ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Dalilan Da Suka Sa Ba Zan Iya Auren Ɗan Film Ba —Bilkisu Bishasha

by Abubakar Abba
3 weeks ago
Film

Bilkisu Ibrahim Bishasha, matashiyar ƴan Film ce, a masana’antar Kannywood.

A hirarta ta da wakilinmu na Kaduna ABUBAKAR ABBA, ta yi bayani kan abinda ya ja hankalinta, ta fara yin Film, goyon bayan da samu daga gun mahifarta, mutuwar aurenta, tare da bayyana dalilinta na rashin son auren Jarumi, a masana’antar da sauransu.

Ki ɗan gaya mana taƙaitaccen tarihin ki?

ADVERTISEMENT

An haife ni a ƙaramar hukumar Kauru a Jihar Kaduna.

Me yana ra’ayinki shiga masana’antar Kannywood?

LABARAI MASU NASABA

Tun Ina Karama Marigayi Tumbuleke Ke Sa Ni Dariya —Hannatu Musawa

Nazari Kan Wasu Dalilan Da Ke Haddasa Sabanin Abotakar Jarumi Ko Jaruma A Kannywood

Tun ina ƙaramar yarinya, inda da sha’awar Film, amma a  lokacin mahaifinmu na raye, ba ma zai bari, mu shiga yin Film ba.

Da na yi aure, auren ya mutu, na zo na sake yin wani auren, shi ma muka rabu da mijina, sai na ci gaba da zama a gida, daga nan, sai na cewa wa mamana, ni dai da zaman nan ma, gwara in je, in shiga Film, ta ce to idan shi ne hanyar arzikin ki, Allah ya ba ni sa a ya kuma taimaka, ke dai kawai, ki tsare kanki.

Amma wasu musamman mata da ke da cewa, sha’awar shiga Film bayan sun baro gidajensu, ba su samun damar ko ganin mai shiya Film, ke ma kin fuskanci hakan kafin ki shiga?

Gaskiya ne, ana samun wannan ƙalubalen, amma ni, gaskiya ban sha wata wahala ɓa wajen shiga Film, awaki wani abokin yaya na, wanda ina zaune ya kira ni ya ce min, akwai wani sabon kamfanin yin Film da suka buɗe, na matsan ƴan wasan Film, ko zan iya shiga, na ce masa to, a lokacin ne, ma na yiwa maman mu magana, sai ta ce, ba damuwa, to daga nan ne, na fara.

Wato dama dai, an tallata maki shida masana’antar ke nan?

Ah!, to a lokacin ne, na ce masa zan yiwa maman mu magana, idan ta amince, sai ya ce, idan ta amince, in shigo garin Kaduna za mu je, a yi gwaji, to a lokacin sai mamanmu, ta amince, daga nan ne, na fara shiga harkar Film.

Wanne Film ɗin kika fara fitowa na farko?

Mun yi wani Film da yake ƙaramin kamfani ne, gaskiya, a U-Tube aka sanya kuma daga baya, abin ya zo ya shirance.

Menene sunan Film ɗin?

Wallahi na manta tunda yanzu kusan shekaru huɗu ke nan da yinsa.

Yau shekara nawa ke nan ki ka fara yin Film gadan-gadan?

Yanzu na kai shekarun huɗu ke nan, domin a waccan lokacin wata ƴar ƙaramar kyamara ce, muke yin amfani da ita a wajen yin gwajin ɗaukar Film har wasu mutane, na yi mana dariya.

Kin yi maganar aure bayan auren ya mutu, yaya maganar ƴaƴa fa?

Allah ya bani ƴaƴa biyu.

Tunda kin ce, shekara huɗu ke nan da fara sana’ar Film, yaran ba su yi wani girma ba ke nan?

Gaskiya, ba su yi wani girma ba sosai.

Shin, kina da ra’ayin yanzu idan ƴaƴanki sun girma suka nuna sha’awar shiga Film, za ki bar su su yi?

Ni ma, na taɓa tayin cewa, idan ma, ana neman yarinya ƙarama, akwai yarinyata.

Akwai zarge-zargen da wasu ke yi cewar, a Film akwai rashin talbiyya da sauransu, ke baki fuskanci hakan ba, da har ki ke son, sa ƴaƴanki a Film?

Gaskiya ni, ban fuskanci hakan ba, saboda ni, na ɗauki Film, sana’a ce, kuma idan ka riƙe ta a sana’a, za ta riƙe ka, sana’a.

Amma ba a iya haɗa mace da namji a ɗaki ɗaya?

Ba a haɗa mace da namiji a ɗaki ɗaya.

Waɗanne  Fina- Finai ne, ki ka fito a cikinsu?

Akwai na Duhun Zuciya, wanda shi ne, ƴan kallo suka fara   sani na, sai kuma aka dakatar da aikin, wanda  mai dogon zango ne. akwai wanda na fito, a matsayin Aljana, na kuma fito a Film ɗin, matar waye da sauransu.

Duk a cikin waɗannan Fina- Finan da ki ka zayyano, wannene tun lokacin da ku ke ɗauka, ki ka ji ya fi ba ki sha’awa?

Gaskiya, Film ɗin Halimatu ya fi bani sha’awa tun a lokacin da ake kan ɗaukarsa.

Daga shi fa sai wanne?

Duhun Zuciya shi ma ya birge ni, ni kankin kai na.

