ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, July 25, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

ASUU Na Barazanar Shiga Yajin Aiki A Jami’o’in Jihohi 11 Kan Rashin Biyan Alawus-alawus

by Sani Anwar
3 weeks ago
ASUU

Ƙungiyar malaman jami’o’i (ASUU), ta yi barazanar shiga yajin aiki na dindindin a jami’o’in jihohi 11, idan gwamnatocin jihohin Ido, Delta, Ondo, Adamawa, Borno, Taraba da Yobe suka kasa aiwatar da yarjejeniyar gwamnatin tarayya da ASUU daga nan zuwa ƙarshen watan Yuli na shekarar 2025.

Shiyyoyin Benin da Yola na ƙungiyar, sun yi wannan gargaɗin ne a wani taron manema labarai daban-daban a ranar Litinin, inda suka zargi gwamnatocin jihohin da abin ya shafa da gaza aiwatar da yarjejeniyar wata shida, bayan ƙulla yarjejeniyar.

Shugaban shiyyar Benin, Farfesa Monday Igbafen, ya ce; rassan ASUU da ke cikin jami’o’in da abin ya shafa, sun fara haɗa kan mambobin ƙungiyar, domin rufe harkokin ilimi baki-ɗaya.

ADVERTISEMENT

Jami’o’in, sun haɗa da Jami’ar Ambrose Alli, Ekpoma; Adekunle Ajasin, Akungba-Akoko; Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Olusegun Agagu, Okitipupa; Jami’ar Jihar Delta, Abraka; Jami’ar Delta, Agbor; Jami’ar Dennis Osadebay, Asaba; Jami’ar Kudancin Delta, Ozoro; Jami’ar Jihar Adamawa, Mubi; Jami’ar Jihar Borno, Maiduguri; Jami’ar Jihar Taraba, Jalingo; da kuma Jami’ar Jihar Yobe, Damaturu.

Igbafen ya ce, yayin da jami’o’in gwamnatin tarayya da jami’o’in jihohi da dama suka aiwatar da yarjejeniyar, har yanzu jihohin da abin ya shafa ba su biya kuɗin tallafin karatu na CATA da sauran alawus-alawus da basussukan da aka amince da su daga watan Janairun 2026.

LABARAI MASU NASABA

Kano Ta Yi Zarra Wajen Kashe Kuɗi Don Raya Ilimi A Yammacin Afirka

Matar Gwamnan Zamfara Ta Sha Alwashin Ci Gaba Da Tsarin Bunƙasa Ilimin Ƴa Mace

Haka zalika, Shugaban shiyyar Yola, Kwamared Dani Mamman, ya ce; ci gaba da rashin aiwatar da yarjejeniyar da sauran alawus-alawus ɗin da aka tattauna, ya haifar da tashin hankali a cibiyoyin da abin ya shafa.

Har ila yau, ya kuma bayyana lamarin a matsayin rashin adalci da kuma keta haddi na gamayya, yana mai jaddada cewa; malamai suna neman halak ɗinsu ne kawai.

Ƙungiyar ta yi kira ga gwamnonin da abin ya shafa, da su gaggauta aiwatar da yarjejeniyar tare da warware duk wasu basussukan da ake bin su, domin kaucewa yajin aikin da ba a san ƙarshensa ba, wanda ka iya harfar da koma baya a sha’anin ilimi.

