Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya buɗe wani shafin intanet mai suna Askatuku.ng, domin bai wa ’yan Nijeriya damar yi masa tambayoyi kan manufofinsa da shirye-shiryensa idan aka zaɓe shi shugaban ƙasa.
Shafin na bai wa masu sha’awar sanin matsayinsa kan batutuwa daban-daban damar tura tambayoyinsu, sannan su zaɓi ko suna son a aika musu da amsoshin ta imel ko kuma ta WhatsApp. Ya zuwa lokacin tattara wannan rahoto shafin ya karɓi tambayoyi sama da 1,000.
Ɗaya daga cikin tambayoyin da aka tura wa Atiku ta fito ne daga Abdullahi Dutsinma, wanda ya nemi sanin matakan da zai ɗauka wajen shawo kan matsalar tsaro a Katsina da sauran jihohin Arewa maso Yamma, Arewa maso Gabas da kuma ƙasar baki ɗaya idan ya zama shugaban ƙasa.
Da yake amsa tambayar, Atiku ya ce idan aka zaɓe shi, gwamnatinsa za ta ƙara yawan jami’an tsaro tare da samar musu da kayan aiki na zamani domin yaƙi da masu garkuwa da mutane da kuma masu kai hare-hare. Ya ce matakan za su taimaka wajen dakile ayyukan masu aikata laifukan tsaro.
A wata tambaya da Denis Lokoja, ya yi masa kan dalilin kafa Jami’ar ABTI da ke Yola, Atiku ya bayyana cewa ra’ayin kafa jami’ar ya samo asali ne daga irin ƙalubalen da ya fuskanta wajen samun ilimi a lokacin ƙuruciyarsa, musamman ƙarancin malamai bayan da Turawan mulkin mallaka suka fara barin Nijeriya bayan samun ‘yancin kai a 1960.
Ya ce wasu jami’an wanzar da zaman lafiya guda 10 ne suka zo suka koyar da su a lokacin, kuma ilimin da ya samu daga gare su ya yi tasiri sosai a rayuwarsa. Atiku ya ƙara da cewa bayan kammala jami’a, shiga aikin gwamnati da harkokin kasuwanci, ya fara tunanin yadda zai taimaka wa al’ummarsa, wanda hakan ya kai ga kafa Jami’ar ABTI.
A cewarsa, ya je Amurka domin neman haɗin gwiwar kawo malamai, inda wasu daga cikinsu suka zo suka duba makarantar da hanyoyin samun kuɗin gudanar da ita kafin a fara ginin jami’ar a Yola. Ya ce ya zaɓi Yola ne saboda irin amfanin da ya samu daga malamai da suka taimaka masa wajen neman ilimi a wannan yanki.














