Alhaji Mustapha Badamasi da aka fi sani da Na Buraska, fitaccen ɗan wasan kwaikwayo ne musamman fannin barkwanci a Masana’antar Kannywood.
Wakilinmu ABUBAKAR ABBA ya tattauna da shi a Kaduna, inda ya yi bayani, tun daga kan tarihinsa, abin da ya sa bai jin tsoron margayi Ibro, idan suka fito a Fim, Fim da shi kansa ya fito ya kuma fi birge shi, da matsayinsa a takarar shugaban ƙasa Bola Tinubu a 2027.
Taƙaitaccen Tarihi:
An haife ne a Jihar Kano, na yi makarantar Firamare da ta Sakandare a Kano na kuma wuce zuwa Zaria, na ƙaro karatu, duk abin da ya shafi, karatun zamani da na addini, ba wanda ban yi ba, daidai gwargwado.
Shekarar Fara Yin Fim:
Ba zan iya tunawa ba, abin da ya wa, saboda a lokacin da hankali kwance idan ka shigo masana’antar, a rana za ka iya ganin masu shirya goma, zai zo ya ɗauke a fitowa ɗaya da kai ko zuwa fitowa daga biyu zuwa uku, wani zaka iya yi masa fitowa biyar zuwa goma, waɗanda zai rarraba fitowar a cikin wasu Fina-Finai. A saboda haka, ba zan iya gane ainihin Fim ɗin da na fara ko riƙe sunansa ba.
Fina-Finan Da Ya Taka Rawa:
Akwai su da dama, kamar na Shela, Daso Ƴar Indiya, Ibro P-Sƙure, Ibro mai Naira, Babban Yaro, Babban Yarinya, Basaja, Na Buruska, Ƙuruciya, Babban Zaure, Adon Gari, da sauransu.
Rawar Da Ya Taka A Fim Ɗin Basaja:
Na fito ne, a matsayin ɗan damfara da wata mariganyiya, da Adam A. Zango ke son ya ɗan ribace ta, ta yadda za ta yarda da shi, sai na yi fitowa ta musamman, a fitowa ta ɗaya, na zo na ce mata, don Allah ki taimake ni ki sa baki, wannan bawan Allah ya ba ni Shinkafa, domin a Fim ɗin, ni dilan Shinkafa ne.
Sai ta ce, ai ita ma, yau ta fara ganinsa, sai na ce mata, ai shi babban mutum ne, duk garin nan, babu wanda ke kawo Shinkafa sai shi, domin idan ya baka Shikafa, to ba ƙaramin jari, ko ƙaramin tasiri abin zai yi ba.
Sai ta ce min shi ke nan, ganin kwarjinin da na zo mata dashi da kuma ni kai na, ba ta taɓa gani na ba, amma ai a makaranta ta ke gani na a matsayin ɗalibi ne, sai ta faɗa a cikin tayin da soyayyar Adam Zango ya yi mata.
To marubucin Fim ɗin sai yaga damfarar ta wa, ta yi daidai da wannan, sai na zama, a matsayin mai taimaka wa Jarumin Fim ɗin Adam Zango, wato a turance, ‘supporting Actor’ a Fim ɗin Adam Zango, na Basaja, duk inda ya cire ƙafa, ni kuma zan sa tawa ƙafar.
Babban Abin Da Zan Iya Tunawa a Fim Ɗin Babban Yaro:
An yi Fim ɗin ne, domin nisahaɗantar da masu kallo, a cikin Fim ɗin, da ni da Musa Mai Sana’a da sauran ragowar jaruman, mun fito a wani ƙauye muke, amma muna ƙaryar cewar mu Nigogi ne, mun sami Radiyo muke jin kiɗa muna koyon rawa, su kuma a ɓangaren su Adam Zango, muke ƙoƙarin mu yi masu fata-fata, to wannan abin ya yi tasiri, masu kallo sun nishaɗantu da Fim ɗin.
Film Ɗin Dani Kai Yafi Nishantar Da Kai:
Akwai Fim ɗin Tashar Daji, ni da Ibrahim Ɗan Ibro, wanda na fito a ɗan daba kuma Ibro na jin tsoro na kuma na ga ƴarsa, ina so zan aura.
A cikin Fim ɗin, na ɗan sha wahala, saboda yanayin da na fito a cikinsa, ta yin dabancin, domin idan za ka sauya murya, ana shan wahala ba ɗan kaɗan ba da kuma yadda za ka ɗage Kafaɗarka, ka yi wata fitowa a cikin Fim ɗin ta irin waɗannan mutanen, ba ƙaramar wahala na sha ba, Fim ɗin na Tashar Daji ya yi matuƙar tasiri gaskiya, saboda an zuba masa jarumai, a lokacin Bosho shi ne Maigari, shi kansa a Fim ɗin yana jin tsoro na, domin idan aka zo Fadarsa aka ce masa Buzuzu ne ya yi, baya yarda ya shigowa cikin sabga ta, saboda ya taɓa shiga cikin sabga ta sau biyu, na bazar da shi.
Yawan Fitowa Ta A Fim Da Marigayi Ibro:
Gaskiya ne, domin kusan marigayi Ibro mutuwarsa ba ƙaramin taɓa ni ta yi ba, sai da muka jero kusan shekaru daga uku zuwa huɗu, muna Kankan da shi, a fitowa tare a Fim ana haɗa mu tare, saboda haɗin masu kallo sun ce, ya bayar da sha’awa.
A duk Fim ɗin da na fito da Ibro ni ba na nuna ina jin tsoronsa, domin akwai wasu jaruman kwamedi, suna jin tsoronsa saboda ya zama tamkar mai gida, shi kuma fitowa a Fim, so ake yi ka yi shi gadan-gadan, domin idan ko yaya ka ɗan nuna shakka a Fim ɗin, to ba zai ƙawatar ba da masu kallo ba.
Me Ya Sa Wasu Ƴan Masana’antar Kannywood Ke Ficewa Daga Ƙungiyar Triple R Kannywood ta Dauda Kahutu Rarara?:
Sai idan kana cikin ƙungiya ne, za ka iya sanin me ke cikinta, tunda kaga ni bana cikinta, duk abin da na sa baki, ban yi masu adalaci ba.
Wasu Ƴan Nijeriya Na Buƙatar Sanin Me Ya Sa Wasu Daga Cikin Ƴan Kannywood Ke Goyon Bayan Ta Zarcen Shugaba Ƙasa Bola Tinubu A 2027
Adalcin da ya kamata alumma su yi shi shi ne, ai ba duka a taru aka zama ɗaya ba, fuskar da ka gani ta fito ta yi tallan abin da ba ka da ra’ayi a kai, a kanta ya kamata al’umma su yi hukunci, domin masana’antar Kannywood, akwai ta a jihohin Kaduna, Kano, Zamfara, Sokoto, Kebbi, Katsina da sauransu.
To shi ke nan, idan ƴan masana’antar Kannywood na Kano misali ya yi wani abu, sai a haɗa sauran a yi masu kuɗin Goro, kaga hakan, ba daidai ba ne, wanda ka ga fuskarsa a ciki, shi ya kamata ka tsaya a kansa.













