ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tashoshin Ruwan Nijeriya Za Su Yi Daidai Da Na Manyan Kasashen Duniya – Dantsoho

by Bello Hamza
4 months ago
Tashoshin

Manajan Darakta kuma Babban Jami’in Zartarwa na Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Nijeriya (NPA), Dakta Abubakar Dantsoho, ya ce da sauye-sauyen da gwamnatin tarayya ke aiwatarwa, tsarin tashoshin jiragen ruwa na Nijeriya zai shiga sabon mataki tare da zama jagora a harkar sufurin ruwa a nahiyar Afirka.

Dantsoho ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a taron Zuba Jari na Tattalin Arzikin Teku (Blue Economy Inbestment Summit) da aka gudanar a Abuja, inda ya ce tashoshin jiragen ruwa na Nijeriya za su taka muhimmiyar rawa wajen jawo manyan masu zuba jari da kuma hanzarta bunkasar tattalin arziki.

Sai dai ya danganta sauyin da ake samu a bangaren harkar ruwa da tasirin Ministan Harkokin Ruwa da Tattalin Arzikin Teku, Dakta Adegboyega Oyetola, da kuma sauye-sauyen da gwamnatin tarayya ke aiwatarwa.

ADVERTISEMENT

Ya kuma tabbatar wa masu zuba jari cewa Nijeriya na da karfin zama jagora a tattalin arzikin tekun Afirka (blue economy), yana mai cewa gyare-gyaren gwamnati da kuma karuwar shigar masu zaman kansu su ne manyan ginshikan wannan sauyi.

Ya ce dole ne Nijeriya ta mayar da hankali wajen amfani da albarkatun tekunta yadda ya kamata domin cimma manufofin ci gaban duniya mai dorewa.

LABARAI MASU NASABA

Yadda Taron Bikin Maulidi Ya Gudana A Unguwar Mile 12 A Legas

NPA Ta Bayyana Cewa Kirkiro Da Sabuwar Hukumar NPERA Ba Zai Zame Mata Tarnaki Ba

“Lokaci ya yi da za a sauya tsarin tattalin arzikin Nijeriya zuwa yadda za a yi cikakken amfani da albarkatun tekunmu. Idan aka yi amfani da tsarin tashoshin jiragen ruwa yadda ya kamata, zai iya zama babban ginshiki na bunkasar tattalin arziki,” in ji shi.

Shugaban NPA ya bayyana cewa matsayi na Nijeriya a taswirar duniya, yawan al’umma da karfin tattalin arziki suna ba ta damar zama cibiyar harkar ruwa a Yammacin Afirka, kamar kasashe irin su Singapore da Morocco.

“Saboda matsayinta na dabaru, girman kasuwa da karfin tattalin arziki, Nijeriya na da damar zama cibiyar harkar jiragen ruwa ta Yammacin Afirka,” in ji shi.

Duk da wadannan damar, Dantsoho ya nuna damuwa cewa a halin yanzu Nijeriya na sarrafa kusan kashi 25 cikin 100 ne kawai na zirga-zirgar kaya a yankin, duk da cewa tana dauke da fiye da kashi 60 cikin 100 na GDP na Yammacin Afirka.

“Abin damuwa ne cewa Nijeriya, duk da cewa tana da sama da kashi 60 cikin 100 na GDP na Yammacin Afirka, tana sarrafa kusan kashi 25 cikin 100 ne kawai na jigilar kaya a yankin. Wannan a fili yana nuna cewa ba mu yi amfani da cikakken damar da muke da ita ba,” in ji shi.

Dantsoho ya jaddada cewa gasa a harkar sufurin ruwa ta duniya na bukatar ingantaccen aiki, farashi mai gasa da kuma kyakkyawar hadin kai tsakanin yankunan cikin kasa da tashoshin ruwa, yana mai cewa dole ne tashoshin Nijeriya su ci gaba da sabawa da sauye-sauyen da ke faruwa a harkar sufurin ruwa a duniya.

“Idan aka ci gaba da aiwatar da wadannan tsare-tsare yadda ya kamata, tsarin tashoshin jiragen ruwa na Nijeriya zai shiga sabon mataki tare da zama jagora a harkar sufurin ruwa a Afirka,” in ji shi.

Ministan Harkokin Ruwa da Tattalin Arzikin Teku, Adegboyega Oyetola, a jawabinsa na farko, ya ce albarkatun da Nijeriya ke da su, ciki har da bakin tekun ta mai tsawon kilomita 823 da manyan hanyoyin ruwa na cikin kasa, suna ba ta damar jagorantar wannan bangare.

“Da bakin teku mai tsawon kilomita 823, manyan hanyoyin ruwa na cikin kasa da kuma matsayi mai muhimmanci a Tekun Guinea, Nijeriya na da damar musamman wajen amfani da albarkatun tattalin arzikin ruwa,” in ji Oyetola.

Ya kara da cewa sauye-sauyen da gwamnatin tarayya ke yi sun inganta hadin kai, karfafa tsaron teku da kuma kara amincewar masu zuba jari, yana mai cewa bangaren na dauke da fiye da kashi 90 cikin 100 na dukkanin kasuwancin Nijeriya na kasa da kasa ta fuskar girma.

Tashoshin
Bello Hamza
+ postsBio
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Jihar Kano Za Ta Amfana Matuka Da Gidauniyar Aliko Dangote – Masu Ruwa Da Tsaki
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    An Nuna Damuwa Kan Sake Kamun Da DSS Ta Yi Wa Boɗejo Bayan Samun Belin EFCC
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Dole Al’ummar Arewa Su Rungumi Hanyoyin Kasuwanci Na Zamani —Alfa Musa
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Ba Mu Taba Biyan Kudin Fansa Ba Kuma Ba Za Mu Biya Ba – Kwamishinan Katsina

MASU ALAKA

Yadda Taron Bikin Maulidi Ya Gudana A Unguwar Mile 12 A Legas
Tattalin Arziki

Yadda Taron Bikin Maulidi Ya Gudana A Unguwar Mile 12 A Legas

September 4, 2026
NPA Ta Bayyana Cewa Kirkiro Da Sabuwar Hukumar NPERA Ba Zai Zame Mata Tarnaki Ba
Tattalin Arziki

NPA Ta Bayyana Cewa Kirkiro Da Sabuwar Hukumar NPERA Ba Zai Zame Mata Tarnaki Ba

September 4, 2026
NPA Ta Tabbatar Da Maido Da Manyan Kayan Aikin Hukumar Wuta Ta Neja Delta —Babbar Manaja
Tattalin Arziki

NPA Ta Tabbatar Da Maido Da Manyan Kayan Aikin Hukumar Wuta Ta Neja Delta —Babbar Manaja

August 28, 2026
Next Post
Majalisar Wakilai Ta Umurci Kamfanonin Rarraba Wutar Lantarki Su Biya Biliyan ₦55.42

Majalisar Wakilai Ta Umurci Kamfanonin Rarraba Wutar Lantarki Su Biya Biliyan ₦55.42

LABARAI MASU NASABA

Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.