Me ya sa a zahiri, ki ke ƙaunar Film ɗin Duhun Zuciya?

Saboda labari ne, mai ɗauke da darasi, da ke koyar da bin maganar iyaye, rashin yin hakan, mutum zai yi danasani.

Su waye Jarumansa?

Ni ce, na fito mai suna Humairah kuma ni ce, na ja shirin Film ɗin, sai shi saurayi na a Film ɗin, Sabi’u.

Wacce rawa ki ka taka a Film ɗin Halimatu?

N fito ne a matsayin Amaryar Baba Ɗan Audu.

Amma Baba Ɗan Audu a cikin labarina aka fi sanin wannan sunan?

A toh! kusan dai sunan da aka sanyawa angina nawa a Film ɗin ke nan, kuma sunan gabi shi, kowa Baba Ɗan Audu.

Wato kin fito a matsayin matar Rabi’u Rikadawa a Film ɗin na Halimatu?

Na fito ne a matsayin matarsa, kuma shi ne Film ɗin da aka fi sani na sosai.

Shi me Film ɗin Halimatu ya ƙunsa ne?

Yarinya ce kamar suke zaune a cikin jin faɗin rayuwa ita da mahaifiyarta da ƴaruwarta, kafin nan, wata rana, Hajiya ta yi tafiya, sai ta ga wata yarinya a bakin Titi wasu maza da mata sun rufe ta duka, sai Habitat ta tsaya ta raba, ta ce, bari ta ɗauke ta, ta kaita gidanta, amma shi Alhajin mijin Hajiyar bai so hakan ba, to dai, ta yi masa bayani cewa, da na kowa ne, sai ya yarda.

A kwana a tashi, sai yarinyar, ta fara yin kisisina irin ta mu ta mata domin ta ja ra’ayin Alhajin.

A masana’nar wasu Jarumai ta na da masoyi wanda har soyayyar kan rikiɗewa zuwa yin aure, ko akwai wani Jarumin da a masana’antar, da ya nuna sha’awar auren ki?

Gaskiya akwai wani wanda mun shirya yin aure sai Allah ya yi masa rasuwa.

Amma ke a kan kanki, kina da sha’awar ki auri ɗan Film?

Gaskiya ni, ba zan iya aurar ɗan Film ba, saboda ina da kishi domin a wani lokacin, ina ɗewa wasu jaruman maza cewa, wallahi matan na haƙuri da ku, amma sai dai su yi dariya su ce, ai Film, ya zamar masu hanya ce ta cin abinci.

Akwai wani abu da ake cewa, jarumai maza a masana’antar Tuwo a Ƙwarya, sai ki ga sun dade, a masana’antar ba su yi kuɗi ba, amma sai wata jarumar da ta shigo harkar ta riga su yin kuɗi a masana’antar, shin me ke kawo hakan?

Ah toh! abinda ke kawo hakan, ka ga ita macen da ke a masana’antar, za ta yi samari ya na ba ta kuɗi ko jari domin kar ta dogara a harkar Film kawai, ta kan ɗan fara juya kuɗin a sana’ar da ta fara ko kuma saurayin, ya ɗan says mata motar hawa.

To amma bayan Film ke ma kina yin wata sana’ar?

Ina yin sana’ar sayar da Takalma ko Jakankunan hannu na mata

Mun gode

Nima na gode

Film
Abubakar Abba
+ postsBio
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Tun Ina Karama Marigayi Tumbuleke Ke Sa Ni Dariya —Hannatu Musawa
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    NPA Ta Bayyana Cewa Kirkiro Da Sabuwar Hukumar NPERA Ba Zai Zame Mata Tarnaki Ba
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Yadda Bikin Girke-girke Ya Karfafa Alaka Tsakanin Musulmai Da Kiristoci A Kaduna
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Nazari Kan Wasu Dalilan Da Ke Haddasa Sabanin Abotakar Jarumi Ko Jaruma A Kannywood

MASU ALAKA

Tun Ina Karama Marigayi Tumbuleke Ke Sa Ni Dariya —Hannatu Musawa
Nishadi

Tun Ina Karama Marigayi Tumbuleke Ke Sa Ni Dariya —Hannatu Musawa

September 5, 2026
Nazari Kan Wasu Dalilan Da Ke Haddasa Sabanin Abotakar Jarumi Ko Jaruma A Kannywood
Nishadi

Nazari Kan Wasu Dalilan Da Ke Haddasa Sabanin Abotakar Jarumi Ko Jaruma A Kannywood

August 29, 2026
Nishadi

Tazarcen Tinubu A 2027: Bai Kamata A Yi Wa Ƴan Kannywood Kuɗin Goro Ba —Na Buraska

August 16, 2026
Next Post
Film

Yadda Kamfanin Dangote Ya Gudanar Da Bikin Ranar Matasa Ta Duniya A Obajana

LABARAI MASU NASABA

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026
Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

September 9, 2026
Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

September 9, 2026
Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

September 9, 2026
Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

September 9, 2026
“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

September 9, 2026
’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

September 9, 2026
Taron Kolin Urumqi Ya Mayar Da Hankali Kan Kwarewar Shugabanci A Xinjiang Da Muhimmancinta Ga Duniya

Taron Kolin Urumqi Ya Mayar Da Hankali Kan Kwarewar Shugabanci A Xinjiang Da Muhimmancinta Ga Duniya

September 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.