ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamna Lawal Ya Cancani Yabo Kan Yunƙurin Farfaɗo Da Masana’antar Yadi Da Sarrafa Auduga Ta Zamfara

by Sulaiman
1 month ago
Zamfara

A da, Jihar Zamfara na daga cikin jihohin da suka yi fice wajen noman auduga a Nijeriya. Wannan ya sa aka kafa masana’antun sarrafa auduga da na yadi da dama, har ta zama ɗaya daga cikin cibiyoyin sarrafa auduga mafi girma a ƙasar.

Sai dai a yau, wannan ɗaukakar ta zama tarihi. Noman auduga ya ragu matuƙa, haka kuma sauran harkokin noma a jihar.

Babban abin da ya jawo hakan shi ne matsalar rashin tsaro da ta addabi jihar tsawon kusan shekaru ashirin, tare da ƙarancin ingantattun iri da manoma za su shuka.Ko manoman da suka ci gaba da noma duk da matsalolin tsaro, sun fuskanci ƙarancin amfanin gona da kuma raguwar ingancin audugar da suke nomawa.

ADVERTISEMENT

Sakamakon haka, masana’antun yadi da masu sarrafa auduga sun fara durƙushewa saboda rashin isasshen auduga, wadda ita ce babban kayan aikin da suke amfani da shi. Hakan ya sa dubban mutane suka rasa ayyukansu, daga manoma zuwa ma’aikatan masana’antu da sauran masu sana’o’in da suka dogara da harkar auduga.

Durƙushewar wannan fanni ta ƙara ta’azzara matsalolin rashin aikin yi, talauci da rashin tsaro a jihar.Abin tambaya shi ne, me ya sa jihar da a da take da masana’antun sarrafa auduga guda 15, waɗanda kowacce ke ɗaukar ma’aikata sama da mutum 200, yanzu ta rage da ƙasa da guda biyar?

LABARAI MASU NASABA

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta

Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin

Me ya sa aka bari Kamfanin Zamfara Textile Limited (ZTL), wanda Marigayi Sir Ahmadu Bello ya ƙaddamar a shekarar 1965 kuma yake ɗaukar ma’aikata kusan 3,000, ya lalace har aka rufe shi a shekarar 2004?

Wane dalili ne ya sa wannan masana’anta da ta kasance ginshiƙin tattalin arzikin dubban iyalai ta durƙushe? Kuma me gwamnati ke yi domin dawo da ita bakin aiki?

Domin warware wannan matsala, wajibi ne gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki su gano ainihin abubuwan da suka jawo durƙushewar wannan masana’antu tare da ɗaukar matakan magance su.

Dole ne a yi tambaya kan rawar da rashin tsaro, ƙarancin ingantattun iri da kuma shigo da yadudduka daga ƙasashen waje ke takawa wajen lalacewar wannan fanni. Haka kuma, ya kamata a tabbatar wa manoma da samar musu da ingantattun iri masu yawan amfanin gona. Sannan gwamnati ta ɗauki tsauraran matakai wajen rage shigo da kayan yadi daga ƙetare.

A kwanakin baya, Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana aniyarsa ta farfaɗo da masana’antun yadi da sarrafa auduga a jihar domin samar da ayyukan yi da rage talauci.

Gwamnan ya bayyana hakan ne bayan wata ziyara da ya kai yankin masana’antu da ke kusa da birnin Cotonou a Jamhuriyar Benin, inda ake sarrafa auduga, goro, waken soya da sauran albarkatun noma zuwa kayayyakin da aka gama ƙerawa.

A ‘yan shekarun nan, Gwamnatin Jihar Zamfara ƙarƙashin jagorancin Gwamna Dauda Lawal ta nuna ƙuduri wajen farfaɗo da sassan tattalin arziƙin jihar da suka yi baya. Daga inganta ababen more rayuwa zuwa ƙoƙarin bunƙasa harkokin noma da masana’antu, gwamnatin na ci gaba da shimfiɗa tubalin dawo da martabar Zamfara a matsayin ɗaya daga cikin cibiyoyin samar da albarkatun noma da masana’antu a Arewacin Najeriya. Wannan ƙuduri ya ƙara ƙarfafa fatan cewa masana’antar auduga da masaku za su sake dawowa da ƙarfi idan aka ci gaba da aiwatar da tsare-tsaren da aka fara.

