ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, June 24, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gudunmawar Likitocin Dabbobi Wajen Hana Barkewar Cututtuka

by Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
2 months ago
Likitocin

Ranar Likitocin Dabbobi Ta Duniya muhimmiyar rana ce da aka ware domin bitar rawar da likitocin dabbobi ke takawa wajen kare lafiyar dabbobi, tsaron abinci da lafiyar jama’a.

A na gudanar da bukin muhimmiyar ranar ne a kowace shekara a ranar Asabar din karshe ta watan Afrilu domin wayar da kan al’umma kan muhimmancin fannin likitocin dabbobi a rayuwar yau da kullum. Taken taron na bana shine Likitocin Dabbobi: Ginshikin Kare Abinci Da Lafiya.

Ranar 25 ga Afrilu din makon jiya da aka gudanar da bukin zagayowar ranar ta 2026, an gudanar da muhimman taruka da bita tare da jaddada gudunmuwar da likitocin dabbobi ke bayarwa wajen hana yaduwar cututtuka, kula da dabbobi da kuma tabbatar da ingantaccen abinci ga al’umma wadda dama ce ga kasashe da kungiyoyi domin kara karfafa manufofi da zuba jari a fannin domin inganta tsaron lafiya da abinci a fadin duniya.

ADVERTISEMENT

Yayin da duniya ke bukin tunawa da ranar likitocin dabbobi, kungiyar likitocin dabbobi a Nijeriya ta jaddada cewar wannan lokaci bai kamata ya tsaya ga shagulgula kawai ba, kamata ya yi ya zama matakin kawo sauyi mai ma’ana wajen daukar matakan da za su bunkasa fannin a tsarin manufofin kasa

A bayyane yake cewar gudunmuwar da likitocin dabbobi ke bayarwa wajen kare lafiyar al’umma ta hanyar kula da lafiyar dabbobi da hana yaduwar cututtuka musamman daga mahauta ta fi gaban a nanata; hasalima tuni fannin ya zama kinshiki mai zaman kansa wajen tabbatar da tsaron abinci da lafiyar jama’a.

LABARAI MASU NASABA

Zargin Ɓata Suna: Kwankwaso Ya Yi Barazanar Neman Diyyar Naira Biliyan 10 Kan Wani Malamin Coci

Atiku Ya Soki Tsare El-Rufai, Ya Ce Sharuɗan Belinsa Sun Yi Tsauri

Kima da tasirin likitocin dabbobi muhimmi ne domin kuwa lafiyar dabbobi da ta mutane suna da alaka kai tsaye ta kut da kut ta yadda kai tsaye za a iya cewa cututtuka da dama na wucewa daga dabbobi zuwa mutane wanda hakan ke nuna kula da lafiyar dabbobi na nufin kare lafiyar dan Adam.

Likitocin dabbobi na da muhimmiyar rawar da suke takawa wajen gano cututtuka da wuri, gudanar da allurar rigakafi da kuma sa idanu kan lafiyar dabbobi domin hana barkewar annoba a cikin al’umma.

A yayin da duniya ke bukin muhimmiyar ranar, kwararrun likitocin dabbobi a Nijeriya sun yi kakkausan gargada cewar tsarin tsaron abinci, lafiyar jama’a da kuma kare muhalli na kasar na fuskantar babbar barazana kamar yadda shugaban kungiyar na kasa, Dakta Moses Arokoyo ya bayyana a ranar.

A kan wannan kungiyar ta bukaci daukar kwararan matakan gaggawa wajen inganta fannin, kara zuba jari da kuma baiwa likitocin dabbobi kulawa tare da bayyana shi a matsayin fannin da ke da matukar tasiri ga rayuwar al’umma.

Kungiyar ta bayyana cewar, kula da lafiyar jama’a da kuma daidaiton muhalli na fuskantar karin barazana sakamakon karancin kudi, raunin da ke akwai a tsarin hukumomi da kuma gazawar aiwatar da manufofi yadda ya kamata.

Shugaban kungiyar, Arokoyo ya bayyana cewa halin da ake ciki ya kai wani matsayi mai hatsari sakamakon sakaci, raunin aiwatar da manufofii da kuma karancin zuba jari a fannin kiwon lafiyar dabbobi.

A cewarsa, Nijeriya ba za ta iya ci- gaba da daukar sha’anin likitancin dabbobi a matsayin karamin abu ba a cikin tsarin tsara manufofin kasa ba, ya jaddada cewa fannin na da matukar muhimmanci domin yana taka muhimmiyar rawa kai tsaye wajen tabbatar da rayuwar al’umma, ingancin abinci da kuma lafiyar jama’a.

