Gwamnan Jihar Kebbi, Dakta Nasir Idris, ya zaɓi Alhaji Ibrahim Augie a matsayin sabon abokin takararsa a zaɓen gwamna na 2027, inda ya maye gurbin Mataimakinsa na yanzu, Sanata Umar Tafida.
Sanarwar da gwamnatin jihar ta wallafa a shafinta na X a ranar Lahadi ta ce Sakataren Tsare-tsaren Jam’iyyar APC na Ƙasa, Alhaji Suleiman Argungu, ne ya bayyana sauyin a Birnin Kebbi. Argungu ya ce an ɗauki matakin ne bisa shawarar ƙwararrun lauyoyi da suka nuna akwai matsala kan cancantar mataimakin gwamnan na yanzu.
Sai dai Argungu ya jaddada cewa an cimma matsayar ne tare da fahimta da amincewar Sanata Tafida, yana mai cewa babu wata taƙaddama tsakanin gwamnan da mataimakinsa. Daga nan ne ya sanar da Ibrahim Augie a matsayin sabon abokin takarar Gwamna Nasir Idris a zaɓen 2027.
Shi ma Gwamna Idris ya yi watsi da duk wata magana da ke nuna cewa an samu saɓani tsakaninsa da Tafida, inda ya yi kira ga ƴan siyasa, da ƴan jam’iyyar APC da magoya bayanta a faɗin jihar da su karɓi matakin tare da haɗa kai domin samun nasarar jam’iyyar a zaɓen 2027.
Ibrahim Augie ya taɓa riƙe muƙamin Kwamishinan Kuɗi a Jihar Kebbi a lokacin mulkin tsohon Gwamna Atiku Bagudu, kuma ya fito ne daga Ƙaramar Hukumar Augie. Gwamna Idris ya kuma buƙaci al’ummar jihar su ci gaba da ba gwamnatinsa haɗin kai domin aiwatar da shirye-shiryen ci gaban jihar.














