Babban Sakataren Ma’aikatar Muhalli da Albarkatun Ƙasa ta Jihar Nasarawa, Barista Ede Yahaya Yakubu, ya sake jaddada cewa dokar da ta haramta sare itatuwa da kuma harkar samar da gawayi tana nan daram, yana mai gargadin cewa duk wanda aka kama yana gudanar da irin wannan aiki zai fuskanci hukunci kamar yadda doka ta tanada.
Barista Ede Yahaya ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai a ofishinsa da ke Lafia, inda ya ce gwamnatin jihar ba ta janye dokar ba, kuma tana ci gaba da aiwatar da ita domin kare muhalli da dakile illolin sauyin yanayi.
Ya ce manufar gwamnatin na hana sare itatuwa ta samo asali ne daga ƙudurin kare dazuzzuka da kuma hana ci gaba da lalacewar ƙasa, wadda ke barazana ga rayuwar al’umma da ci gaban jihar.
A cewarsa, masu harkar gawayi na aikata abin da ya saɓa wa doka, saboda haka jami’an tsaron dazuzzuka na ci gaba da sintiri domin kamo masu karya dokar.
“Idan jami’an tsaron dazuzzuka suka kama mutum da gawayi ko kuma yana gudanar da wannan sana’a, za a kama shi tare da ɗaukar matakin doka a kansa, ciki har da cin tara,” in ji shi.














