ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, June 24, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Fasahar AI Nasara Ko Kalubale?

by CGTN Hausa and Sulaiman
4 weeks ago
AI, Artificial intelligence, innovation and technology Concept. Businessman hand holding virtual digital icons for online information network

AI, Artificial intelligence, innovation and technology Concept. Businessman hand holding virtual digital icons for online information network

Yayin da fasahar kirkirarriyar basira ta AI, da fasahohi masu nasaba da ita kamar na mutum-mutumin inji ke kara shiga sassan rayuwar yau da kullum, a nan kasar Sin kasuwar wannan fasaha ta AI na kara fadada, inda wasu alkaluma ke cewa nan zuwa shekarar 2030, za ta kai darajar kudin kasar yuan biliyan 400, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 58.96, adadin da mai yiwuwa ya haura yuan tiriliyan daya zuwa shekarar 2035, tare da samar da guraben ayyukan yi sama da miliyan daya.

Wadannan alkaluma na nuni ga matukar darajar da ke tattare da fasahar AI, wadda tuni ta zamo sabon inji dake ingiza ci gaban tattalin arziki, da masana’antun kirkire-kirkire, da samar da guraben ayyukan yi ga dumbin al’ummun kasar ta Sin.

To sai dai kuma duk da wannan tagomashi, akwai sassa dake nuna dar dar, cewa fasahar AI na iya gurgunta kasuwar kwadago ta gargajiya, da maye guraben ayyuka na bil’adama da injuna, kuma wannan damuwa ba ta takaita ga kasar Sin kadai ba, muna ma iya cewa damuwa ce ta al’ummun duniya baki daya.

ADVERTISEMENT

Amma a daya bangaren, abu ne sananne cewa a dukkanin lokutan da duniya ta fuskanci juyin juya halin masana’antu a tarihi, al’ummun duniya su kan nuna irin wannan damuwa, cewa kirkire-kirkiren fasahohin za su kwacewa bil’adama damammaki na ayyukan yi. Tabbas akwai wasu sassa da ci gaban masana’antu kan zo da irin wannan sauyi.

Alal misali, an ga yadda babban sauyi a masana’antun masaku ya yi awon gaba da tsarin saka na gargajiya a kasashe daban daban. Mun ga yadda wayoyin salula na tafi da gidanka suka kawar da akasarin wayoyin wayar tarho da a baya ake amfani da su da dai sauran misalai da dama. Wato a duk lokacin da aka samu ci gaban kyautatuwar fasahohi, ana samun wasu rukuni na ayyukan da za su zama tsohon yayi, kana masu gudanar da su na iya rasa guraben ayyukansu gaba daya.

LABARAI MASU NASABA

Binciken CGTN: Amfanarwa A Aikace Shi Ne Nagartaccen Ma’aunin Tantance Ainihin Kimar Sabbin Fasahohi

Kasar Sin Na Kara Zama Babban Ginshikin Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya Na Gaba

Amma duk da haka, a nan yana da kyau mu lura cewa yayin da sabbin fasahohi ke kawar da salon gudanar da ayyuka na gargajiya, a daya hannun suna kuma bullo da wasu sana’o’in masu nasaba.

Alal misali, yayin da na’urori masu kwakwalwa suka kawar da aiki da keken rubutu ko typewriter, a daya hannun sun bullo da sana’ar tsara manhajoji, da ta masu kula da yanar gizo, da masu nazarin bayanai, da masu tsaro intanet da sauransu ga miliyoyin mutane. Wato dai tarihi ya wanzar da cewa, sabbin fasahohi na maye gurbin wasu ayyuka ne kawai, amma ba wai raba bil’adama da guraben ayyukan yi gaba daya ba.

Don haka masana da dama ke cewa, ita ma fasahar AI za ta bi wannan salo, wato za ta haifar da rasa wasu ayyuka a wasu sassa, amma kuma a lokaci guda, za ta bude sabbin babuka na ci gaba.

Wannan ra’ayi ya yi daidai da abun dake kunshe cikin rahoton kasa da kasa, na dandalin fitar da bayanai game da makomar ayyukan yi a nan gaba na 2025, wanda ya ce ya zuwa shekarar 2030, akwai yiwuwar gushewar guraben ayyukan yi miliyan 92 a duniya, amma a lokaci guda kuma, zuwa karshen karnin nan, mutane za su samu sabbin ayyukan yi kimanin miliyan 170.