A kan wannan kungiyar ta bukaci gwamnati da hukumomin da lamarin ya shafa su dauki matakan gaggawa ciki har da kara zuba jari, inganta tsarin kula da lafiyar dabbobi da kuma karfafa dokoki da manufofi domin magance barazanar da ke kara kamari.

LEADERSHIP Hausa ta labarto cewar masanan sun kuma bayyana cewar idan aka samu hadin guiwa a tsakanin sassan lafiya, noma da muhalli za su taimaka sosai wajen rage hadarin cututtuka da tabbatar da ingantaccen abinci ga al’umma.

A wani kakkausan gargadi, shugaban kungiyar Dakta Arokoyo ya bayyana likitocin dabbobi a matsayin wani ginshikin bayan fage a tsarin abinci a Nijeriya wanda ke sahun gaba wajen kare cututtukan da ke wucewa a boye tsakanin dabbobi da mutane.

Shugaban ya yi gargabin cewa duk da yadda aka fi mayar da hankali kan asibitoci da magungunan mutane, ainihin inda ake fara yaki da cututtuka shi ne a gonaki, mahauta, kasuwannin dabbobi da kuma dakunan gwaje-gwaje a inda lafiyar dabbobi ke tantance lafiyar mutane tun kafin barkewar cuta ta kai garuruwa.

“Daga gonaki, mahauta, zuwa teburin abinci, daga dakin gwaje-gwaje zuwa tsara dokoki, likitancin dabbobi ne ke dora ginshkiin tsaron abinci da lafiyar kasa wanda a kan hakan kadai ya kamata a ce fannin ya samu kulawar musamman.”

Haka ma kungiyar ta kuma nuna damuwa kan gazawar gwamnatin kasar nan wajen bai wa fannin isassun kudi da kulawar da ta kamata wanda rashin yin hakan ke haifar da babban gibi mai hadari wajen dakile cututtuka kafin su barke a cikin al’umma.

Kungiyar ta bayyana cewa yanzu haka Nijeriya na fuskantar haduwar babbar barazanar da ta hada da sauyin yanayi, juriyar magunguna da kuma bullar sabbin cututtukan da ke wucewa daga dabbobi zuwa mutane wadanda matsalolin na kara nuna yadda lafiyar dabbobi, ta mutane da kuma muhalli suke da alaka ta kusa- kusa.

A cewar shugaban kungiyar, duniya ta riga ta shiga wani zamani na matakin “Lafiya Daya” ta yadda barkewar cututtuka ba su bin iyakokin da aka saba da su a baya. Ya ce a yanzu cututtuka suna yaduwa cikin sauri tsakanin dabbobi da mutane, yayin da matsin lambar muhalli ke kara hanzarta yaduwarsu.

A kan wannan shugaban ya bayyana cewar rawar da likitocin dabbobi ke takawa na kara zama gagaruma musamman wajen gano barkewar cututtuka da wuri, gudanar da allurar rigakafi, duba ingancin abinci da dakile yaduwar annoba.

Ya ce ko kadan ba za a iya raba lafiyar dan Adam da ta dabba ko muhalli ba, don haka ya zama wajibi a dauki matakan da suka kamata na hadin guiwa domin kare rayuwar al’umma.

Duk da wannan karin nauyi da ake dorawa likitocin dabbobi, kungiyar a Nijeriya ta nuna damuwa kan yadda har yanzu ake raina fannin, ba a ba shi isassun kudi kuma ba a baiwa fannin kulawa a yayin tsara manufofiin kasa.

Haka ma kungiyar ba ta yi kasa a guiwa ba wajen bayyana cewar daya daga cikin manyan matsalolin da aka fi mayar da hankali a kai shi ne rashin ingantaccen bayanai kan dabbobi da lafiyarsu a Nijeriya wanda babban gibi ne da kungiyar ta ce yana hana ingantaccen tsarin tattalin arziki da kuma dakile cututtuka yadda ya kamata.

A kan wannan shugaban kungiyar Dakta, Arokoyo ya yi kira da a gaggauta gudanar da shirin kidayar dabbobi na kasa yana mai gargadin cewar idan babu cikakkun bayanai, a na daukar kwararan matakai ne a cikin duhu kawai.

A kan wannan kungiyar ta jaddada muhimmancin tattara sahihan bayanai domin a cewar ta idan ba a yi gwajin abu ba to tamkar bai wanzu ba ne a tsarin manufofi don haka gwajin ke da tasirin gaske.

Haka ma kungiyar ta ce bayanai kan allurar rigakafi, matakan da ake dauka a yayin  barkewar cututtuka da kuma sakamakon binciken nama, duka ba a rubuta su yadda ya kamata wanda hakan ke hana jawo hankalin masu zuba jari ko kawo gyara mai ma’ana a wannan fannin.

