Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya buƙaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya buɗe asusun Kamfanin Mai na Ƙasa (NNPCL) ga jama’a su gani domin tantancewa, tare da bayyana wa ƴan Nijeriya ainihin waɗanda ke ɗaukar nauyin yaƙin neman zaɓensa.
A cikin wata sanarwa da ya fitar, Atiku ya nuna shakku kan yadda ake tafiyar da harkokin kuɗaɗen kamfanin na NNPCL, inda ya yi zargin cewa akwai rashin gaskiya da ɓoye-ɓoye wajen sarrafa kuɗaɗen shigar man fetur, a daidai lokacin da al’ummar ƙasar ke cikin matsanancin halin ƙuncin rayuwa da tsadar mai.
Atiku ya ƙalubalanci Shugaba Tinubu da ya fito fili ya yi wa ƴan ƙasa bayani kan tushen kuɗaɗen da ake amfani da su wajen tafiyar da harkokin siyasarsa da yaƙin neman zaɓensa, yana mai tambayar ko akwai karkatar da kuɗaɗen kamfanin mai na ƙasa domin biyan buƙatun siyasa na gwamnati mai ci.
Haka kuma, ya jaddada cewa bayan janye tallafin man fetur da gwamnati ta yi, ya kamata a ce an samu ƙarin kuɗaɗen shiga a asusun ƙasa da zai inganta rayuwar talakawa, amma har yanzu rashin bayyana gaskiya a kan alƙaluma da lissafin NNPCL ya bar tambayoyi da dama a zuƙatan ƴan Nijeriya.
A ƙarshe, Atiku ya yi kira da a ba da damar gudanar da cikakken sasihin binciken kuɗi mai zaman kansa (forensic audit) a kan dukkan harkokin kasuwanci da kuɗaɗen NNPCL, yana mai buƙatar al’umma da ƙungiyoyin kare haƙƙin jama’a da su ci gaba da matsa lamba domin tabbatar da gaskiya da riƙon amana a fannin man fetur na ƙasar.