ASUU
Sani Anwar
+ postsBio
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Yadda Ciwon Hanta Ke Yaduwa Tsakanin Ma’aurauta
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Sake Daukar Shettima Da Tinubu Ya Yi Zai Kara Karfafa APC A Zaben 2027 –Farfesa Yerima
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Shugaban Rundunar Sojojin Nijeriya Ya Nemi Haɗin Kan Fararen Hula
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Ƴan Ƙwadago Sun Buƙaci Naira 300,000 A Matsayin Mafi Ƙarancin Albashi

MASU ALAKA

Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya
Ilimi

Kano Ta Yi Zarra Wajen Kashe Kuɗi Don Raya Ilimi A Yammacin Afirka

July 11, 2026
Matar Gwamnan Zamfara Ta Sha Alwashin Ci Gaba Da Tsarin Bunƙasa Ilimin Ƴa Mace
Ilimi

Matar Gwamnan Zamfara Ta Sha Alwashin Ci Gaba Da Tsarin Bunƙasa Ilimin Ƴa Mace

June 20, 2026
Hukumar Ilimin Bai-ɗaya Ta Jihar Yobe Ta Raba Kayan Karatu
Ilimi

Hukumar Ilimin Bai-ɗaya Ta Jihar Yobe Ta Raba Kayan Karatu

June 20, 2026
Next Post
‘Lokaci Ya Yi Na Ɗaukar Mataki Kan Masu Yanke Hukunci Da Kansu’

'Lokaci Ya Yi Na Ɗaukar Mataki Kan Masu Yanke Hukunci Da Kansu'

LABARAI MASU NASABA

An Karrama Masana Ilimin Lissafi Na Kasar Sin Da Lambobin Yabo Na Fields Medal

An Karrama Masana Ilimin Lissafi Na Kasar Sin Da Lambobin Yabo Na Fields Medal

July 24, 2026
Ta Da Zaune Tsaye Da Philippines Ta Yi A Teku Ba Zai Lalata Dangantakar Hadin Gwiwar Sin Da ASEAN Ba

Ta Da Zaune Tsaye Da Philippines Ta Yi A Teku Ba Zai Lalata Dangantakar Hadin Gwiwar Sin Da ASEAN Ba

July 24, 2026
Jadawalin INEC:Kotun Daukaka Kara Ta Kassara Fatan Jam’iyyu Da ‘Yan Siyasa

Jadawalin INEC:Kotun Daukaka Kara Ta Kassara Fatan Jam’iyyu Da ‘Yan Siyasa

July 24, 2026
An Zartas Da Sanarwar Chengdu A Taron Ministocin Kungiyar APEC Kan Harkar Raya Fasahohin Dijital Da AI

An Zartas Da Sanarwar Chengdu A Taron Ministocin Kungiyar APEC Kan Harkar Raya Fasahohin Dijital Da AI

July 24, 2026
NNPP Za Ta Kwace Mulki A Jihar Imo – Kwankwaso

Jam’iyyar NDC Ta Shirya Tsaf Domin Kafa Gwamnati A 2027 —Kwankwaso

July 24, 2026
Sin Ta Kara Kamfanoni 14 Na Tarayyar Turai Cikin Jerin Wadanda Aka Hana Fitar Masu Da Kaya

Sin Ta Kara Kamfanoni 14 Na Tarayyar Turai Cikin Jerin Wadanda Aka Hana Fitar Masu Da Kaya

July 24, 2026
Kashim Shettima Ya Mayar Da Martani Kan Tsadar Rayuwa

Kyamar Baki: Shettima Ya Ja Kunnen Gwamnatin Afirka Ta Kudu

July 24, 2026
Yadda Kasar Sin Ta Samar Da Ci Gaba Na Bai Daya

Yadda Kasar Sin Ta Samar Da Ci Gaba Na Bai Daya

July 24, 2026
Hatsin Da Kasar Sin Ta Girbe Da Lokacin Zafin Bana Ya Zarce Tan Miliyan 150

Hatsin Da Kasar Sin Ta Girbe Da Lokacin Zafin Bana Ya Zarce Tan Miliyan 150

July 24, 2026
Wani Dalilin Da Ya Sa Al’Ummar Afirka Ke Kaunar Kasar Sin Shi Ne Yadda Take Kokarin Zuba Musu Jari

Wani Dalilin Da Ya Sa Al’Ummar Afirka Ke Kaunar Kasar Sin Shi Ne Yadda Take Kokarin Zuba Musu Jari

July 24, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.