Kungiyar ta kuma fallasa amfani da magungunan dabbobi da ake yi ba bisa ka’ida ba tare da gargadin cewa wannan na iya kara saurin yaduwar matsalar juriyar magunguna wadda barazana ce ta duniya da ke iya sa cututtukan yau da kullum su zama ba su yin magani ga dabbobi da mutane lamarin da shugaban kungiyar ya bayyana cewar ba matsalar likitocin dabbobi ba ce kadai matsalar ceton rayuwa ce bakidaya.

Sai dai duk da muhimmancin da fannin ke da shi bincike ya nuna har yanzu a na fama da sakaci a tsarin don haka akwai bukatar aiwatar da cikakken tsarin likitocin dabbobi na kasa wanda zai shawo kan kara yawan ma’aikata a matakan jihohi da kananan hukumomi da tabbatar da isassun kudi ga shirye-shiryen allurar rigakafi, gyaran mahauta da kuma tsarin sa ido kan cututtuka.

A kan wannan za a iya cewar rashin daukar matakai zai kara jefa al’ummar kasa a cikin hadarin barkewar cututtuka da za a iya kaucewa, karancin abinci da kuma asarar tattalin arziki mai yawa a fannin kiwon dabbobi wanda daya ne daga cikin manyan ginshikan noma da kiyo.

A kan wannan za a ga cewar ci-gaba da yin sakaci da tsarin kiwon lafiyar dabbobi ba karamin kuskure ba ne domin babbar barazana ce ga rayuwar kasa da tsaronta don haka ya zama wajibi a bayar da kulawar da ta kamata.

Kwararrun likitocin dabbobi na taka muhimmiyar rawa a dukkan matakan samar da abinci tun daga kan kiwon dabbobi da rigakafin cututtuka zuwa duba mahauta, bincike a dakunan gwaje-gwaje da sa ido kan cututtuka har zuwa ba da shawara wajen tsara manufofi.

A kan gudunmuwar likitocin dabbobi wajen tabbatar da yanka lafiyayyun dabbobi a mahauta, kwararrun likitocin sun jaddada muhimmiyar rawar da suke takawa wajen kare barkewar cututtuka, musamman ta hanyar tabbatar da lafiyar dabbobin da ake amfani da su wajen samar da abinci.

A cewar shugagaban kungiyar, Dakta Arokoyo, likitocin dabbobi su ne sahun gaba wajen hana yaduwar cututtuka, musamman wadanda ke wucewa daga dabbabi zuwa mutane, ya ce matakan kariya na farawa ne tun daga gonaki, kasuwannin dabbobi da kuma mahauta a inda lafiyar dabbobi ke da tasiri kai tsaye ga lafiyar mutane kafin cuta ta kai ga al’umma.

Rahotanni sun tabbatar da cewar likitocin dabbobi na bayar da gagarumar gudunmuwa daga kan kiwon dabbobi, rigakafin cututtuka, zuwa duba lafiyar nama a mahauta da kuma bincike a dakunan gwaje-gwaje wanda a bayyane tsarin na taimakawa wajen tabbatar da ganin abincin da ake ci ba ya dauke da cututtuka tare da rage yiwuwar barkewar annoba.

LEADERSHIP Hausa ta labarto cewar a mahauta, aikin likitocin dabbobi yana da matukar muhimmanci wajen tabbatar da  lafiyayyun dabbobi kawai ake yankawa, hasalima masana sun bayyana cewa rashin kula da tsafta da kuma rashin sa idon  kwararru a irin wadannan wurare na iya janyo yaduwar cututtukan da ake samu daga abinci wanda ke barazana ga lafiyar jama’a.

Sai dai duk da wannan muhimmanci, kungiyar likitocin dabbobi ta yi gargadi kan yawaitar ma’aikatan bogi da ke amfani da magungunan dabbobi ba bisa ka’ida ba wanda babbar matsala ce mai zaman kan ta da suke fatar ganin an shawo kan ta da ke kara tsanantar matsalar juriyar magunguna da ke barazana ga lafiyar dabbobi da mutane.

A bayyane yake cewar likitocin dabbobi na bayar da gagarumar gudunmuwa a rayuwar al’umma, hasalima su ne ginshikin tabbatar da kariyar abinci da hana yaduwar cututtuka musamman a yanayin gurbacewar sha’anin kiyon lafiya a duniya da ke kara tsananta.

