ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Farfesa Gwarzo Ya Gwangwaje Cibiyar Ilimi ‘Alliance Française Kano’ Da Gini Mai Hawa Biyu Na Zamani

...ya kuma bayar da tallafin Naira Miliyan 10 na gudanarwa

by Bello Hamza and Sulaiman
10 months ago
Gwarzo

Wanda ya kafa gamayyar jami’o’in MAAUN, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, ya bai wa cibiyar ilimin koyon harshen faransanci ta ‘Alliance Française Kano’ ginin bene mai hawa biyu ɗauke da dukkan kayan aiki na zamani—ciki har da ajujuwan karatu na zamani, dakunan koyon harshe na zamani, dakunan sauraro da nune-nune harshe, da kujeru da tebura na musamman da aka tsara don inganta koyarwa.

Fitaccen mai bunkasa harkokin ilimin ya ƙara tabbatar da irin jajircewarsa wajen bunƙasa ilimi da kuma musayar al’adu, ta hanyar ƙara bayar da tallafin Naira miliyan 10 domin gudanar da ayyukan yau da kullum da kuma tabbatar da dorewar cibiyar.

  • Sin Ta Ce Ikirarin Japan Cewa Matsayarta Kan Batun Taiwan Ba Ta Sauya Ba, Bai Wadatar Ba
  • Martabar Kasar Sin Na Karuwa A Idanun Duniya

Ginin da jakadan Faransa a Nijeriya, Marc Fonbaustier, tare da Farfesa Gwarzo suka kaddamar da shi ga al’umma, ya ƙunshi allunan koyarwa na zamani, na’urar intanet mai ƙarfi, ɗakunan taro, kayan koyar wa da ke amfani da sauti da hoto, da kuma dakunan karatu na dijital.

ADVERTISEMENT

Ginin da ke Ahmadiyya Junction a kan titin filin jirgin sama na Kano, yanzu ana ɗaukarsa a matsayin ɗaya daga cikin cibiyoyin koyar da harshen Faransanci da al’adu a zamance a Arewacin Nijeriya.

LABARAI MASU NASABA

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

A cewar Farfesa Gwarzo, kafa irin wannan cibiya ta zamani zai taka rawar gani wajen farfaɗo da ilimin harsuna biyu a Kano, tare da bai wa ɗalibai damar samun ingantaccen horo na harshen Faransanci a matakin duniya.

A jawabinsa, Jakadan Faransa a Nijeriya, Marc Fonbaustier, ya yaba wa Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo bisa kyautar ginin da kuma samar da gagarumin kayayyakin da aka tanada a ciki.

Jakadan ya yi addu’ar Allah Ya kara wa Farfesa Gwarzo tsawon rai da lafiya, domin ya cigaba da bayar da irin wannan gudummawa ta jinƙai da kuma bunkasa ilimi wanda ya shahara da su.

Daraktan Alliance Française Kano, Ali Dabo, ya bayyana matukar godiyarsa ga Farfesa Gwarzo bisa ginin da kuma kayayyakin zamani da ya samar.

Ya ce a tsawon shekarun da cibiyar ta fara aiki a Kano, babu wani mutum da ya taɓa gyara wa ko sauya tsarin cibiyar, balle ɗaukaka ta zuwa wannan mataki na musamman kamar yadda Farfesa Gwarzo ya yi.

Ya ƙara da cewa, Farfesa Gwarzo ya kawo ƙarshen dogon lokacin da cibiyar ta shafe tana zaman haya fiye da shekara goma, ta hanyar samar mata da ofishi na dindindin kuma mai daraja.

Gwarzo
Bello Hamza
+ posts Bio
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Jihar Kano Za Ta Amfana Matuka Da Gidauniyar Aliko Dangote – Masu Ruwa Da Tsaki
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    An Nuna Damuwa Kan Sake Kamun Da DSS Ta Yi Wa Boɗejo Bayan Samun Belin EFCC
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Dole Al’ummar Arewa Su Rungumi Hanyoyin Kasuwanci Na Zamani —Alfa Musa
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Ba Mu Taba Biyan Kudin Fansa Ba Kuma Ba Za Mu Biya Ba – Kwamishinan Katsina
Gwarzo
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi
  • Sulaiman
    Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

MASU ALAKA

Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja
Labarai

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji
Manyan Labarai

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Next Post
Mbappe

Mbappe Ya Kafa Wani Sabon Tarihi A Gasar Zakarun Turai

LABARAI MASU NASABA

Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.