Don haka dai, muna iya cewa fasahar AI, ta zo wa duniya da tarin damammaki, sama da kalubalen da ake tunani, musamman idan bil’adama ya aiwatar da manufofi masu dacewa da kuma yin hangen nesa wajen cin gajiyar fasahar AI. (Saminu Alhassan)

AI
CGTN Hausa
+ posts Bio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Dandalin DAVOS Na Bana: Fage Ne Da “Kirkire-Kirkiren Sin” Ya Sadu Da “Kyakkyawan Fatan Afirka”
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Binciken CGTN: Amfanarwa A Aikace Shi Ne Nagartaccen Ma’aunin Tantance Ainihin Kimar Sabbin Fasahohi
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Kasar Sin Na Kara Zama Babban Ginshikin Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya Na Gaba
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sin Ta Gabatar Da Tsarin Karfafa Kwarin Gwiwar Kamfanoni Masu Jarin Waje
AI
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Dandalin DAVOS Na Bana: Fage Ne Da “Kirkire-Kirkiren Sin” Ya Sadu Da “Kyakkyawan Fatan Afirka”
  • Sulaiman
    Binciken CGTN: Amfanarwa A Aikace Shi Ne Nagartaccen Ma’aunin Tantance Ainihin Kimar Sabbin Fasahohi
  • Sulaiman
    Kasar Sin Na Kara Zama Babban Ginshikin Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya Na Gaba
  • Sulaiman
    Tsaro: Dasuki Ya Bukaci Tinubu Ya Gyara Alaka Da Nijar Domin Kare Iyakokin Arewa-Maso-Yamma

MASU ALAKA

Binciken CGTN: Amfanarwa A Aikace Shi Ne Nagartaccen Ma’aunin Tantance Ainihin Kimar Sabbin Fasahohi
Daga Birnin Sin

Binciken CGTN: Amfanarwa A Aikace Shi Ne Nagartaccen Ma’aunin Tantance Ainihin Kimar Sabbin Fasahohi

June 24, 2026
Kasar Sin Na Kara Zama Babban Ginshikin Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya Na Gaba
Daga Birnin Sin

Kasar Sin Na Kara Zama Babban Ginshikin Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya Na Gaba

June 24, 2026
Sin Ta Gabatar Da Tsarin Karfafa Kwarin Gwiwar Kamfanoni Masu Jarin Waje
Daga Birnin Sin

Sin Ta Gabatar Da Tsarin Karfafa Kwarin Gwiwar Kamfanoni Masu Jarin Waje

June 24, 2026
Next Post
Ya Kamata EU Ta Yi Hangen Nesa Game Da Alakar Cinikayya Dake Tsakaninta Da Kasar Sin

Ya Kamata EU Ta Yi Hangen Nesa Game Da Alakar Cinikayya Dake Tsakaninta Da Kasar Sin

LABARAI MASU NASABA

Dandalin DAVOS Na Bana: Fage Ne Da “Kirkire-Kirkiren Sin” Ya Sadu Da “Kyakkyawan Fatan Afirka”

Dandalin DAVOS Na Bana: Fage Ne Da “Kirkire-Kirkiren Sin” Ya Sadu Da “Kyakkyawan Fatan Afirka”

June 24, 2026
Binciken CGTN: Amfanarwa A Aikace Shi Ne Nagartaccen Ma’aunin Tantance Ainihin Kimar Sabbin Fasahohi

Binciken CGTN: Amfanarwa A Aikace Shi Ne Nagartaccen Ma’aunin Tantance Ainihin Kimar Sabbin Fasahohi

June 24, 2026
Kasar Sin Na Kara Zama Babban Ginshikin Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya Na Gaba

Kasar Sin Na Kara Zama Babban Ginshikin Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya Na Gaba

June 24, 2026
Tsaro: Dasuki Ya Bukaci Tinubu Ya Gyara Alaka Da Nijar Domin Kare Iyakokin Arewa-Maso-Yamma

Tsaro: Dasuki Ya Bukaci Tinubu Ya Gyara Alaka Da Nijar Domin Kare Iyakokin Arewa-Maso-Yamma

June 24, 2026
Sabbin Ministoci

Kafa ‘Yansandan Jihohi: Majalisa Ta Amince Da Tsarin ‘Yar Tinƙe Wajen Kaɗa Ƙuri’a 

June 24, 2026
Sin Ta Gabatar Da Tsarin Karfafa Kwarin Gwiwar Kamfanoni Masu Jarin Waje

Sin Ta Gabatar Da Tsarin Karfafa Kwarin Gwiwar Kamfanoni Masu Jarin Waje

June 24, 2026
Shugaban Kasar Burundi: Dangantakar Afirka Da Sin Misali Ce Ta Hadin Gwiwar Kasashe Masu Tasowa

Shugaban Kasar Burundi: Dangantakar Afirka Da Sin Misali Ce Ta Hadin Gwiwar Kasashe Masu Tasowa

June 24, 2026
Yadda Na Sayar Da Kadarori Na Don Ɗaukar Nauyin Ɗalibai A Ƙasashen Waje – Kwankwaso

Zargin Ɓata Suna: Kwankwaso Ya Yi Barazanar Neman Diyyar Naira Biliyan 10 Kan Wani Malamin Coci

June 24, 2026
Li Qiang Ya Halarci Bikin Bude Dandalin Tattalin Arzikin Duniya Na Davos Na Shekarar 2026

Li Qiang Ya Halarci Bikin Bude Dandalin Tattalin Arzikin Duniya Na Davos Na Shekarar 2026

June 24, 2026
Xi Ya Yi Kiran Daukar Matakan Zamanantar Da Aikin Gona Da Yankunan Karkara

Xi Ya Yi Kiran Daukar Matakan Zamanantar Da Aikin Gona Da Yankunan Karkara

June 24, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.