Likitocin
Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
+ postsBio
  • Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
    https://hausa.leadership.ng/author/sharfaddeen-sidi-umar-sokoto/
    Tsaro: Dasuki Ya Bukaci Tinubu Ya Gyara Alaka Da Nijar Domin Kare Iyakokin Arewa-Maso-Yamma
  • Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
    https://hausa.leadership.ng/author/sharfaddeen-sidi-umar-sokoto/
    Ƴan Bindiga Sun Tilasta Wa Ƙauyukan Sakkwato Biyan Sabon Haraji
  • Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
    https://hausa.leadership.ng/author/sharfaddeen-sidi-umar-sokoto/
    Zulum Ya Ƙaddamar Da Gidajen Ƴan Gudun Hijira 100 A Sakkwato
  • Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
    https://hausa.leadership.ng/author/sharfaddeen-sidi-umar-sokoto/
    Siyasar 2027: Yadda Ƴan Adawa Ke Ƙara Shiga Tsaka-mai-wuya

MASU ALAKA

Yadda Na Sayar Da Kadarori Na Don Ɗaukar Nauyin Ɗalibai A Ƙasashen Waje – Kwankwaso
Manyan Labarai

Zargin Ɓata Suna: Kwankwaso Ya Yi Barazanar Neman Diyyar Naira Biliyan 10 Kan Wani Malamin Coci

June 24, 2026
Tinubu Ya Gaza Wajen Magance Matsalar Tsaro A Nijeriya — Atiku
Manyan Labarai

Atiku Ya Soki Tsare El-Rufai, Ya Ce Sharuɗan Belinsa Sun Yi Tsauri

June 24, 2026
‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta
Manyan Labarai

’Yansanda Sun Kama Wani Mutum da Harsasai 174 A Nasarawa

June 24, 2026
Next Post
NPA Ta Tara Kudin Shiga Naira Biliyan 758.2 A 2024

Tashoshin Ruwan Nijeriya Za Su Yi Daidai Da Na Manyan Kasashen Duniya – Dantsoho

LABARAI MASU NASABA

Dokar Sin Ta Gurfanar Da Masu Rajin Ballewar Kabilun Kasar Da Ke Kasashen Waje Ta Dace

Dokar Sin Ta Gurfanar Da Masu Rajin Ballewar Kabilun Kasar Da Ke Kasashen Waje Ta Dace

June 24, 2026
’Yan Kasuwa Na Kasashen Waje Sun Yaba Wa Yanayin Kasuwanci Na Sin

’Yan Kasuwa Na Kasashen Waje Sun Yaba Wa Yanayin Kasuwanci Na Sin

June 24, 2026
Yadda Uba Sani Ya Farfaɗo Da Asibitin Da Aka Yi Watsi Da Shi Tsawon Shekaru 40 – Hakimin Makarfi

Yadda Uba Sani Ya Farfaɗo Da Asibitin Da Aka Yi Watsi Da Shi Tsawon Shekaru 40 – Hakimin Makarfi

June 24, 2026
Dandalin DAVOS Na Bana: Fage Ne Da “Kirkire-Kirkiren Sin” Ya Sadu Da “Kyakkyawan Fatan Afirka”

Dandalin DAVOS Na Bana: Fage Ne Da “Kirkire-Kirkiren Sin” Ya Sadu Da “Kyakkyawan Fatan Afirka”

June 24, 2026
Binciken CGTN: Amfanarwa A Aikace Shi Ne Nagartaccen Ma’aunin Tantance Ainihin Kimar Sabbin Fasahohi

Binciken CGTN: Amfanarwa A Aikace Shi Ne Nagartaccen Ma’aunin Tantance Ainihin Kimar Sabbin Fasahohi

June 24, 2026
Kasar Sin Na Kara Zama Babban Ginshikin Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya Na Gaba

Kasar Sin Na Kara Zama Babban Ginshikin Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya Na Gaba

June 24, 2026
Tsaro: Dasuki Ya Bukaci Tinubu Ya Gyara Alaka Da Nijar Domin Kare Iyakokin Arewa-Maso-Yamma

Tsaro: Dasuki Ya Bukaci Tinubu Ya Gyara Alaka Da Nijar Domin Kare Iyakokin Arewa-Maso-Yamma

June 24, 2026
Sabbin Ministoci

Kafa ‘Yansandan Jihohi: Majalisa Ta Amince Da Tsarin ‘Yar Tinƙe Wajen Kaɗa Ƙuri’a 

June 24, 2026
Sin Ta Gabatar Da Tsarin Karfafa Kwarin Gwiwar Kamfanoni Masu Jarin Waje

Sin Ta Gabatar Da Tsarin Karfafa Kwarin Gwiwar Kamfanoni Masu Jarin Waje

June 24, 2026
Shugaban Kasar Burundi: Dangantakar Afirka Da Sin Misali Ce Ta Hadin Gwiwar Kasashe Masu Tasowa

Shugaban Kasar Burundi: Dangantakar Afirka Da Sin Misali Ce Ta Hadin Gwiwar Kasashe Masu Tasowa

June 24, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.