ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 24, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gadar Oporoma a jihar Bayelsa ta Najeriya ta kara hada zukatan jama’ar Sin da Najeriya

by Sulaiman
5 months ago

Kwanan nan, an kammala gina babbar gadar Oporoma a jihar Bayelsa ta Najeriya kuma aka kaddamar da ita. Wannan gada mai tsawon mita 630 wadda kamfanin China Civil Engineering Construction Corporation (CCECC) ya gina, ta ratsa kogin Nun, wani reshe na kogin Neja.

Gadar wadda ita ce mafi girma a jihar Bayelsa, tana da matukar muhimmanci wajen hade babban birnin jihar Bayelsa, wato Yenagoa, da shalkwatar karamar hukumar kudancin Ijaw, wato Oporoma.

Ga mazauna yankin kudancin Ijaw, muhimmancin wannan gada tana da ma’ana ta musamman, domin wannan yanki mai cike da koguna da rafuka ya dade yana dogara sosai kan hanyoyin ruwa domin zirga-zirga, wanda ke haifar da wahalar tafiya da tsadar jigilar kaya, inda hakan yake kawo cikas ga ci gaban tattalin arzikin yankin.

ADVERTISEMENT

Amma Gadar Oporoma ta daidaita wannan matsala, kana ta inganta aikin jigilar amfanin gona da tafiye-tafiyen mazauna yankin cikin sauki.A wurin bikin kammala aikin, shugaban Najeriya Bola Tinubu ya bayyana cewa, gadar Oporoma ta inganta zirga-zirgar yankin sosai, baya ga samar da ayyukan yi da kyautata yanayin rayuwar mazauna.

Hakika, wannan misali ne na yadda hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka ta fannin aikin gina ababen more rayuwa ke amfanar da jama’a.Daga layin dogo na tsakanin Tanzania da Zambia zuwa gadar Oporoma, Sin ta kasance abokiyar gina Afirka mafi aminci a cikin fiye da rabin karni da ya gabata.

LABARAI MASU NASABA

Ra’ayin Kasar Sin Kan Fasahar AI Yana Samar Da Damammaki Ga Afirka

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta

Ba tare da sanya sharuddan siyasa ba, ba tare da tsoma baki cikin harkokin cikin gida ba, Sin tana mai da hankali ne kawai kan abubuwan da jama’ar kasashen Afirka ke bukata da kuma ci gaban da suke nema, kuma wannan shi ne sirrin dorewa da ingancin hadin gwiwar Sin da Afirka.

Wannan gada, ba wai kawai ta hada gefen kogi biyu ba ce, har ma ta hada zukatan mutanen Sin da Afirka. Yayin da motoci ke ta zirga-zirga a kan gadar Oboroma, kuma musayar al’amura tsakanin gefen biyu ke kara yawaita, an yi imani cewa: Abotar Sin da Afirka tana da karfi kamar wannan gada, kuma makomar hadin gwiwar Sin da Afirka za ta kara haske.(Marubuci: MINA)

Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Sultan Ya Gargaɗi Malaman Addini Kan Kare Masu Cin Hanci Da Rashawa
  • Sulaiman
    ’Yansanda Sun Ƙwato Motoci 52, Sun Kama Masu Laifi 177 A Mako Guda
  • Sulaiman
    Kada Ku Ɗauki Nauyin Aikin Hajji Da Kuɗaɗen Da Aka Sace — Sultan Ga ’Yan Siyasa
  • Sulaiman
    Ya Kamata Kowane Dan Nijeriya Ya Samu Horon Soja – Ministan Tsaro

MASU ALAKA

Ra’ayin Kasar Sin Kan Fasahar AI Yana Samar Da Damammaki Ga Afirka
Ra'ayi Riga

Ra’ayin Kasar Sin Kan Fasahar AI Yana Samar Da Damammaki Ga Afirka

September 14, 2026
Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta
Ra'ayi Riga

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta

September 8, 2026
Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin
Ra'ayi Riga

Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin

September 4, 2026
Next Post
Wike Ya Caccaki Atiku, Ya Ce Zai Sake Tsayawa Takara A 2031 Tun Da Ya Saba

Wike Ya Caccaki Atiku, Ya Ce Zai Sake Tsayawa Takara A 2031 Tun Da Ya Saba

LABARAI MASU NASABA

Musk Ya Hango Gagarumin Ci Gaban Mutum-Mutumi Masu Siffar Dan’Adam A Kasar Sin Tare Da Yabawa Da Yadda Kasar Ke Da Ban Sha’awa

Musk Ya Hango Gagarumin Ci Gaban Mutum-Mutumi Masu Siffar Dan’Adam A Kasar Sin Tare Da Yabawa Da Yadda Kasar Ke Da Ban Sha’awa

September 23, 2026
Zargin Maita: ‘Yansanda Sun Cafke Mutum Huɗu Bisa Hallaka Wani A Bauchi

Zargin Maita: ‘Yansanda Sun Cafke Mutum Huɗu Bisa Hallaka Wani A Bauchi

September 23, 2026
Dandalin Al’adu Na Beijing Zai Mayar Da Hankali Ga Batun Gadon Al’adu Da Koyi Da Juna Tsakanin Mabanbantan Wayewar Kai

Dandalin Al’adu Na Beijing Zai Mayar Da Hankali Ga Batun Gadon Al’adu Da Koyi Da Juna Tsakanin Mabanbantan Wayewar Kai

September 23, 2026
Sultan

Sultan Ya Gargaɗi Malaman Addini Kan Kare Masu Cin Hanci Da Rashawa

September 23, 2026
Li Qiang Ya Halarci Bikin Bude Taron Nuna Kwarewar Sana’o’i Na Duniya Na Shekarar 2026

Li Qiang Ya Halarci Bikin Bude Taron Nuna Kwarewar Sana’o’i Na Duniya Na Shekarar 2026

September 23, 2026
‘Yansanda Sun Kashe Masu Garkuwa Da Mutane 8, Sun Kubutar Da Mutane 3 A Jihar Bauchi

’Yansanda Sun Ƙwato Motoci 52, Sun Kama Masu Laifi 177 A Mako Guda

September 23, 2026
Yayin Da Taron UNGA Na 81 Ya Zo A Lokacin Da Duniya Ta Shiga Tsaka-mai-wuya…

Yayin Da Taron UNGA Na 81 Ya Zo A Lokacin Da Duniya Ta Shiga Tsaka-mai-wuya…

September 23, 2026
Sultan

Kada Ku Ɗauki Nauyin Aikin Hajji Da Kuɗaɗen Da Aka Sace — Sultan Ga ’Yan Siyasa

September 23, 2026
Liu Guozhong Ya Halarci Shagulgulan Bikin Girbi Na Manoman Kasar Sin Na Bana

Liu Guozhong Ya Halarci Shagulgulan Bikin Girbi Na Manoman Kasar Sin Na Bana

September 23, 2026
Basukan Giratuti: Gwamnatin Bauchi Ta Fara Biyan ₦10bn Ga ‘Yan Fansho 1,700

Basukan Giratuti: Gwamnatin Bauchi Ta Fara Biyan ₦10bn Ga ‘Yan Fansho 1,700

September 23, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.