A cewarsa, abin da ya gani ya ƙara masa ƙwarin gwiwar ganin an dawo da irin wannan ci gaba a Zamfara.Haƙiƙa, idan aka samar da ingantacciyar manufa daga gwamnati, aka gina ababen more rayuwa, sannan aka samu haɗin gwiwar masu zuba jari masu zaman kansu, za a haɗa manoma da masana’antu kai tsaye. Wannan zai rage fitar da ɗanyen kayan noma zuwa ƙasashen waje tare da samar da dubban ayyukan yi a bangaren noma da masana’antu.

Masana’antar yadi ta Zamfara, wadda a da ta kasance tushen aikin yi ga dubban mutane, na buƙatar a dawo da ita cikin gaggawa. Babu shakka wannan fanni na da ƙarfin samar da ayyukan yi masu yawa.

A matakin ƙasa kuwa, Nijeriya na buƙatar sabon tsari na farfaɗo da masana’antar Auduga, Yadi da Tufafi (CTG), domin wannan fanni na iya samar da fiye da ayyukan yi miliyan 1.5, tare da ƙarfafa masana’antu da kuma haɓaka fitar da kayayyaki zuwa ƙasashen waje.

Shekaru na sakaci, rashin ingantaccen tsari da kuma dogaro da kayayyakin da ake shigo da su daga ƙasashen waje ne suka jawo koma bayan wannan masana’anta.

Idan gwamnatin jihar Zamfara ta aiwatar da shirinta yadda ya kamata tare da haɗa hannu da shirin Gwamnatin Tarayya na bunƙasa sarkar masana’antar Auduga, Yadi da Tufafi, za a dawo da martabar wannan fanni, tare da gina cikakkiyar sarkar samar da kayayyaki daga noma zuwa ƙera tufafi da za su iya yin gogayya a kasuwannin duniya.

Don haka, abin da ake buƙata yanzu shi ne gwamnatin Dauda Lawal ta mayar da alkawarinta zuwa aiki. Ta tanadi kuɗi da ƙwararrun ma’aikata, sannan ta ɗauki matakan magance matsalar rashin tsaro, domin ba tare da zaman lafiya ba ba za a iya farfaɗo da noman auduga ko masana’antun da suka dogara da shi ba.

Idan aka cimma wannan buri, Zamfara da Nijeriya baki ɗaya za su amfana matuƙa. Za a samar da dubban ayyukan yi, tattalin arziki zai bunƙasa, kuma rashin aikin yi da ke ɗaya daga cikin manyan abubuwan da ke haddasa rashin tsaro zai ragu sosai.

Zamfara
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna
  • Sulaiman
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

MASU ALAKA

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta
Ra'ayi Riga

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta

September 8, 2026
Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin
Ra'ayi Riga

Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin

September 4, 2026
Samun Rarar Kudin Ciniki Ba “Laifi” Ba Ne, Hadin Gwiwa Da Cin Moriya Tare Ita Ce Mafita Ga Kowa
Ra'ayi Riga

Samun Rarar Kudin Ciniki Ba “Laifi” Ba Ne, Hadin Gwiwa Da Cin Moriya Tare Ita Ce Mafita Ga Kowa

September 2, 2026
Next Post
Jinin Waɗanda Aka Kashe Wajen Haƙar Ma’adanai a Birnin Gwari Ba Zai Tafi Banza Ba – Hon. Bashir Zubairu

Jinin Waɗanda Aka Kashe Wajen Haƙar Ma’adanai a Birnin Gwari Ba Zai Tafi Banza Ba – Hon. Bashir Zubairu

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.