ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Daga Yankin Gulf Zuwa Afirka, Me Sansanonin Sojan Amurka Suka Haifar?

by CGTN Hausa and Sulaiman
6 months ago
Gulf

Sama da kwanaki 20 ke nan da Amurka da Isra’ila suke daukar matakan soja a kan Iran, sai dai martanin da Iran ta mayar ya sa wutar yaki har ta kama kusan dukkanin sassan yankin Gulf, lamarin da kuma ya tono mana gaskiyar yadda Amurka ke fakewa da batun kiyaye tsaro wajen kafa sansanonin sojanta a sassan duniya, duba da cewa sansanonin soja da ta kafa a kasashen yankin Gulf a maimakon su ba da kariya ga kasashen, sai ga shi har sun janyo musu hare-hare. Abin da kuma ya aza musu tambaya, wato ya kamata a dogara ga kasar da ke nuna fin karfi don ta samar musu abu na wai tsaro, ko kuma ya kamata su kiyaye mulkin kansu da kuma ’yancinsu?

Bisa ga kididdigar da aka yi, yanzu haka Amurka ta kafa sansanonin soja kimanin 800 a kasashe da shiyyoyi kimanin 80, sansanonin da suka taka muhimmiyar rawa a yake-yaken da Amurka ta yi cikin shekaru sama da 100 da suka wuce, wadanda kuma suka kasance muhimmiyar madogara a gare ta wajen nuna karfi da kafa babakere a fadin duniya. Amurka ta kan cimma burinta na kafa sansanoninta a wasu kasashe, ta hanyar daddale yarjejeniya da su game da samar musu tsaro, ta yadda za ta kai ga sa hannu, da ma ba da jagoranci a harkokin shiyyar. A hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kaddamar a kan Iran a wannan karo, sansanin sojan sama na Al Udeid da ke Qatar, da kuma sansanin rundunar sojan ruwa ta biyar ta Amurka da ke kasar Bahrain, duk sun zama ginshikin Amurka wajen daukar matakan soja. Daidai kamar yadda David Vine, mashahurin masanin ilmin aikin soja na kasar Amurka ya fada, cewa sansanonin soja na Amurka da ke ketare suna samar mata sauki wajen aiwatar da ayyukan soja, wadanda suka zama mafarin yake-yaken da take yi a sassan duniya.

ADVERTISEMENT

Sai dai ko da gaske ne sansanonin suna samar da tsaro ga kasashen da suka karbe su? Idan mun yi nazari a kan rikicin da ya faru a wannan karo, za mu gano cewa, ban da kasar Isra’ila, Iran ta kuma kai hare-hare sansanonin sojan Amurka da ke kasashen Qatar, da Kuwait, da hadaddiyar daular Larabawa, da Bahrain, da Saudiyya, da Iraki, da Jordan, kuma a cewar Iran, ba wai kasashen mashigin tekun Farisa take kaiwa hare-hare ba, a’a, sansanonin sojan da Amurka ta kafa a kasashen ne take hari.

LABARAI MASU NASABA

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta

Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin

Lallai na’urorin soja da Amurka ta girke a maimakon su samar wa kasashen tsaro, ga shi sun zama abin da ke janyo musu rashin tsaro. Dalilin hakan shi ne ainihin rawar da sansanonin suke takawa, ita ce kare muhimman muradun kasar Amurka, ko ta zama hanyar shawo kan Iran, ko samun iko a kan muhimman hanyoyin ruwa, ko kuma kwace albarkatun kasa. Amma idan rikici ya tsananta, sansanonin su kan zama wurare da ake kaiwa hare-hare.

A nahiyar Afirka ma, Amurka ta fake da batun “yaki da ta’addanci” da na “hadin gwiwar tsaro”, wajen kafa sansanonin soja a wasu kasashen nahiyar. Sai dai sansanonin da ma sojojin da take girkewa sun kasa samar da abu da take kira wai tsaro. In mun ba da misali da Nijer, inda kasar Amurka ta fara kafa sansanonin soja a kasar tun shekarar 2013, bisa sunan wai yaki da ta’addanci da dakaru masu tsattsauran ra’ayi a yankin Sahel. Amma sama da shekaru 10 sun wuce, ayyukan ta’addanci sun dada karuwa a maimakon raguwa. A ganin kasar Nijer, hakan ya faru ne sakamakon yadda Amurka ta fake da batun yaki da ta’addanci wajen cimma muradun kanta a shiyyar, lamarin da ya sa ta kori sojojin Amurka a shekarar 2024.

Hakikanan abubuwan da suka faru sun yi ta shaida cewa, amincewa da kafa sansanonin sojan kasar Amurka ya gaza samar da tsaro ga kasashen da suka karbe su. Ko a yankin Gulf ko kuma a nahiyar Afirka, ba za a kai ga tabbatar da tsaro ba, har sai an tsaya an kafa ikon kai na aiwatar da harkokin diplomasiyya, da hadin gwiwa da kasashen yankin, da kuma tabbatar da tsaro na bai daya. A lokacin da laimar kariya ta rika zama abin da ke janyo rashin tsaro, to, lokaci ya yi da ya dace a sake tunani game da me ya kamata a zaba.

Gulf
CGTN Hausa
+ posts Bio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa
Gulf
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Na Sayar Da ’Ya’yana, Na Sace Wasu 19 – Wata Da Ake Zargi Da Safarar Yara
  • Sulaiman
    Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan
  • Sulaiman
    ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto
  • Sulaiman
    PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

MASU ALAKA

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta
Ra'ayi Riga

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta

September 8, 2026
Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin
Ra'ayi Riga

Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin

September 4, 2026
Samun Rarar Kudin Ciniki Ba “Laifi” Ba Ne, Hadin Gwiwa Da Cin Moriya Tare Ita Ce Mafita Ga Kowa
Ra'ayi Riga

Samun Rarar Kudin Ciniki Ba “Laifi” Ba Ne, Hadin Gwiwa Da Cin Moriya Tare Ita Ce Mafita Ga Kowa

September 2, 2026
Next Post
APC Ta Bayyana Shirin Taron Ƙasa Don Zaɓen 2027 — Masari

APC Ta Bayyana Shirin Taron Ƙasa Don Zaɓen 2027 — Masari

LABARAI MASU NASABA

’Yan Takarar ADC A Arewa Maso Yamma Sun Yi Alƙawarin Biyan N110,000 A Matsayin Mafi Ƙarancin Albashi

’Yan Takarar ADC A Arewa Maso Yamma Sun Yi Alƙawarin Biyan N110,000 A Matsayin Mafi Ƙarancin Albashi

September 9, 2026
Yadda Jami’an ‘Yansanda Suka Yi Garkuwa Da Wani Mazaunin Abuja, Sun Kwashe Fiye Da Naira Miliyan 20 A Asusunsa

Na Sayar Da ’Ya’yana, Na Sace Wasu 19 – Wata Da Ake Zargi Da Safarar Yara

September 9, 2026
Iran Ta Musanta Ikirarin Trump Tare Da Zafafa Hare-hare Kan Isra’ila

Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan

September 9, 2026
ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

September 9, 2026
Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.