Rundunar Sojin Nijeriya ta ce ta ceto mutane tara da wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne suka sace a hanyar Ajaokuta zuwa Itobe, a ƙaramar hukumar Ofu ta Jihar Kogi.
Rundunar ta ce sojojin da ke sansanin Itobe sun samu rahoton harin da aka kai wa matafiya, inda suka isa wurin suka tarar da wata mota ƙirar Toyota Hiace da Toyota Sienna a gefen hanya, yayin da aka tafi da fasinjojin.
Sojojin sun bi sahun masu garkuwar har zuwa wajen ƙauyen Adumu da ke ƙaramar hukumar Dekina, inda suka yi musayar wuta da su.
A cewar rundunar, masu garkuwar sun tsere zuwa daji bayan sun kasa jure ɓarin wutar da sojojin suka yi musu, inda suka bar mutanen da suka sace.
Mutanen tara da aka ceto sun haɗa da tsofaffi maza biyu, tsofaffi mata biyu, wasu maza huɗu da kuma jariri ɗaya.
An kai mutanen waje mai tsaro sannan aka miƙa su ga ’yansandan Itobe domin ci gaba da gudanar da bincike kafin haɗa su da iyalansu.
Rundunar ta ce tana ci gaba da neman masu garkuwar tare da gudanar da bincike.
Ta kuma yi kira ga jama’a da su taimaka wa hukumomin tsaro da sahihan bayanai domin daƙile ayyukan masu laifi.














