Tare Da Yawu”

September 3, 2026
Kiwon Lafiya

2 – 3 Cikin 10 Na Masu Cutar Diphtheria Na Iya Mutuwa A Katsina – NMA

August 30, 2026
Ko Kun San Amfanin Kwanciya Da Bangaren Hagu?
Kiwon Lafiya

Ko Kun San Amfanin Kwanciya Da Bangaren Hagu?

August 29, 2026
Next Post
Baje Kolin Canton Fair Karo Na 139 Ya Hallara Masu Sayayya Na Ketare Kimanin 245,000

Baje Kolin Canton Fair Karo Na 139 Ya Hallara Masu Sayayya Na Ketare Kimanin 245,000

LABARAI MASU NASABA

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026
Xi Ya Zanta Ta Wayar Tarho Da Firaministan Birtaniya

Xi Ya Zanta Ta Wayar Tarho Da Firaministan Birtaniya

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.